Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026.
Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar White House ta ce Amurka za ta dakatar da bayar da bizar ƴan ci rani ga ƴan kasashe 75.
Ƙasashen da hakan ya shafa sun haɗa da Rasha da Iran da Afghanistan da wasu ƙasashen Afirka, har da Thailand da Brazil.
A cikin wata takarda da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta umarci ofisoshin jakadancinta a ƙasashen su daina bayar da bizar, yayin da ake ci gaba da yin bita kan matakan da ake bi wajen tantancewa.
Dakatarwar za ta soma aiki ne nan da mako guda, kuma babu tabbacin tsawon lokacin da za a ɗauka kafin a janye ta.

Asalin hoton, Reuters
Wakilin Trump na musamman a Gaza ya sanar da ƙaddamar da mataki na biyu na shirin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
A wannan matakin, za a kafa gwamnatin ƙwararru a Gaza, sannan za a ƙwance ɗamarar ƙungiyar Hamas, kuma sojojin Israila za su janye.
Zuwa yanzu dai Hamas ta ƙi amincewa ta miƙa makamanta, haka-zalika Isra'ila ta ƙi amincewa da ficewa baki ɗaya daga Gaza.
Yarjejeniyar da aka cimma na tsawon watanni uku na da rauni.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce Falasɗinawa fiye da 400 suka mutu a hare-haren Isra'ila tun bayan tsagaita wuta.
Najeriya da Moroko na can suna fafatawa a wasan dab da karshe na gasar cin kofin Afirka.
Akwai shafi na musamman da ke kawo rahotanni kan wasan....

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya da ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar (ASUU) sun rattaɓa hannu kan sabon tsarin yarjejeniya domin inganta tsarin ilimin jami’o'in ƙasar.
ASUU ta ce sabuwar yarjejeniyar da aka cimma, za ta taimaka wajen inganta harkokin koyo da koyar wa a jami’o’in ƙasar.
Ƙungiyar ta ce yarjejeniyar za ta kuma kawo ƙarshen tafiya yajin aiki da ake yawan yi saboda gazawar ɓangaren gwamnati na mutunta yarjejniyar da suka cimma tun 2009.
Shugaban ƙungiyar ta ASUU reshen jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Tajo, ya ce abubuwan da sabuwar yarjejniyar ta ƙunsa sun haɗa da ƙarin albashi da kashi 40 da kuɗaɗen bunƙasa bincike da na gwaje-gwaje da kuma sauran harkokin koyarwa.

Asalin hoton, TSGT Scott Reed, USAF
Rundunar sojin Amurka na kwashe dakarunta da ke wasu sansanoninta a yankin Gulf, yayin da shugaba Trump ke duba yiwuwar bayar da umurnin kai wa Iran harin soji sakamakon zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa ana kuma janye ƙananan ma'aikatan Birtaniya daga sansanin Al Udeid na Qatar, wanda aka kai wa hari a yaƙin da Iran da Isra'ila suka yi na kwanaki 12 a shekarar da ta wuce.
Jami'ai a Amurka sun ce kwashe dakarun wani mataki ne na kandagarki.
Trump ya yi gargaɗin ɗaukar mummunan mataki idan Iran da rataye masu zanga-zanga.

Asalin hoton, Getty Images
Shikenan an tashi wasa!
Kwallon Sadio Mane ta kai Senegal wasan karshe na gasar cin kofin Afirka.
Burin Mohamed Salah na cin Afcon ya sake zuwa karshe.
Senegal da ta lashe Afcon a 2021 za ta hadu da duk wadda ta yi nasara anjima tsakanin Najeriya da Moroko, a wasan karshe da za a yi ranar Lahadi.
Masar na da sauran minti biyar domin samun damar farkewa.
Sadio Mane ya ci wa Senegal kwallonta na farko a wannan fafatawa.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya na kan hanyar bunƙasa mafi girman cikin fiye da shekara goma.
Ana hasashen cewa zai ƙaru da kashi 4.4 cikin 100 a shekarun 2026 da 2027.
Bankin ya bayyana hakan ne a sabon rahotonsa na ci gaban tattalin arzikin duniya wato Global Economic Prospects da ya fitar a ranar Talata.
Sai dai masana na cewa hasashen ya yi hannun riga da halin rayuwa da al’ummar ƙasar ke ciki.
Masar ba ta taɓuka wani abin kirki a gidan Senegal.
Babu haɗin-kai tsakanin ƴan wasan baya da kuma na gaba.
An koma zagaye na biyu a wasan daf da karshe da ake fafatawa tsakanin Masar da Senegal.
Hukumomin shari’a a Burkina Faso sun bayyana cewa sun fara bincike kan mutuwar wata tsohuwar ministar gwamnati, bayan da aka tsinci gawarta a gidanta da ke birnin Ouagadougou.
Masu gabatar da ƙara sun ce shaidu na farko sun nuna cewa an kai mata hari ne tare da kashe ta.
An gano gawar Yolande ne ranar Asabar a gidanta da ke unguwar Karpala a birnin.
Babban mai gabatar da ƙara, Lafiama Prosper Thombiano, ya ce an ɗauki lamarin a matsayin abin gaggawa, inda aka tura jami'an tsaro da ƙwararrun masana binciken gawarwaki domin gano yadda mutuwar ta faru da kuma gano waɗanda ke da hannu.
Hukumomi sun kuma yi kira ga jama’a da su taimaka da bayanan da za su taimaki bincken.
Marigayiyar ta kasance fitacciyar ’yar siyasa a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Blaise Compaoré, wanda ya mulki Burkina Faso na tsawon shekaru 27 kafin kifar da shi a juyin-juya-halin jama’a na shekarar 2014.
Alkalin wasa Pierre Ghislain Atcho ya busa tafiya hutun rabin lokaci daf da lokacin da Senegal ke shirin bugun kusurwa.
Babu ci tsakanin ƙungiyoyin zuwa yanzu.
Mohamed Salah ya samu katin gargaɗi, bayan da ya riƙe tsohon ɗan wasan Liverpool Sadio Mane, bai ji daɗin katin ba.
Ɓangarorin masu horar da tawagogin ƙasashen biyu duka sun harzuka a bayan fili.
Pape Gueye ya yi ƙoƙarin buga kwallo a kusa da ragar Masar, sai dai bai buga kwallon da ƙarfi ba - ba ta yi haɗari ba.
Senegal na da shot huɗu yayin da Masar ba ta da ko ɗaya kawo yanzu.
Senegal na ci gaba da mamaye wasan, sai dai ƴan wasan Masar na ƙoƙari wajen ganin sun dawo sun tsare gida da hana abokan karawarsu samun dama mai kyau.
Babu ƙungiyar da ta samu ƙwaƙƙwarar dama zuwa yanzu.
Koulibaly ba zai ji daɗin fita ba daga wannan wasa. Babbar asara ce a wajen ɗan wasan, musamman ma irin jagoranci da ke yi wa tawagar.
Jim kaɗan bayan samun katin gargaɗi, kyaftin ɗin Senegal Kalidou Koulibaly ya ji ciwo sannan ya kwanta a ƙasa.
Da alama raunin ba mai sauki bane.
Za mu iya cewa watakila ya buga wasansa na karshe a wannan gasar.

Asalin hoton, Reuters
Ɗan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson ya karɓi kwallo, inda ya ɗaɗa ta zuwa gidan Masar sai dai kwallon ta yi sama ta fita.
Wannan wata dama ce da tsohon ɗan wasan na Chelsea ya samu - amma ba ta yi amfani ba yanzu.