Me ya sa wasu manyan muƙarraban Buhari suka shiga haɗakar ADC?

Wasu muƙarraban gwamnatin Buhari

Asalin hoton, Social Media

Bayanan hoto, An ga fuskokin wasu muƙarraban tsohuwar gwamnatin Buhari a sabuwar haɗakar
    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Zargin da wasu ke yi cewa muƙarraban tsohuwar gwamnatin Buhari ba sa jin daɗin gwamnatin Tinubu na ƙara fitowa fili, bayan da aka ga fuskokin wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin kane-kane cikin sabuwar haɗakar ADC.

A ranar Laraba ne wasu jiga-jigan yansiyasar ƙasar daga jam'iyyun hamayya da ma wasu a APC suka sanar da yin haɗaka ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ADC da nufin kawar da gwamnatin APC ta Bola Tinubu.

A watannin da suka gabata ne dai wasu daga cikin tsagin tsohuwar jam'iyyar CPC da Buhari ya jagoranta a baya - da ta narke cikin haɗakar APC a 2014 - suka nuna damuwarsu kan rashin damawa da su a gwamnatin Tinubu.

Kodayake wani tsagin cikin tsohuwar CPCn ya fito ya barranta kansa daga wancan zargi tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu.

To amma da alama wancan zargi ya ƙara fitowa fili bayan da a makonnan haɗakar ƴanhamayya suka ayyana jam'iyyar ADC a matsayin wadda za su taru a cikin domin tunkarar gwamnatin APC a zaɓen 2027.

A iya cewa mafi rinjaye cikin jiga-jigan haɗakar ƴan jam'iyyar APC ne masu biyayya ga tsohon shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari, hasali ma suna daga cikin mutanen da suka riƙe manyan muƙamai a tsohuwar gwamnatin ta Buhari.

Me hakan ke nufi a siyasance?

Masanin kimiyyar siyasa, malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano, Mallam Kabir Sufi ya ce shigar muƙarraban gwamnatin Buhari haɗakar ADC ba abin mamaki ba ne la'akari da abubuwan da suka faru a baya

"Wasu na kallon matakin a matsayin wani abu da ke gaskata zargin cewa wasu daga cikinsu ba su goyi bayan takarar Tinubu a zaɓen 2023 ba."

Ya ce wataƙila "adawar ce ta fito fili a yanzu", shi ya sa suka ɓalle suka fita daga jam'iyyar domin ƙalubalantarsa a zaɓe mai zuwa.

Sai dai kuma masanin siyasar ya ce akwai waɗanda ake ganin ba sa jin daɗin zama a jam'iyyar tun bayan abubuwan da suka faru a lokacin zaɓen fitar da gwani na APC gabanin babban zaɓen 2023.

"Mutane kamar su Rotimi Amaechi da suka yi takara da Tinubu a baya, zama a cikin jam'iyyar ya ƙi yi musu daɗi tun wancan lokacin, saboda haka za su gwammace su fice daga cikinta domin samun wata madafar," in ji Sufi.

Sai dai masanin siyasar ya ce "babu alamun maigidan nasu, Muhammadu Buhari na da irin wannan ra'ayi kasancewar ya sha nanata cewa shi mai biyayya ne ga jam'iyyarsa ta APC."

Wasu gaggan tsohuwar gwamnatin Buharin da ke cikin haɗakar sun haɗa da:

Abubakar Malami

Abubakar Malami

Asalin hoton, Abubakar Malami/Facebook

Bayanan hoto, Tsohon Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnati

Abubakar Malami ya kasance jigo a tsohuwar gwamnatin Buhari, inda har wasu ke cewa yana cikin manyan ƙusashin tsohuwar gwamnatin da ake yi wa laƙabai da ''Cabal''.

Ya riƙe muƙamin ministan shari'a na ƙasar, kuma babban lauyan gwamnati na tsawon lokacin da tsohuwar gwamnatin ta kwashe, wato shekara takwas.

A ranar Laraba ne Malami ya sanar da ficewa daga jam'iyyarsa ta APC tare da shiga sabuwar haɗakar ta ADC, inda kuma ya ce a shirye yake wajen bayar da gudunmowarsa domin tunɓuke gwamnatin Tinubu.

Cikin wata hira da BBC a ranar Larabar, Malami ya ce 'mun fito fili ne domin mu yaƙi jam'iyyar APC, musamman yadda ta bar abubuwa suka taɓarɓare a ƙasar, ciki har da tsaro da tattalin arziki da kuma sauran dangogin wahalhalu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jefa talakawa''.

Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi

Asalin hoton, Rotimi Amaechi

Bayanan hoto, Tsohon ministan sufuri a lokacin gwamnatin Buhari

Amaechi ya kasance ɗaya daga cikin makusantan Buhari, waɗanda tsohon shugaban ƙasar ya fi ji da su a gwamnatinsa.

Ya kasance ministan sufuri a zamanin mulkin Muhammadu Buhari na tsawon shekara takwas daga 2015 zuwa 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya kasance cikin waɗanda suka tsaya wa jam'iyyar APC takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, kuma shi ne ma ya zo na biyu bayan Tinubu.

A wata hira da ya yi da BBC a baya-bayan nan, tsohon ministan ya ce a shirye yake domin shiga duk wata haɗakar da za ta kawar da gwamnatin Tinubu.

