Abin da ya sa za mu saki ƴan fashin daji - Gwamnatin Katsina

Gwamnan Katsina

Asalin hoton, Dikko Umar Radda/X

Lokacin karatu: Minti 5

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta yi ƙarin haske kan rahotonnin da ke cewa tana shirin sakin wasu da ake zargi da kasancewa ƴan fashin daji da hukumomin suka kama a baya.

Rahotonnin wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa gwamnatin jihar na shirin sakin wasu ƴan fashin daji kimanin 70 da ake tsare da su, bayan kama su da zargin fashin daji da garkuwa da mutane.

Sai dai kwamishinan al'amuran tsaro da cikin gida na jihar, Hon. Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu ba a kammala tantance adadin mutane da gwamnatin ke shirin saki ba.

Ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin sakin mutanen ne kasancewa yana cikin sharuɗɗan yarjejeiniyar zaman lafiya da wasu al'umomin jihar suka cimma da ƴanbindigar a garuruwansu.

Sharuɗɗan yarjejeniyar

Kwamishinan tsaron jihar ya ce a lokacin da al'umomin jihaar suka cimma yarjejeniyar da ƴanbindigar akwai wasu sharuɗa da suka amince da su.

Sharuɗɗan da aka cimma a lokacin kamar yadda kwamshinan ya yi ƙarin haske sun haɗa da:

  • Bai wa ƴanbindigar damar shiga kasuwanni domin saye da sayarwa
  • Ba su damar zuwa asibiti domin neman magani da duba yan'uwansu
  • Ba su damar zirga-zirga zuwa inda suke so, ba tare da tsangwama ko kyara ba
  • Yin cuɗanya da jama'a
  • Daina kai hare-hare cikin garuruwa da ƙauyuka
  • Daina sace jama'a domin neman kuɗin fansa
  • Sakin mutanen da ake garkuwa da su
  • Sakin ƴan bindiga da ke hannun hukumomi

Ya kuma ce an riƙa aiwatar da sharuɗɗan daki-daki inda a yanzu aka isa kan sharaɗin da ake magana a kai (sakin ƴan bindiga da ake tsare da su).

Me ya sa gwamnati ta za saki ƴanbindigar?

Wasu yanbindiga a wurin sulhu

Asalin hoton, KTTV

Kwamishinan tsaron na Katsina Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar ta shiga cikin maganar ne "bisa la'akari da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a faɗin jihar sanadiyyar sulhun da aka yi".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya dai gwamnatin jihar ta sha bayyana wa duniya cewa ba za ta yi sulhu da ƴanbindiga ba, kodayake ba ta hana al'umomin garuruwan jihar yin hakan ba

To amma kwamishinan tsaron jihar ya ce abin da ya sa a yanzu gwamnatin jihar ta shiga maganar shi ne ''zaman lafiya da aka samu ta hanyar yarjejeniyar''.

''Gwamnatin jihar Katsina ta al'umma ce, don haka duk abin da al'umma suka yi domin zaman lafiyarsu, gwamnati ba za ta hana su ko watsa musu ƙasa a ido ba'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ci gaba tabbatar da cewa yarjejeniyar ta samar da zaman lafiya, kuma mutanen jihar ne suka tafiyar da yarjejeniyar, da kuma zaman lafiyar da aka samu, ta dalilin yarjejeniyar.

''Kuma a matsayinmu na gwamnati duk, abin da al'umma suka yi matsawar bai saɓa wa doka ba, to gwamnati za ta goyi bayansa don ci gaban al'ummarmu'', in ji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati ta ga alfanun sulhun, domin kuwa akwai garuruwa da suka kusan shekara guda ba tare da samun labarin harin ƴanbindiga a cikinsu ba.

''Alal misali ƙaramar hukumar Jibiya, tun ranar 28 ga watan Fabrairun 2025 da ka yi yarjejeniyar har yau ba a sake kai hari ba, haka ma ƙananan hukumomin Safana da Batsari, kai ƙananan hukumomi kusan 19 da ake da matsalar nan yanzu ta ragu da kusan kashi 95 cikin 100'', in ji shi.

