Inec ta sauya ranar zaɓen shugaban Najeriya na 2027

Hukumar zaben Najeriya

Asalin hoton, X/Inec

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta sanya sabbin ranakun gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma na ’yan majalisun tarayya da na jihohi na kasar na 2027.

Hakan na zuwa ne mako biyu bayan hukumar ta fitar da jadawalin zaben na farko, wanda ya sha suka daga bangarori da dama kasancewar ranakun da hukumar ta sanar za su iya fadawa cikin watan azumin Ramadana na shekarar 2027.

Lamarin ya kai ga cewa majalisar dokokin kasar ta yi gyara ga dokar zaben kasar game da lokaci mafi kankanta na sanar da ranar gudanar da zabe.

A jadawalin farko da hukumar ta fitar, ta sanya ranar 20 ga watan Fabarairun 2027 a matsayin ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, sai kuma 6 ga watan Maris 2027 a matsayin ranar zaben gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.

Sa dai a cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Fabarairun 2025, wadda ta samu sa hannun shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a Mohammed Kudu Haruna, ta ce: “bayan yin gyara ga dokar zabe ta 2022, da kuma amincewa da dokar zabe ta 2026, hukumar ta yi gyara tare da sauye-sauye ga lokutan shirye-shiryen zabe da kuma na zabukan domin ya yi daidai da tsarin sabuwar doka”.

Sabbin kwanan watan zabukan 2027

Sabbin ranakun babban zaben Najeriya na 2027, kamar yadda hukumar ta fitar su ne:

  • Zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya: Asabar, 16 ga watan Janairun 2027
  • Zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi: Asabar, 6 ga watan Fabarairun 2027

Ayyukan gabanin zabe

Sanarwar da hukumar ta fitar ya ci gaba da cewa “bisa dogaro da sabon jadawalin”, hukumar ta amince da wadannan kwanakin wata domin shirye-shiryen zaben:

Za a gudanar da zaben fitar da ‘yan takara, da kuma warware duk wata takaddama da za ta taso a lokacin zabukan, daga ranar 22 ga watan Afrilun 2026 zuwa 30 ga watan Mayun 2026.

Za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya daga ranar 19 ga watan Agusta 2026.

Yakin neman zaben gwamnoni da na ’yan majalisar dokokin jihohi zai fara daga ranar 9 ga watan Satumban 2026.