Ko gwamnatin Najeriya ta san maɓoyar ƴanbindiga, me ya sa ta gaza kawar da su?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC New, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 7
Batun sanin maɓoyar ƴanbindiga da suka addabi wasu jihohin arewa maso yammaci na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.
A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi iƙirarin cewa ya san maɓoyar ƴanbindigar da ke addabar jiharsa.
A cikin wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa, Gwamna Lawal ya yi iƙirarin cewa zai iya maganace matsalar cikin wata biyu in da yana da iko.
''Na san inda ƴanbindigar suke, amma babu yadda zan iya kawar da su tun da ba ni da iko da jami'an tsaro, suna karɓar umarni ne daga sama (Abuja)'', in ji shi.
''Na rantse da Allah, duk inda wani shugaban ɗanbindiga yake a cikin jihar nan, na sani, in ma ya fita daga jihar nakan sani, da wayar hannuna zan iya nuna maka inda suke a yau, amma ba abin da za mu iya, tun da abin ya fi ƙarfinmu'', in ji gwamnan.
Iƙirarin gwamnan ya haifar da muhawara tsakanin yan ƙasar har ma da masana inda wasu ke ɗiga ayar tambaya.
To amma mece ce gaskiyar iƙirarin Dauda Lawal?
Za a iya sanin maɓoyar ƴanbindiga?
Audu Bulama Bukarti, lauya kuma mai bincike kan ayyukan ƙungiyoyin ƴanbindiga a Afirka ya ce maganar Gwamna Dauda Lawan ba wani sabon al'amari ba ne.
''Duk wanda ke zaune a wasu ƙauyukan Zamfara da Sokoto da Kebbi da Kaduna da Neja, inda waɗannan ƴanbindigar suke, za su gaya maka inda suke kama daga Lakurawa da ƴan fashin daji'', in ji shi.
Shi ma Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce a bayyana take wajen sanin maɓoyar ƴanbindiga a Najeriya.
''An san inda suke an san abubuwan da suka mallaka da sana'o'insu da abubuwan da suka sanya suka faɗa harkar''.
A ina ƴanbindigar suke?

Asalin hoton, Getty Images
Barista Bukarti ya ce yankunan da suka yi ƙaurin suna dangane da zama maɓoyar ƴanbindiga a arewa maso yammacin Najeriya sun haɗa da:
- Wasu yankunan ƙaramar hukumar Isa: Dakta Bukarti ya ce idan ka fita daga shalkwatar ƙaramar hukumar Isah, akwai wuraren da ƴanbindigar Lakurawa suka yi sansani.
- Haka ma ya ce a wasu yankunan jihar Kebbi akwai wuraren da an sani Lakurawa sun yi sansani a wurin, suna cin karensu babu babbaka, mutanen yankunan sun sani.
Dakta Kabiru Adamu kuwa ya ce wasu ƴanbindigar suna rayuwa a dazukan da aka sani, wasu ma a cikin jama'a suke rayuwa.
'"Shi ɗan bindiga idan ya gawurta sai ya bar daji ya koma cikin gari ya kori mutane domin mallakar garin,'' in ji Kabiru Adamu.
Bukarti ya zayyano wasu dazuka bakwai da ya ce sun yi ƙaurin suna wajen zama mafakar ƴanbindiga da suka haɗa da:
- Dajin Rugu (wanda ya ratsa Katsina da Kaduna da Zamfara da Neja)
- Dajin Kamuku (Wanda ke yankin Birnin Gwari)
- Dajin Kuyanbana ( Wanda ke tsakanin Kaduna da Zamfara)
- Dajin Kuriga/Gwari (Da ke jihar Kaduna)
- Dajin Dansadau (Wanda ke jihar Zamfara)
- Dajin Sububu (A jihar Zamfara)
- Dazukan Faskari da Safana (A jihar Katsina)
Ta waɗanne hanyoyi ake gane maɓoyar ƴanbindiga?

