Yadda APC da ADC ke cacar baki kan rikicin siyasar Edo

APC da ADC

Asalin hoton, OTHER

Lokacin karatu: Minti 3

Ana ci gaba da cacar baki tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, da kuma jam'iyyar hamayya ta ADC, dangane da harin 'yan bindiga da suka kai wa wasu kusoshin jam'iyyar adawar a jihar Edo.

Jam'iyyar APC ta yi watsi da zargin da ta ce ADC ta kakaba mata kan aukuwar lamarin.

APC ta kuma bukaci a zurfafa bincike kan harin da aka kai, inda ta ce kamata ya yi a fara bincken daga cikin jam'iyyar ADC, saboda wata hatsaniya da ta taso a sakamakon rarrabuwar kawuna a wajen taron jam'iyyar na jihar Edo.

Martani na baya-bayan nan a cacar bakan da ta sarke, ya fito ne daga Mista Felix Morka, sakataren yada labarai na jam'iyyar APC na kasa, wanda ya ce jam'iyyar ADC ta zargi APC da hannu a harin da aka kai kan 'yan jam'iyyar adawar a jihar Edo, kuma ta kwatanta harin da cewa wani aiki ne na ta'addanci da APC ta tafka.

"Mun dauki wadannan zarge-zarge a matsayin kalamai na rashin hujja da ba a yi la'akari da sakamakonsu ba, wadanda kuma hakan gaba daya wani rashin hankali ne,"In ji Mista Felix.

Abin da jam'iyyar ADC ta bayyana wani riga malam masallaci ne, kafin 'yansanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan abin da ya auku a jihar Edo.

Kasancewarmu jam'iyya mai mulki, ba hakan na nufin duk wani mugun abu da ya auku a Najeriya, daga jam'iyyar ya fito ba. Idan ka yi zargi, wajibi ne ka kafa shaida." a cewar Mista Felix.

Kazalika kakakin jam'iyar APCn ya kuma bayar da shawara inda ya ce," Na yi kira ga 'yan sanda da su gudanar da cikakken bincike, na kuma ba su shawara da su fara binciken nasu daga kan ita jam'iyyar ADC, domin kuwa rahotanni sun nuna cewa akwai zazzafan rikici tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar ta Edo."

Martanin da jam'iyyar APC ta mayar, ya gamu da raddi daga jam'iyyar adawar ta ADC, inda daya daga cikin masu magana da yawunta Faisal Kabir, ya shaida wa BBC cewa, idan APC ta musanta kai wannan hari, ai a baya an kai wa Abubakar Malami irin wannan hari.

"Haka ma an kai wa Malam Nasir el-Rufa'i hari da wasu mutane duk an kai musu irin harin, saboda haka halayya ce ta jam'iyyar APC kamar yadda ta bari 'yan bindiga suna sace mutane a wasu garuruwa ake kuma kai wa talakawa hari," In ji Faisal Kabir.

Wannan gutsuri tsoma dai ta taso ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da jam'iyyar adawa ta ADC, sakamakon wani hari da ake zargin wasu 'yan bindiga sun kaddamar a sakatariyar ADC, da gidan wani jigon jam'iyyar adawar, John Odigie Oyegun, a birnin Benin na jihar Edo, a ranar Talatar 24 ga watan Fabrairun, 2026.