Jihohin Najeriya 5 da siyasarsu ke ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027

Gwamnoni

Asalin hoton, multiple/social media

Lokacin karatu: Minti 5

Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin zaɓen shekarar 2027, za a iya cewa harkokin siyasa sun fara zafi a Najeriya, musamman a wasu jihohin ƙasar da suka yi fice wajen siyasa mai zafi.

A dokokin kundin hukumar zaɓen ƙasar ta INEC, har yanzu ba a fitar da jadawalin zaben 2027 ba, balle a san lokacin fara siyasa gadan-gadan.

To amma tun daga shekarar da ta gabata ne siyasa ta ɗauki zafi a wasu jihohin Najeriya, inda ƴan siyasa suka riƙa sauya sheƙa, a wasu wuraren aka fuskanci hargitsi a wasu jihohi kuma ake ta musayar yawu.

BBC ta yi nazari kan jihohin Najeriya da siyasarsu ke daukan hankali gabanin zaɓen na 2027.

Kano

A halin da ake ciki a yanzu za a iya cewa gajimaren rashin tabbas ya lullube sararin samaniyar siyasar Kano, tun bayan rade-radi masu karfi da ke nuna cewa gwamnan jihar Abba Kabir ya gama kulle kayansa, domin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP mai mulki jihar zuwa APC, wadda ba a ga-maciji tsakaninsu.

Babban abin mamakin shi ne ana ganin cewa Gwamna Abba zai yi gaban kansa ne zuwa APC, ba tare da amincewar ubangidansa, Rabiu Kwankwaso ba.

Kamar yadda ake cewa siyasar Kano, sai ɗan Kano. Za a iya cewa an ga haka a yanayin siyasar wannan lokaci.

Kano ta daɗe tana ɗaukar hankali a fagen siyasa Najeriya tun a zamanin marigayi Malam Aminu Kano.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan zaɓen 2023, da NNPP ta doke APC a zaɓen gwamnan jihar ne aka fara sabuwar siyasar jihar.

Bayan zaɓen ne aka fara samun musayar yawu tsakanin ɓangaren Ganduje da ɓangaren Kwankwasiyya, sannan daga baya aka samu ɓangaren Sanata Barau Jibrin, musamman bayan da ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Daga baya saɓani ya fito fili tsakanin ɓangaren Ganduje da ɓangaren Barau, inda na kusa da Barau suka fara tallata shi a matsayin wanda ya fi cancanta ya yi takarar gwamna a jam'iyyar APC.

An ga yadda wasu ƴan jihar suka rasa wasu muƙamai, ko da aka rasa baki ɗaya ko aka canja da wasu, lamarin da ake alaƙantawa da siyasar jihar.

A yanzu da aka fara raɗe-raɗin cewa gwamnan jihar na yunƙurin komawa APC, sai lissafin ya fara sauyawa, inda aka ga ƴan asalin APC ɗin suna yada wa juna magana, wasu na maraba, wasu na guna-guni, yayin da ita NNPP wasu ke jifar abokansu da cin amana.

Siyasar Kano na jan hankali sosai, inda ake yawan tafka muhawara kan abubuwan da ke faruwa a wasu jihohin da dama na ƙasar.

Rivers

A jihar Rivers siyasar ta dagule, kuma babu wanda ya san mene ne zai faru sai Allah.

Hamayyar siyasa tsakanin gwamna mai ci Siminalayi Fubara da magabacinsa, kuma minista mai karfin fada a ji, Nyesom Wike ta jefa jihar cikin rikicin da babu wata jiha da ta fada makamancinsa a cikin sama da shekara biyu da aka kwashe bayan babban zaben 2023.

Yanzu haka batu ake yi na tsige gwamnan jihar.

Labarin sake yunƙurin tsige gwamnan jihar da ƴan majalisar jihar, waɗanda na kusa da Nyesome Wike ne ya ja hankalin mutane, musamman a fagen siyasar Najeriya.

Ana kallon dai rikici tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, da ubangidansa Minista Nyesom Wike a matsayin fafutikar ƙwatar iko da siyasar jihar mai arzikin man fetur.

Kusan za a iya cewa Wike ne ya yi uwa da makarɓiya wajen tabbatar da Fubara ya zama gwamnan jihar domin ya gaje shi bayan ya kammala wa'adinsa na biyu na mulki.

Tun a shekarar 2023 bayan samun nasara a zaɓen ne shugabannin biyu suke takun-saƙa a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo da magana a faɗin ƙasar.

Tun a farko-farkon mulkin Fubara aka fara rikici a game da shugabannin ƙananan hukumomi, inda bayan wa'adin waɗanda Fubara ya gada daga Wike ya ƙare, ya buƙaci su tafi, su kuma suka ce allambaran suna da sauran lokaci.

Ana cikin wannan ne ya sanar da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya domin su maye gurbin waɗancan, lamarin da ya tayar da tashin hankali a jihar.

Daga baya ƴan majalisar jihar da ke tare da Fubara sun sanar da tsige mafi yawan ƴan majalisar da ke tare da Wike, lamarin da ya ƙara ta'azzara rikicin siyasar jihar, sannan Fubara ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, inda mutanensa suka lashe.

