Rashford ya tsawaita zamansa a Barca, Gordon zai iya tafiya Arsenal

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan Manchester United Marcus Rashford, wanda ke zaman aro a Barcelona ya amince da sabuwar yarjejeniya da kungiyar. Aston Villa ta kwallafa rai kan dan wasan gaban Chelsea Nicolas Jackson, Real Madrid na son dan wasan Manchester City Rodri.

Dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekaru 28, ya amince da yarjejeniyar shekaru uku da Barcelona, ​​kuma kungiyar ta Spain na da niyyar biyan kudin da ya kai fam miliyan 26 domin kulla yarjejeniyar din-din-din da dan wasan a lokacin bazara. (Sports Spanish)

Dan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson mai shekaru 24 na Chelsea, wanda ke buga aro a Bayern Munich, da kuma dan wasan gaban Guinea na Borussia Dortmund Serhou Guirassy, ​​mai shekaru 29, suna cikin yan wasan da AC Milan ke sha'awar saya. (Gazzetta dello Sport)

Aston Villa na sha'awar sayan Jackson yayin da take shirin barin dan wasan gaban Ingila mai shekaru 30 Ollie Watkins ya tafi a lokacin bazara. (Football Insider)

Real Madrid na son sayen dan wasan tsakiya na Manchester City mai shekaru 29 Rodri, inda farashin dan wasan na Spain zai kai fam miliyan 44. (Radio Marca)

Ana rade-radin cewa ɗan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon zai koma Arsenal (Sky Sports)

Atletico Madrid da Juventus da Newcastle na neman siyan ɗan wasan gaba na Uruguay mai shekaru 26 Darwin Nunez, wanda ya koma Al-Hilal ta Saudi Pro. (Football Insider)

Juventus ta sanya ɗan wasan gaban Faransa mai shekaru 27 Randal Kolo Muani, wanda ke zaman aro a Tottenham daga Paris St-Germain, a matsayin babban ɗan wasan da take nema a lokacin bazara. (Tuttosport)

Ana rade-radin cewa tsohon kocin Ingila Gareth Southgate zai karbi Manchester United amma ya ce "ba ya neman wani aiki a yanzu'' (Football Boardrrom Podcast)

Kocin AC Milan Massimiliano Allegri ya yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa yana la'akari da makomarsa a ƙungiyar Serie A. (Football Italia)