Nasiru Mu'azu ya ce tun fara aiki da yarjejeniyar ƴanbindigar sun saki aƙalla mutum 1,000, "wanda hakan gagarumin ci gaba ne, da ya kamata gwamnati da duba domin cika musu alƙawarin da aka yi musu na sakin ƴan'uwansu".

''Wannan ƙoƙari da al'umma suka yi, to bai kamata kuma gwamnati ta watsa musu ƙasa a ido ba, wajen kasa cika alkawarin da suka yi da ƴanbindigan'', in ji shi.

Nasir Mu'azu ya kuma ƙara da cewa ko "a lokacin yaƙi ma, idan aka yi yarjejeniya tare da cimma alƙawura, to ya kamata a cika alƙawuran da aka ɗauka lokacin yarjejeniyar".

Su wa za a saki, kuma ta ya za a zaƙulo su?

...

Kwamishinan ya ce akwai kwamitocin sansanci na ƙananan hukumomin waɗanda su ne suke karɓar sunayen ƴanbindigar da ake tsare da su daga wajen ƴanbindigar da aka yi sasancin da su.

''Waɗannan kwamitoci su ke tattara sunayen kuma kawo yanzu ba a riga an kammala tattara sunayen ba, ballantana ma a san adadinsu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala tattara sunayen kwamitocin za su miƙa wa gwamnati, wadda ita kuma za ta bai wa kotunan da ke yi wa mutanen shari'a domin dubawa.

''Ita kotu, ita ce za ta duba, domin tattabar da bai saɓa wa dokokinsu ba, kafin aiwatar da shirin'', in ji shi.

Me ya sa babu ajiye makamai cikin sharuɗɗan?

Wasu makamai

Asalin hoton, Getty Images

Masana tsaro da masu sharhi da dama dai na nuna fargaba da damuwa kan yadda ake gudanar da sulhun ba tare da ajiye makaman ƴanbindigar ba.

A duk wuraren da aka yi sulhun akan ga hotuna da bidiyoyin yadda ƴanbindigar ke zuwa wuraren sulhu riƙe da manyan makamai, su kuma tafi da su bayan kammala sulhun.

Wani abu da wasu masana ke ganin tamkar nuna ƙarfi ƴanbindigar ke zuwa maimakon sulhu.

To sai dai kwamishinan tsaron jihar Katsinan ya ce shi ma wannan sharaɗin ana tafe za a je kansa sannu a hankali.

''Lokacin da aka fara ai cewa aka yi ba zai yiwuwa ba, amma sai ga shi ya yiwuwa, don haka shi ma wannan sharaɗin za a cimma shi'', in ji shi.

Haka ma Kwamishinan ya ce akwai wasu dalilai da aka yi la'akari da wasu rashin saka sharaɗin ajiye makaman ƴanbindigar.

Ya ce jihar Katsina na da tarin fulani da dukiyoyinsu masu tarin yawa da ke zaune a wuraren da ke kusa da dazuka masu yawa.

''To idan ba su da makaman da za su kare dukiyoyinsu wata rana wasu daga wata jihar ko wata ƙasar za su je har inda suke su sace musu dukiyoyinsu'', in ji shi.

Haka ma ya ce gwamnati na shirin yadda za ta toshe hanyoyin da suke samun makamai, kafin karɓe waɗanda ke hannayensu.

A shekarar da ta gabata ne dai wasu garuruwa da ƙananan hukumomin jihar Katsina suka fara yhin sulhu da ƴanbindiga a wani ɓangare na ƙoƙarin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar al'umominsu.

Matakin ya samar da sauƙi a wasu yankunan, duk da cewa a wasu yankunan an ci gaba da kokawa kan yadda irin waɗannan ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da al'umma.