Wane mataki Donald Trump zai iya ɗauka kan Iran?

Close up of Donald Trump looking serious on board Air Force One. We can see his head and upper body and he is looking directly at the press but not speaking.

Asalin hoton, Andrew Caballero-Reynolds/ AFP via Getty Images

    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent, Washington
  • Lokacin karatu: Minti 4

A wajen Shugaba Trump, yanzu lokaci ne na ɗaukar mataki.

Kimanin kwana 10 da suka gabata ne ya ce Amurka a shirye take ta kai ɗauki domin "ceto" masu zanga-zanga a Iran idan gwamnatin ƙasar ta yi amfani da ƙarfi a kasu.

Ya yi wannan maganar ne tun kafin a fara amfani da ƙarfi kan masu zanga-zangar, amma yanzu da duniya ta ga abin da ke faruwa a ƙasar ta Iran, za a sa ido a ga me Trump ɗin zai yi.

"Babu wanda ya san abin da Trump zai yi, sai shi kaɗai," in ji sakataren watsa labaran fadar shugaban Amurka, Karoline Leavit. "Sai dai za a cigaba da hasashe ne kawai da jira."

Amma sai yaushe?

Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, Trump ya ce a shirye yake ya ɗauki mataki mai ƙarfi.

Trump dai ya bayyana nasarar da ya samu a Venezuela wajen kama Nicolas Maduro a matsayin ɗaya daga cikin aikin soji da Amurka ta fi samun nasara a tarihinta.

Kamar yadda aka gani a bara, Amurka za ta iya ƙaddamar da hari daga waje mai nisa. Makamin B-2 ya yi tafiyar kusan awa 30 daga sansanin sojin Amurka da ke Missouri domin kai hari a cibiyar nukiliyar Iran.

Ko dai Amurka za ta sake maimaita irin wannan harin ne, ko kuma za ta farmaki wasu daga cikin masu riƙe da madafun iko da suke da hannu wajen fatattakar ƴan zanga-zangar ne, alamu dai sun nuna Amurka na da aiki babba.

Wani jami'in Pentagon ya shaida wa kafar CBS da ke da alaƙar aiki da BBC cewa matakan da Amurka za ta ɗauka a Iran sun ƙunshi hare-haren intanet da na canja domin jefa ruɗu a ƙasar da ma ruɗar da gwamnatin Iran.

Bayanan bidiyo, Rahoton sashen tantance gasakiyar labarai na BBC a cikin harshen Ingilishi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai duk yadda Iran ɗin take, ta wuce Venezuela. Ƙasa ce da take wahalar sha'ani, don haka tsige mutum ɗaya kaɗai ba zai tanƙwara ƙasar baki ɗaya ta koma mubaya'a ga Amurka ba.

Yadda Trump ya yi waiwaye da yunƙurin Amurka na ceto wasu Amurkawa da aka tsare a Iran da Jimmy Carter ya jagoranta, ya nuna cewa yana sane da ƙalubalen da ke gabansa.

Amurkawa 8 ne suke rasu lokacin da helikwafta da EC-130 suka haɗe a gabashin Iran.

Rashin nasarar da aka samu, da kuma wulaƙancin da aka yi wa ƙasar ta hanyar yin holen Amurkawan a Tehran ya taimaka wajen kayar da Carter a zaɓen lokacin.

Yanzu, kimanin shekara 46, tambayar da ake yi ita ce shin me Trump ke so ya cimmawa a Iran a yanzu?

Wataƙila Trump na da burin sauya akalar gwamnatin Iran ne, kamar yadda Todman ya bayyana, maimakon yunƙurin kifar da gwamnatin baki ɗaya.

"Ina tunanin yunƙurin kifar da gwamnati na da haɗari sosai, wanda hakan ya sa nake ganin da wahala Amurka ta ɗauki wannan matakin."

Trump ya ce hukumomin Iran sun fara neman sulhu, inda suke neman tattaunawa, musamman kan shirin ƙasar na nukiliya.

An Iranian woman in a leopard print headscarf walks past an anti-US mural on a street in Tehran, showing a the Statue of Liberty in red and white with damage to its arm.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance na cikin ɗaiɗaikun manyan jami'an gwamnatin ƙasar da suke shawartar Trump ya fara amfani da hanyar diflomasiyya.

"Abin da ya fi dacewa Iran ta yi shi ne shiga tattaunawa da Amurka game da shirinta na nukiliya."

Amma idan amfani da ƙarfi kan masu zanga-zanga ya cigaba a Iran, amfani da diflomasiyya zai zama tamkar gajiyawa.

Wasu na tunanin idan Amurka ta ƙaddamar da ƙaramin har, za ta ƙarfafa gwiwar masu zanga-zangar, sannan zai zama gargaɗi ga gwamnatin Iran cewa somin-taɓi ne.

"Amurka ya kamata Trump ya yi, shi ne ya kai wani ɗan hari da zai ɗaga hankalin gwamnatin Iran," in ji Bilal Saab, wanda mai bincike ne kan gabas ta tsakiya da arewacin Afirka a Chatham House da Landan.

Sai dai Saab ya ce amfani da ƙarfin kuma zai iya barin baya da ƙura domin Iran za ta yanke shawarar mayar da martani.

Abubuwa da dama ne ke ƙunshe a zuciyar Trump, musamman bayan jin yadda Iran ta ce a shirye take ta mayar da martani idan Amurka ta kai mata hari.

Sannan duk da raunana ta da hare-haren Amurka da Isra'ila suka yi, har yanzu Iran da ɗimbin makamai masu linzami a jibge.

Duk da cewa an karya ƙungiyoyin da suke taimakon Iran a gabas ta tsakiya, irin su Hezbollah a Lebanon da gwamnatin Bashar al-Assad, har yanzu akwai masu goya mata baya irin su Houthi a Yeman da wasu ƙungiyoyin ƴan Shi'a masu riƙe da bindiga da za su iya ɗaukar mataki.

Daga cikin wasu fatan ganin Trump ya ɗauki matakin amfani da ƙarfi akwai wanda yake da burin jagorantar Iran domin ficewa daga gwamnatin addini.

"Ya kamata shugaban ƙasa ya ɗauki mataki cikin gaggawa," in ji Reza Pahlavi, ɗan tsohon shugaban Iran, Shah da yanzu yake gudun hijira a zantawarsa da CBS.

"Idan ana so a taƙaita kashe mutane a Iran, to dole a ɗauki mataki da sauri."

Akwai ƙarin bayani daga Kayla Epstein