Asalin hoton, Getty Images
Bulama Bukarti ya ce kawai hanyoyi da dama da za a iya gane maɓoyar ƴanbinbiga.
- Ɗaya daga cikin hanyoyin gane su shi ne wayar da suke yi, kamar yadda Bukarti ya bayyana.
- Idan gwamnati tana so za ta iya bibiyar duka wayoyin da ake yi a Najeriya domin kamo waɗanda suke yi'', in ji shi.
- Amfani da fasaha don gano wurin da suka naɗi bidiyo. Bukarti ya ce idan aka yi amfani da hanyar fasaha mafi sauƙi za a iya gano inda ƴanbindigar ke naɗar bidiyoyinsu.
- ''Ta hanyar amfani da hotunan tauraron ɗan'adam za a iya gano wurin da suka naɗi bidiyon'', in ji Bukarti.
- Mutanen ƙauyukan sun san inda ƴanbidnigar suke, kuma ita hanyar tattara bayanan sirri za a iya jin labarinsu ta hanyar waɗannan mutane.
- Yadda suke tafiya a kwamba. Bukarti ya ce mafi yawan ƴanbindigar sukan tafi a kwambar babura 100, ko 200 ko wani abu makamancin haka, ''To ka ga duk inda waɗannan babura suka taho za su tayar da ƙura da ƙarar ta yadda za a iya sanin inda suka taho ko suka nufa''.
- Amfani da jirage marasa matuƙa: Bukarti ya ce akwai fasahar zamani mai sauƙi da za a iya gane maɓoyar ƴanbindiga, ''Akwai ƙananan jirage marasa matuƙa da za a iya saka musu wata na'urar da za su gane bindiga domin sanar da kai, duk inda suka hango wanda ke ɗauke da bindiga za su iya gano shi''.
Me dokar soji ta ce kan bin umarni?

Asalin hoton, Defence HQ/X
Dangane da batun da gwamnan Zamfarar ya yi cewa ba shi da iko da jami'an tsaron da ke yaƙi da ƴanbindigar, Bulama Bukarti ya ce a tsarin dokokin da suka shafi soja a Najeriya, gwamna ba shi da iko kan sojoji a abin da ya shafi kai hari.
''Haka ma ministan tsaro ko mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro duka ba su da hurumin umartar sojoji su kai hari''.
Bukarti ya ce wanda ke da ikon hakan shi ne shugabana ƙasa kaɗai, wanda shi kuma yakan bayar da umarnin ta hanyar manyan hafsoshin tsaron ƙasar.
''Kuma daga bayanan da muke samu ba a bai wa sojojin umarnin ''standing order'', wato idan kuka ga abu kaza ku kai hari, dole sai sun samu umarni, ko suna tsaka da yaƙi idan akwai buƙatar janyewa, dole sai sun jira umarni daga sama'', in ji shi.
'Abin da ya sa aka kasa kawar da ƴanbindiga'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bulama Bukarti ya ce a ganin shi abubuwa uku ne suka sa gwamnati ta kasa magance matsalar ƴanbindiga a Najeriya.
Mummunan sakaci a ɓangaren gwamnati.
Fitaccen lauyan ya ce ba ya zargin gwamnati cewa da gangan ta kasa kawo ƙarshen ƴanbidiga a ƙasar, sai dai ya ce akwai mummunan sakaci daga ɓangaren gwamnatin.
''Za ka ga gwamnati ta kai jirage Katsina ko Zamfara, kuma mutanen gari su hango maharan sun taho, su kuma yi gaggawar sanar da jami'an tsaron, amma sai su ce babu yanayi mai kyau da jirgi zai tashi'', in ji shi.
Bukarti ya ce ya kamata gwamnati ta samar da wata hanya mai sauƙi da jami'an tsaron za su iya kai ɗaukin gaggawa idan aka buƙace su.