Daga bisani kotun ƙoli ta ta soke zaɓen, sannan ta soke cire ƴan majalisun, tare da umartar Fubara ya je gabansu ya gabatar da kasafin kuɗi.

Ana cikin haka ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan, tare da naɗa gwamnan riƙon-ƙwarya na wata shida, sannan ya jagoranci sulhunta Wike da Fubara.

Bayan sulhun ne aka yi sabon zaɓen ƙananan hukumomi, inda mafi yawansu suka kasance na kusa da Wike.

Sai tun bayan da Fubara ya sanar da komawa APC ne rikici ya ƙara komawa ɗanye, inda aka fara rikici kan waye ya kamata ya jagoranci tallata Tinubu.

Legas

Duk da cewa rikicin siyasar jihar Legas bai cika fitowa fili ba, amma lallai jihar tana fama da rikice-rikice.

An ga yadda aka kayar da tsohon gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode a takarar fitar da gwani saboda ya samu saɓani da shugaban ƙasa na yanzu, Bola Tinubu. Haka kuma kafin shi, ana tunanin tsohon gwamnan jihar, Babatunde Fashola ma da ƙyar ya sha wajen komawa wa'adi na biyu.

Shi ma gwamna na yanzu, an ga yadda a watannin bayan Tinubu ya je Legas, amma ya ƙi gaisawa da shi duk da cewa ya je tarbarsa, sannan ana yaɗa jita-jitar cewa Seyi Tinubu zai tsaya takarar gwamnan jihar.

Amma a ranar 13 ga watan Janairun 2025 siyasar jihar ta ɗauki zafi bayan ƴan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige kakakin majalisar, Mudashiru Obasa bayan sun zarge saɓa dokokin majalisa da kuma almundahana.

Tuni dai majalisar ta maye gurbinsa da mataimakinsa Mojisola Meranda.

Misis Meranda, wadda ke wakiltar mazabar Apapa 1, ta kasance tsohuwar mai tsawatarwar majalisar. Yayin da Mojeed Fatai ya kasance sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin ta jihar Legas.

An tsige Obasa ne wata guda bayan da ake zarge shi da kashe Naira biliyan 17 wajen gyara kofar da ke kai wa majalisar.

Sai ba da daɗewa ba aka fara cewa ba da yawun Tinubu aka tsige Obasa ba, lamarin da ya sa daga baya da kanta sabuwar shugabar majalisar ta sauka, inda Obasa ya koma kujerarsa.

Kaduna

A wannan karon za a iya cewa siyasar jihar Kaduna ta ƙara zafi sama da yadda aka saba gani a zaɓukan baya, lamarin da ba zai rasa nasaba da kasancewar El-rufai a jam'iyyar hamayya ba.

Amma ko a zaɓen 2019 da 2023 an yi gwagwarmaya a siyasar Kaduna, musamman tsakanin gwamna Nasiru da wasu tsofaffin abokan siyasarsa irin su Sanata Shehu Sani da Othman Hunkuyi da sauransu.

Gwamnan jihar Kaduna na yanzu Uba Sani da Nasiru El-Rufai dai abokai ne, kuma El-Rufai ne ya shige gaba wajen ganin Uba Sani ya gaje shi a kujerar gwamnatin jihar ta Kaduna.

Sai dai ba daɗe ana ɗasawa ba, inda tun ana ɓoyewa har abin ɓoye ya fara fitowa fili, inda ɓangarorin makusantan junan biyu suka fara musayar yawu.

Daga bisani tsohon da kansa ya fito ya yi zargin cewa da hannun gwamnan mai ci ake masa bi ta da ƙulli, sannan ya ƙuduri aniyar ganin ya jagoranci kayar da gwamnan a zaɓe mai zuwa.

Wani abu da yake sa siyasar jihar Kaduna ke ƙara zafi da ɗaukar hankali shi ne batun addini da ƙabilanci, inda ɓangaranci ke taka rawa sosai wajen juya akalar siyasar jihar.

Zamfara

Jihar Zamfara ta shiga wannan jerin ne ganin yadda siyasar jihar mai arzikin ma'adinai ta yi zafi sosai a wannan karon.

Siyasar Zamfara ita ma ta daɗe tana zafi, amma tun bayan da gwamna Lawal Dauda ya doke Bello Matawalle, sannan Tinubu ya naɗa Matawalle a matsayin minista, sai siyasar ta ƙara jan hankali.

Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar tsaro, inda kusan kowane ɗan siyasar yake sanya batun magance matsalar a cikin abubuwan da yake fata zai yi idan ya samu dama.

An dai sha jin gwamnan na cewa ana masa katsalandan a harkokin tsaron jiharsa, inda ya ce daga gwamnatin tarayya ake shirya sulhu da ƴanbindiga, lamarin da ya ce ko kaɗan ba zai lamunta ba.

Ana dai ganin Matawalle na da burin sake tsayawa takarar gwamnan jihar ta Zamfara, inda zai fafata da gwamna mai ci na yanzu, wanda ya doke shi.