Me ya janyo rikicin jagoranci a jam'iyyar ADC?

Asalin hoton, Social Media/David Mark
Da alama tun ba aje ko'ina ba rikicin cikin gida ya fara a jam'iyyar haɗaka ta ADC, bayan da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ya ce yanzu shi ne jagora mai cikakken iko na jam'iyyar.
Hakan dai na faru ne a daidai lokacin da ƴan jam'iyyar ke iƙararin gujewa rikice-rikicen cikin gida daga jam'iyyunsu na asali da suka baro da suka haɗa da PDP, da APC da LP da kuma NNPP.
Masu fashin baƙi sun sha nanata cewa ita kanta sabuwar tafiyar ba ta tsira ba daga rikicin cikin gida da ke faruwa sakamakon abubuwa da dama da suka haɗa da rashin adalci wurin kasafta jagorancin jam'iyya da ma zarge-zargen da ake yi wa jam'iyya mai mulki na rikita jam'iyyun hamayya.
Me ya faru?
A ranar 2 ga watan Yuli ne dai tsohon shugaban jam'iyyar ADC, kuma wanda ya kafa ta, Ralph Nwosu, ya sanar da rushe jagorancin jam'iyyar domin bai wa sabbin ƴan hamayya da suka shiga jam'iyyar dama.
Hakan ne kuma ya bai wa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata David Mark damar kasancewa shugaban jam'iyyar haɗakar ta ADC.
To sai dai kasa da wata ɗaya da yin hakan sai aka jyo tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Gombe, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ADC, Nafi'u Bala yana ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar haɗakar a yanzu.
Nafi'u wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja ya zarki shugaban jam'iyyar ta ADC na yanzu, tsohon shugaban majalisr dattawan Najeriya, Sanata David mark da ƙwace ragamar jagorancin jam'iyyar da kuma yi wa kundin tsarin jam'iyyar karsantsaye.
Nafi'u Bala ya kuma sha alwashin ƙalaubalantar al'amarin da ya bayyana da "juyin mulkin siyasa ido biyu daga baƙi" a gaban kuliya.
"David Mark ban ma san lokacin da ya shigo jam'iyyar ADC ba. Abin da na sani shi ne shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa ya sanar da cewa ya ajiye muƙaminsa. To ni a matsayina na mataimaki daga cikin mataimakansa na ƙasa ban ajiye mukamina ba.
"To dokar tsarin mulkin jam'iiyarmu da tsarin mulkin ƙasa da ma dokokin zaɓe na ƙasa sun ba ni iko da dama kai tsaye na kasance shugaban jam'iyyar na ƙasa." In ji Nafi'u Bala.
Dangane kuma da tambayar da aka yi masa cewa ko me ya sa ya yarda ya ajiye muƙaminsa a lokacin da jagororin jam'iyyar suka amince su rushe tsarin jagorancin domin sake sabuwar tafiya sai ya ce:
"Kafin ranar ma ni na je na sanar tunda ina da masaniyar suna da wannan ƙulleleniyar cewa za su yi wannan abun, na ce to ni ba na cikin wannan tsari na ace zaɓaɓɓe ya ajiye kujerarsa saboda wani. Wannan kuskure ne kuma cin zarafin dimokraɗiyya ne." In ji Nafi'u Bala.
Martanin ADC
Malam Faisal Kabir ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ADC,
"Wallahi muna ɗaukar shi a matsayin shiririta kawai tunda ita jam'iyya ai kamar wata cibiyar ilimi ce. Ba za ka wayi gari kawai ka ce kai ne shugaban ƙasar Najeriya ba.
"Sannan abu na biyu, wannan mutumin yana daga cikin mutanen da suka rubuta takardar sauka daga muƙaminsu cewa ya sauka domin bayar da dama a samu haɗakar jama'iyya. Ai ba David Mark ba ne ya naɗa kansa ba. Taron ƙoli aka yi aka zartar. To shi wannan zai je ya ƙalubalanci majalisar ƙoli ne?" In ji Faisal.
Jam'iyyar APC dai ta yi zargin jam'iyya mai mulki ta APC da ƙoƙarin ganin ta raba kan haɗakar.
Tsohon shugaban jam'iyyar ta ADC, Ralph Nwosu ya yi zargin cewa an yi masa tayin ministoci uku domin ya wargaza tafiyar haɗakar tasu amma ya yi watsi da tayin.
Sai dai fadar shugaban ƙasa da ma jam'iyyar APC duka sun musanta zargin Nwosu inda suka ce labarin ƙanzon kurege ne.
Dalilan da ke janyo rikicin cikin jam'iyya
Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna, KASU kuma mai nazarin kimiyyar siyasa ya lissafa dalilai guda uku da ya ce ɗaya daga cikinsu ne ka janyo jan ƙafa daga ƴan hamayya.
- Rashin adalci: A lokuta da dama rashin adalcin da ka iya kunno kai a lokutan rabon muƙamai ko kuma zaɓe yana haddasa rikicin da ka dabaibaye jam'iyya. Misali, a kan samu yanayin da sabbin ƴan siyasar da suka shiga wata jam'iyya sai su fuskanci wariya ko kuma su su nemi yin ƙarfa-ƙarfa waniabun da zai haddasa rikici.
- Burun ƴan siyasa na takara: Akwai yiwuwar cewa son rai da burin da ƴan siyasar suke da shi na tsayawa takara ka iya zama dalilin samun rikicin cikin gida a jam'iyya. Misali Atiku Abubakar da alama yana kan bakarsa na son yin takara. Shi ma Peter Obi ya lashi takobin yin takara. Haka ma Rotimi Amaechi ya bayyana burinsa na takara. Kenan kowane ɓangare ka iya ɗaukar duk matakin da yake ganin masalaha ne a gare shi.
- Hannun jam'iyya mai mulki: Akwai masu hasashen cewa rashin haɗin kan ƴan hamayyar ba zai rasa nasaba da irin rawar da jam'iyyar APC mai mulki za ta iya takawa wajen kunna da kitsa rikice-rikice a tsakanin ƴan hamayyar.
Me ya sa ake zargin APC da rura rikici a ADC?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano ya ce a mafi yawancin lokuta idan ka ji rikicin cikin gida a jam'iyyar hamayya to ba a rasa hannun jam'iyya mai mulki.
"Ganin yadda abubuwa ke faruwa ba za a yi mamaki ba idan an ce jam'iyya mai mulki na da hannu a rikicin. Ko dai ba ita ta ƙirƙira ba, zai iya zama tana da hannu wajen rura rigingimun domin ganin ba su ƙare ba.
Haka ake yi a siyasar Najeriya, inda kowace jam'iyya take ƙoƙarin rushe abokiyar hamayyarta ita kuma ta gina kanta."
Sai dai kuma Farfesa Fagge ya ce dabara ta ragewa jam'iyyun hamayya su gyara gidansu domin ita jam'iyya mai mulki a har kullum tana son ci gaba da mulki ne kuma za ta yi duk iya yinta wajen ganin hakan ya tabbata.
"Abin da yake gabansu shi ne mulki. Kamata ya yi jam'iyyun hamayya su tsara gidansu ta yadda za su ja hankalin masu zaɓe. Ai da ba APC ba ce take mulki, daga baya ne suka yi gyara, suka haɗe da wasu jam'iyyun, sannan suka kayar da PDP. Ita ma haka PDP ta yi a baya."
"Ya kamata su yi la'akari da cewa duk wanda yake kan mulki yana so ya ci gaba, ya rage nasu su san dabarar da za su yi domin ƙwace mulki." In ji Farfesa Fagge.