Rauf Aregbesola

Rauf Aregbesola

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Tsohon Ministan cikin gida

Aregbesola ya kasance na gaba-gaba a sabuwar tafiyar haɗakar ta ADC, inda ma har aka ba shi muƙamin sakataren sabuwar haɗakar na ƙasa

A shekarar 2019 tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa Aregbosla ministan harkokin cikin, muƙamin da ya riƙe har 2023.

A farkon wannan shekara ne tsohon gwamnan na jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC.

Nasir El Rufai

Tsohon gwamnan Kaduna

Asalin hoton, Nasir El-Rufai/Facebook

Bayanan hoto, El-Rufai ya ce ba shi da ubangidan siyasa da ya wuce Buhari

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna - wanda a yanzu haka ke kan gaba a haɗakar ta ADC - na daga cikin ƴansiyasar da suka jima tare da tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari kuma suke yi masa biyayya.

A watan Maris ne El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga APC, inda a nan ma ya ce sai da ya sanar wa Buhari matakin nasa.

A kakar zaɓen 2023, El-Rufai ya kasance na gaba-gaba wajen goyon bayan Bola Tinubu na APC.

To sai dai bayan lashe zaɓen Tinubu ɓaraka ta kunno kai tsakaninsa da El-Rufai bayan da majalisar dattawa ta ƙi amincewa da tantance shi domin ba shi muƙamin minista a gwamnatin.

Solomon Dalung

Dalung
Bayanan hoto, Tsohon ministan matasa da wasanni

Fitaccen ɗan gwagwarmayar ya faɗa siyasa dumu-dumu ne bayan da tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari na naɗa shi muƙamin ministan matasa da wasanni a 2015.

A baya-bayan nan Dalung ya riƙa nuna adawarsa ga gwamnatin Tinubu, yana mai sukarta da rashin tausaya wa talaka.

Cikin wata hira da BBC a baya-bayan nan, Dalung ya ce a tsawon shekaru biyu na mulkin Tinuba mutanen arewacin Najeriya ba su ga komai ba.

"Ban da yunwa da rashin tsaro babu wani abu da ƴan arewacin Najeriya za su iya bugun ƙirji su ce sun samu a ƙarƙashin gwamnatin nan." In ji tsohon ministan.

Air Vice Marshal A Sadiq (mai ritaya)

Toshon babban hafsan sojin sama

Asalin hoton, Media Team

Bayanan hoto, A A Sadiq ne babban hafsan sojin saman Najeriya lokacin mulkin Buhari

Tsohon babban hafsan sojin sama na ƙasar na daga cikin mutanen da suka ayyana haɗuwa a ƙawancen ADC.

A shekarar 2015 tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa Air Vice Marshal Abubakar Sadiq mai ritaya, matsayin babban hafsan sojin sama na ƙasar, muƙamin da ya riƙe na tsawon shekara shida.

Bayan saukarsa daga muƙamin a 2021 ya faɗa harkokin siyasa inda ya tsaya takarar gwamnan jihar Bauchi ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, kodayake bai yi nasara ba.

Abubakar Bawa Bwari

Abubakar Bawa Bwari

Asalin hoton, Abubakar Bawa Bwari

Bayanan hoto, Tsohon ministan tama da ƙarafa

Tsohon ministan tama da ƙarafa a lokacin gwamnatin Buhari na daga cikin waɗanda suka shiga hadakar ta ADC.

Dan asalin jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya ya shafe shekaru yana riƙe da minista a lokacin gwamnatin Buhari.

Mohammad Hassan Abdullahi

..

Asalin hoton, Mohammad Abdullahi

Bayanan hoto, Tsohon Ministan Muhalli

Muhammad Abdullahi ya kasance minista a gwamnatin Buhari da ta gabata.

Ɗansiyasar ɗan asalin jihar Nasarawa da ke yankin arewa ta tsakiyar ƙasar ya riƙe muƙamin minista a ma’aikatun ƙasar.

Da fari ya kasance ƙaramin ministan kimiyya da fasaha daga 2019 zuwa 2022, kafin daga baya ya zama ministan muhalli daga 2022 zuwa 2023.

Lauretta Onochie

Lauretta Onochie

Asalin hoton, Lauretta Onochie/X

Bayanan hoto, Tsohuwar hadimar Buhari

Tsohuwar babbar mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari kan shafukan sada zumunta na daga cikin wadanda suka ƙulla ƙawancen ADC.

A taron haɗakar da aka yi ranar Laraba an ga ƴarsiyasar tare da manyan jiga-jigan da ke cikin haɗakar.

Martanin APC

APC

Asalin hoton, APC

Ita dai jam'iyyar APC ta sha cewa muƙarraban Buharin da ke sukarta suna ne kawai saboda ba su samu muƙamai a gwamnatin Tinubu ba.

Haka kuma jam'iyyar ta ce sabuwar haɗakar ƴanhamayyar ba ta razana su ko kaɗan.

Cikin wata hira da BBC sabon shugaban riƙo na jam'iyyar, Ali Bukar Dalori ya ce ko kaɗan yunƙurin haɗewar jam'iyyun adawa ba ya tayar wa APC hankali.