KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/03/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Iran ta naɗa Alireza Arafi jagoran addinin ƙasar na riƙo

    sabon jagoran addinin Iran

    Asalin hoton, intanet

    Hukumomin Iran sun sanar da naɗin, Ayatollah Alireza Arafi matsayin jagoran addinin ƙasar na riƙo, kafin a zaɓi sabo.

    Majalisar manyan malaman ƙasar mai mambobi 88 ce za ta za bi sabon jagoran addinin.

    Al'ummar kasar ne dai ke zabar mambobin majalisar bayan kowace shekara takwas.

    A ƙarƙashoin dokokin Iran, waɗannan manyan malaman ne ke da alhakin zaɓen sabon jagoran addini da zarar wanda yake kan muƙamin ya kau, to sai dai ana ganin hakan zai yi wahala kasancewar babu kwanciyar hankali a ƙasar da ke cikin yanayi na yaƙi.

  2. An kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Pakistan

    Hoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum takwas ne suka mutu a zanga-zangar goyon bayan Iran da aka gudanar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da birnin Karachi na kasar Pakistan.

    kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa na yankin, Muhammad Amin ya shaida wa kamfanin dilalncin labarai na AFP cewa mutum 20 ne suka jikkata yayin zanga-zangar.

    Wasu rahotonni sun bayyana cewa jami'an tsaron Amurka da ke harabar ofishin jakadncin ne suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar, sannan daga baya ƴansandan Pakistan suka harba yahaƙi mai sa hawaye.

    A cewar AFP wasu fusatattun matasa ne suka haura katangar domin shiga harabar ofishin jakadancin ya yi da wasu suka karya tagogin ginin.

    Bidiyoyin da aka yaɗa sun nuna yadda matasan suka riƙa karya tagogin.

    Dubban mutane suka fantsama kan titunan Lahore da Skerdi, domin guidanar da zanga-zangar, yayin da ake sa ran yin zanga-zangar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da Islamabad, babban birnin ƙasar.

  3. Hotunan ɓarnar da hare-haren Iran suka yi kan sansanonin sojin Amurka

    Hotuna na ci gaba da bayyana na yadda baƙin hayaƙi ke tashi bayan harin ramuwar gayyar Iran kan sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

    An ɗauki wasu daga cikin hotunan cikin dare, wasu kuma da safe a ƙasashen Bahrain da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa.

    hoto

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An ga baƙin yahaƙi a birnin Doha na Qatar bayan harin Iran
    Hoto

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Harin jirgin Iran maras matuƙi ya shafi wani gini tare da ƙona shi a Manama, babban birnin Bahrain.
  4. Harin Iran ya lalata wani gini a birnin Tel Aviv na Isra'ila

    Wani gida da Iran ta ruguza a Tel Aviv

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Harin makami mai linzamin Iran ya lalata wani gida a tsakiyar Tel Aviv, babban birnin Isra'ila.

    Rahotonni daga ƙasar sun ce harin ya yi sanadin mutuwa mace guda, wadda ita ce mutuwa da farko da aka bayar da rahotonta a Isra'ila tun bayan fara wannan yaƙi.

    Isra'ila ta kakkaɓo kusan duka makaman linzami da Iran ta harba cikinta.

    Amma duk da haka wasu sun samu faɗawa ciki, musamman bayan tarwatsewa a sama.

  5. Iraƙi ta ayyana makokin kwana uku bayan kisan Khamenei

    Gwamnatin ƙasar Iraƙi ta ayyana makokin kwana uku a fadin ƙasar domin nuna alhini kan kisan jagoran addainin Iran Ayatollah Ali Khamenei.

    Cikin wata sanarwar da gwamnatin ƙasar ta fitar, ta aike da saƙon jaje ga al'ummar Iran, kan kisan jagoran addinin ƙasar, wadda ta bayyana da ''aikin takalar faɗa''.

  6. Dubban Iraniyawa na jimamin mutuwar jagoran addinin ƙasar

    mutane

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban Iraniya sun taru a birnin Tehran domin yin alhinin mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei da Amurka da Isra'ila suka kashe a hare-harensu.

    wasu mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Tuni dai hukumomin ƙasar suka sanar da makokin kwanaki 40 a faɗin ƙasar

    wasu mata

    Asalin hoton, Getty Images

    Ayatollah Ali Khamenei na da farin jini da ƙarfin faɗa a ji a ƙasar Iran

    Hoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Ya shafe fiye da shekara 35 yana jan ragamar ƙasar, mai ƙarfin faɗa a ji a yankin Gabas ta Tsakiya.

  7. 'Jiragen Iran sun yi ruwan boma-bomai kan sansanonin sojin Amurka'

    gini ya kama da wuta

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA ya ce jiragen yaƙin ƙasar sun yi ruwan boma-bomai kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gulf da yankin Kurdistan na Iraƙi.

    Dakarun sojin Iran sun ce jiragen yaƙin ƙasar sun samu nasarar kai munanan hare-hare kan sansanonin.

    Sojojin sun ƙara da cewa ''duka sansanonin maƙiya'' a yankin ba su gagari jiragen yaƙin mu ba.