Manyan buƙatun da ƴanbindiga suka gabatar wa gwamnatin Katsina

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda

Asalin hoton, Dikko Umaru Radda/FB

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda
Lokacin karatu: Minti 4

Matsalar ƴanbindiga da ke addabar wasu jihohin arewacin Najeriya na ci gaba da kasancewa alaƙaƙai, inda gwamnatoci da masana ke ta muhawara kan yadda za a iya shawo kan matsalar.

Yayin da wasu jihohi suka dage kai da fata cewa babu batun sulhu, wasu kuma sun rungumi tattaunawar da ƴan fashi, kuma suna ganin wannan ne abin da ya fi dacewa da su.

Katsina na cikin jihohin da matsalar ta yi katutu, kuma a baya gwamnatinta na cikin waɗanda suka dage kan cewa ba za su taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba, sai dai wani sabon salo da aka gani shi ne yadda al'umma ke jagorantar tattaunawar sulhu da ƴan bindiga a jihar.

Hakan ba zai rasa nasaba da sake taɓarɓarewar tsaro a yankunan jihar ba.

Wasu daga cikin munanan hare-hare da ƴan fashin dajin suka kai a baya-bayan nan da suka girgiza al'umma, an kai su ne a jihar ta Katsina, kamar lokacin da ƴanbingigan suka kashe mutane 28 da ke ibada a cikin masallaci.

A farkon wannan mako gwamnatin jihar ta yi wani babban taron tattaunawa kan matsalar domin nemo mafita, kuma kwamishinan tsaro na jihar ya yi bayani kan halin tsaro da jihar ke ciki, har ma ya tabbatar wa BBC shirin jihar na biya wa ƴan bindigan wasu buƙatu da suka miƙa domin ganin an samu zaman lafiya.

Mene ne buƙatun da ƴanbindiga suka gabatar?

Kwamishinan tsaro na jihar Katsina Nasiru Mu'azu ya tabbatar wa BBC cewa ƴan fashin dajin sun gabatar da wasu manyan buƙatu:

  • Gina makarantu
  • Gina asibitoci
  • Mashayar dabbobi
A cikin shekara ta 2023 ne gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da dakarun Katsina Security Watch domin yaki da matsalar tsaro

Asalin hoton, Dikko Umaru Radda/FB

Tun asali masana tsaro a Najeriya sun sha alaƙanta matsalar ƴan fashin daji da rashin samar da ababen more rayuwa da kuma samar da doka a yankunan karkara.

Ko a cikin bayanin da ya yi a lokacin taron masu ruwa da tsakin na Katsina, kwamishinan ya bayyana "rashin adalci a cikin manyan abubuwan da suka haifar da matsalar fashin daji da kuma ta garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Kuma duk da dagewar da gwamnatin jihar ke yi kan cewa har yanzu ba ta da aniyar tattaunawa da ƴan fashin daji, to amma kwamishinan ya bayyana rushewar shirin yafiya na gwamnatin a matsayin abin da ya ƙara ta'azzara matsalar tsaro a jihar.

"Kwamishinan ya bayyana yadda matsalar ƴanbindiga ta yadu daga ƙananan hukumomi biyar na jihar tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2015, zuwa ƙananan hukumomi 25 a shekarun 2015 zuwa 2023 sanadiyyar rushewar shirin yin afuwa," in ji sanarwar bayan taro da aka fitar.

Ko ya kamata a biya wa ƴanbindiga buƙatunsu?

Kabiru Adamau, wanda masanin tsaro ne a Najeriya ya ce matakin da gwamnatin Katsina ta ɗauka zai iya taimakawa wajen magance matsalar tsaron da take fama da ita.

"Cikin dalilan da ke jawo matsalar (ƴanbindiga) shi ne an zalunci wasu daga cikinsu, kuma idan ba a ba su tallafi ba, ba za a iya kawo ƙarshen matsalar ba," in ji Kabiru Adamu.

Sai dai ya ce ba dukkan su (ƴanbindiga) ne ya kamata a bai wa tallafi ba, "wajibi ne a tantance waɗanda suka kamata a taimaka mawa ba, saboda akwai cikinsu waɗanda suka mayar da sata a matsayin sana'a, bai kamata a taimaka wa wanda yake sata, yake cin zarafin al'umma ba domin kada a ƙara masa ƙwarin gwiwa," a cewar masani.

Sulhu gwamnatin Katsina ke yi da ƴanbindiga?

Baya ga yadda za a shawo kan matsalar tsaro, wata muhawarar da ta fi zafi game tsakanin jihohin da ke fama da matsalar tsaro ita ce yin sulhu ko kuma amfani da ƙarfi wajen magance matsalar ƴan fashin daji.

A cikin sanarwar bayan taron da gwamnatin Katsina ta fitar ta ce "Ba gwamnatin (Katsina) ce ta kawo batun yarjejeniyar zaman lafiya da ƴanbindiga ba - al'umma ne suka buƙaci hakan.

"Shugabannin ƙauyuka ne suka tattauna da ƴanbindiga da suka tuba, abin da ya kai ga yin yarjejeniyar zaman lafiya a ƙananan hukumomin Dan Musa da Jibiya da Batsari da Kankara da Kurfi da kuma Musawa."

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda

Asalin hoton, Dikko Umaru Radda/FB

A wata uku na farkon shekarar 2025, wani rahoto na kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya ya ce an kashe mutum 341 da yin garkuwa da mutum 495 a hare-hare 247 da aka kai a jihar.

A watan Yuli gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta ƙaddamar da wani shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai ba da jimawa ba.

Gwamnatin ta ce za a buɗe azuzuwan koyar da karatu da dubarun koyar da sana'o'i domin sauya tunanin ƴanbindigar, inda daga bisani za su koma cikin al'umma.

Hukumar da ke kula da ilimin manya ta jihar ce ke da alhakin tsara yadda shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar zai kasance.

Ƙarƙashin shirin za a bai wa waɗanda suka miƙa makamansu damar koyon karatun zamani da na addinin musulunci tare da fahimtar da su illar kisan mutane da kuma neman fansa.