''A lokuta da dama kafin kai hari jami'an tsaro kan samu bayanan sirri game da harin amma ba sa ɗaukar matakai, har sai an kai harin,'' in ji Bukarti
Cin hanci da rashawa
Bukarti ya ce matsala ta biyu ita ce mummanar cin hanci da rashawa da ake samu a ɓangaren yaƙi da ƴanbindiga a Najeriya.
''Kama daga harkar sayen makamai zuwa yadda ake tafiyar da yaƙin, duk cin hanci ya yi katutu'', a cewar lauyan.
''Don haka cin haci da rashawa ne ya sa ake shigar da makamai wurin ƴanbindigar'', in ji Bukarti.
Rashin cikakkiyar manufar gwamnati kan yaƙi da ƴanbindiga
Dakta Bulama Bukarti ya ce har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta da wata cikakkiyar manufa kan yaƙi da ƴanbidiga.
''Yau su ce maka yaƙi suke yi, gobe su ce maka sulhu suke yi, sai ka rasa mene ne ainihin manufarta'', in ji shi.
"Gwamnatin nan yau shekararta biyu, amma har yau ba ka taɓa jin gwamnanonin yankin arewa maso yamam sun zauna tare da mai bai wa shugaban shawara kan tsaro da manyan hafsoshin tsaron ƙasar don magance matsalar ko fito da wata manufa ba'', in ji shi.
Barista Bukarti ya ce wannan shi ne dalilin da zai sa idan aka yi sulhu da ƴanbindiga a Kaduna gobe sai su tafi Katsina su kai hari, kuma su koma Kaduna su yi zamansu.
Shi kuwa Dakta Kabiru Adamu ya ce a ganinsa abu biyu ne ke kawo tarnaki a yaƙi da ƴanbindiga.
Rashin sa ido da ladabtarwa
Masanin tsaron ya ce wannan na da asali da yadda ƴansiyasa ke sakaci wajen ladabtar da jami'an tsaro.
''Za ka ga an bai wa mutum damar kare wani yanki, kuma a kai masa hari amma duk da haka sai a kasa ladabtar da wanda ke da alhakin kare yankin'', in ji shi.
Siyasa
Dakta Kabiru Adamu ya ce siyasa na taka muhimmiyar rawa wajen rashin kawo ƙarshen matsalar ƴanbindiga.
''Wani sashen za ka ga an ƙi ɗaukar matakin ne domin kada matsalar ta shafi siyasar wani'', in ji shi.
Ta yaya za a kawar da ƴanbindiga?

Asalin hoton, Getty Images
Fitaccen lauyan ya ce idan ana son kawar da ƴanbindiga a Najeriya hanya biyu ya kamata gwamnati ta bi.
- Buɗe musu wuta
Na farko shi ne a jibge tarin sojoji a duka dazukan da ake tsammanin ƴanbindigar na ciki, a yi musu ƙofar rago ta ko'ina.
''A buɗe musu wuta, sannan a tura jiragen sama da jirage marasa matuka su riƙa tattaro bayanan da ke cikin dajin suka aika wa na waje, domin sanin matakan da za su ɗauka'', in ji shi.
Lauyan ya ce yadda ƴanbindigar ke sace mutane da dama su shigar da su cikin daji, idan jiragen marasa matuƙa suka riƙa shawagi a sama za su gan su.
''Duka waɗancan dazukan akwai inda ya haɗa su, don haka sai a yi ƙoƙarin mamaye mahaɗar tasu'', in ji Bukarti
- Buɗe ƙofar tuba
Bukarti ya ce bayan kamar wata shida ana yi musu wuta, an datse kai musu makamai da ƙwayoyi da abinci, "dole za su yi la'asar".
''Daga nan sai a buɗe musu ƙofar tuba, a ce duk wanda ke son tuba ya je wuri kaza ya gabatar da kansa, ya mika wuya'', in ji shi.
Bukarti ya ce ba sulhu za a ce ba, tuba za a ce don haka za su ga afuwa aka yi musu, maimakon sulhu da suke ganin za su saka sharuɗa.











