Ƴan hamayya sun amince da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka

Peter Obi, Rauf Aregbesola, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i

Asalin hoton, X/Multiple

Bayanan hoto, Nasir El-Rufa'i, Atiku Abubakar, Rauf Aregbesola, Peter Obi
Lokacin karatu: Minti 4

Gamayyar wasu jiga-jigan ƴansiyasa a Najeriya da ke hamayya da gwamnatin jam'iyyar APC sun amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama'iyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.

Ƴansiyasar sun ce sun amince da ADC ne da nufin haɗa ƙarfi da ƙarfe a cikinta da nufin kawar da jam'iyyar APC daga mulkin Najeriya a zaɓen 2027.

An cimma ƙawancen ne a taron haɗakar da aka gudanar ranar Laraba a babban ɗakin taro na Ƴar'adua Centre da ke birnin Abuja.

Tuni dai haɗakar ƙawancen ta zaɓi wasu ƙusoshin tafiyar sabon ƙawancen domin su jagoranci sabuwar tafiyar.

Sabuwar haɗakar ta ADC ta zaɓi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar, wadda suka amince da ita a matsayin jam'iyyar haɗaka.

David Mark

Asalin hoton, David Mark

Bayanan hoto, David Mark

Tun a ranar Talata ne dai haɗakar ta bayyana tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

A wajen taron na ranar Laraba an samu halartar manyan ƴan adawa da suka haɗa da Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufa'i da sauran su.

Tun farko taron nasu ya ci karo da matsala bayan an hana su amfani da wurin da aka shirya domin gudanar da taron, sai dai daga baya an gudanar da taron a cibiyar Musa Ƴar'aduwa da ke tsakiyar birnin.

Ana kuma sa ran gamayyar 'yansiyasar za su bayyana yadda za a kasafta tsarin jagorancin jam'iyyar.

Ɗantakarar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, da na Labour Party, Peter Obi, na cikin jiga-jigan adawar da suka shafe yinin Talata suna tattaunawa, inda kowane ɓangare ya gana da abokan tafiyarsa.

ADC

Asalin hoton, Aregbesola Facebook/El Rufai X

Sauran sun ƙunshi tsohon gwamnan Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi na APC, da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

'Yan jam'iyya PDP

Asalin hoton, Facebook/Atiku Abubakar

Bayanan hoto, Wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP kenan lokacin ganawarsu kafin taron jam'iyyar haɗaka ta ADC a Abuja ranar Talata

"An tattauna ne kan abubuwan da ake ganin za su zama ginshiƙi na sauran tafiyar da za a yi," a cewar Ibrahim Usaini Abdulkarim, wani na hannun daman Peter Obi kuma wanda ya halarci taron da aka gudanar a ranar Talata.

Ibrahim ya faɗa wa BBC cewa sun rarraba muƙamai na riƙon jam'iyyar a tsakaninsu kafin babban taro na ƙasa a nan gaba.

Gwamnan Kaduna El-Rufai ya tabbatar cewa haɗakar ta ADC ta zaɓi Aregbesola a matsayin sakatarenta na ƙasa na riƙo, har ma ya wallafa jawabin karɓar muƙamin da ya yi a shafukan sada zumunta.

Matakin 'yan adawar na shiga ADC na zuwa ne bayan sun kasa cimma buƙatarsu ta yi wa sabuwar ƙungiya mai suna All Democratic Alliance' (ADA) rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.

A tasu ganawar, Atiku Abubakar da wasu manyan jam'iyar PDP sun nemi 'yan jam'iyyar su haɗa hannu da su wajen shiga haɗakar ta ADC domin ƙalubalantar gwamnarin ta Bola Tinubu.

Haɗakar 'yan hamaya ba ta hana mu barci - APC

Ali Bukar Dalori

Asalin hoton, X/APC

Bayanan hoto, Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban APC na riƙo
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar Litinin ne sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki na riƙo, Ali Bukar Dalori, ya fara aiki bayan saukra Abdullahi Ganduje.

Yayin wata hira da BBC, Dalori ya ce wannan haɗaka da 'yan adawa ke yi abin murna ne ma a wajensu.

"Ba maganar hana barci ma, mu muna jin daɗi ne saboda muna so mu nuna wa duniya cewa muna tare da jama'armu kuma ba su da wani tasirin da za su kai kayansu kasuwa domin wani ya saya," in ji shi.

Dalori, wanda kafin hawansa kujerar, shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar na arewacin ƙasar, ya ce zai yi "ƙoƙarin haɗa kan ƴaƴan jam'iyyar da kuma yi wa kowa adalci ba tare da nuna wani fifiko ba".

APC ta kama mulkin Najeriya ne bayan samun nasarar doke PDP a zaɓen 2015, inda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa'adi biyu na shekara takwas, kafin Bola Tinubu ya gaje shi a 2023.

Ita ma APC ta kafu ne sanadiyyar haɗaka tsaakanin jam'iyyun CPC, da ACN, da NNPP, da wani ɓangare na jam'iyyar APGA kafin shiga zaɓen na 2015.