Matakai biyar da za su iya sauya siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027

Asalin hoton, APC
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 7
Duk da cewa kowa ya yarda akwai sauran lokaci kafin babban zaɓen Najeriya na 2027, amma kowa ya shaida yadda 'yansiyasar ƙasar ke shiri tun daga yanzu.
A makon da ya gabata ne kwatsam shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Abdullahi Ganduje, ya ajiye mulki a wani abu da masana ke cewa na da alaka da lisaafin da manyan ‘yansiyasar ke yi gabanin zaben 2027.
Haka nan, abubuwa da yawa na ta faruwa a lokaci guda, kamar sauya shekar ‘yansiyasa daga wata jam’iyya zuwa wata, da batun hadakar ‘yan'adawa, da kuma yadda wasu suka yi lamɓo suna kallon yadda abubuwa ke sauyawa kafin su yanke hukuncin inda za su kama.
Masana harkokin siyasa na ganin komai zai iya faruwa daga yanzu zuwa lokacin zaben shugaban kasa na 2027, kuma ya yi wuri a yanke hukunci kan abin da zai faru.
Mun duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da za su iya sauya lissafin siyasar ƙasar gabanin babban zaɓen na gaba.
Makomar Kashim Shettima

Asalin hoton, APC
Batun tazarcen Shugaba Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin abokin takara ya fara jefa jam'iyyar APC cikin ruɗani a watan Yuni.
Hatsaniya ta ɓarke yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiyyar arewa maso gabas - inda Shettima ya fito - wanda aka yi a jihar Gombe.
An samu ruɗani a taron ne bayan shugabannin APC na yankin sun ambaci sunan Shugaba Tinubu shi kaɗai a matsayin wanda zai yi wa APC takara a zaɓen 2027 ba tare da ambatar mataimakinsa Kashim Shettima ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matakin ya haifar da yamutsi a zauren taron, lamarin da ya sa har ta kai ga ba wa hammata iska, inda wasu suka yi wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje barazana kafin jami'an tsaro su fitar da shi daga wurin.
"Irin abin da ya faru a taron masu ruwa da tsaki na APC a shiyyar arewa maso gabas, manuniya ce ga jam'iyyar APC cewa duk wani yunƙuri na sauya Kashim Shettima na iya jefa jam'iyyar cikin matsala a yankin," in ji Farfesa Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja.
Shi kuwa Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero na ganin ajiye Kashim Shettima zai yi wa APC mummunan tasiri a zaɓen 2027.
“A gaskiyar magana idan har ba a ci gaba da wannan tafiya da Mataimakin Shugaban Najeriya [Kashim Shettima] ba shakka babu APC za ta iya rasa yankin arewa maso gabas, musamman da ake ƙishin-ƙishin ɗin cewa Tinubu zai ɗauko wanda ba Musulmi ba a matsayin mataimaki,” in ji shi.
"Idan har ya yi abin da ake zargi to Musulmai za su ga cewa ya ajiye nasu, idan ba a yi aune ba sai jam'iyyar APC ta rasa yankuna da dama a Najeriya."
Fadar shugaban Najeriya ta ce Tinubu zai zaɓi abokin takara bayan ya karɓi tikitin takarar a hukumance yayin taron jam'iyyar da za a yi nan gaba, amma ba ta ce komai ba game da batun ajiye Shettima.
Ana sa ran za a yi taron a watan Disamba mai zuwa.
Wanda zai zama shugaban APC na kasa

Asalin hoton, APC
A ranar Juma'a da ta gabata ne shugaban jam'iyyar APC mai mulki na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka daga muƙamin nasa bayan shafe shekara biyu.
APC ta ce shugaban ƙasa ya umarci Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaba na riƙo kafin kwamatin zaɓaɓɓu su gana game da batun.
Jami'in yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa babban dalilin da Ganduje ya bayar game da murabus ɗin nasa shi ne batun lafiya.
Sai dai wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ta umarce shi da yin hakan.
Da ma tun lokacin da aka bai wa Ganduje shugabancin jam'iyyar wasu 'yan jam'iyyar, musamman daga yankin arewa maso tsakiya, suka dinga gunaguni cewa su ya kamata a bai wa.
Zuwa yanzu babu tabbas game da wanda fadar shugaban ke son ya karɓi shugabancin jam'iyyar, amma ko ma wane ne ɓangaren da ya fito da kuma kimarsa a siyasance za su yi tasiri game da ko APC za ta ci gaba da jagorancin Najeriya ko kuma a'a a 2027.
Rikicin siyasar jihar Rivers

Asalin hoton, Nigeria Presidency
A makon da ya gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci sulhu tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamnan Rivers Siminalyi Fubara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Tsohon gwamnan Rivers Wike da kuma Fubara mai-ci - amma wanda aka dakatar bayan saka dokar ta-ɓaci a jihar - sun daɗe suna rigimar nuna iko a jam'iyyarsu ta adawa PDP tun bayan zaɓen 2023, rikicin da Shugaba Tinubu ya yi amfani da shi wajen kafa dokar ta-ɓacin.
Bayan ganawa da shugaban ƙasar, jagororin siyasar biyu sun yi jawabai masu nuna alamun cewa a shirye suke su mayar da wuƙaƙensu cikin kube kuma su yi aiki da juna.
"Mun amince mu yi aiki tare. Yanzu komai ya wuce. Da ma asali mun fito ne daga gidan siyasa ɗaya, kuma a matsayinmu na ƴan'adam muna samun saɓani kuma a yi sulhu. Yanzu komai ya wuce, babu wani saɓani," a cewra Wike.
Abin da har yanzu masu bibiyar al'amuran siyasa ba su tabbar ba shi ne abin da sulhun ke nufi.
Ta yaya za su yi aiki tare da juna? Fubara zai bar PDP zuwa APC ne, ko kuma zai haɗa kai da Tinubu su yaƙi PDP kamar yadda Wike ke yi a yanzu?
Rikicin PDP

Asalin hoton, PDP
PDP ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya kuma kusan shekara uku kenan tana cikin rikici na cikin gida, wanda har yanzu babu alamun ƙarshensa.
A makon da ya gabata ma rikicin ya sauya salo bayan shugabanta Ilya Damagun ya sanar da mayar da sakatarenta na ƙasa Samuel Anyanwu kan muƙaminsa bayan shari'o'in da aka tafka sakamakon dakatar da shi.
Matakin nasa ya jawo zanga-zangar rashin amincewa daga wasu mambobin kwamatin gudanarwa na jam'iyyar, inda jam'iyyar ta tabbatar cewa har yanzu Setonji Koshoedo ne ke riƙe da muƙamin a matakin riƙo.
Rikicin na PDP ya samo asali ne tun daga zaɓen fitar da gwani na takarar zaɓen shugaban ƙasa a 2023, inda Nyesom Wike ya ja daga da Atiku Abubakar wanda ya yi nasarar samun tikitin. Daga baya Wike ya siga gwamnatin APC kuma ya ci gaba da nuna adawa da sauran shugabancin jam'iyyar a dukkan matakai.
Masana da dama na ganin rikicin zai iya jawo wa PDP gagarumin koma-baya a nan gaba idan ba a shawo kansa ba.
Idan hakan ta faru, tasirin da rikicin zai yi shi ne: ko dai wata jam'iyyar daban ta maye gurbin PDP a matsayin babbar mai adawa, ko kuma APC mai mulki ta samu tazarce kai-tsaye ba tare da wani ƙalubale ba.
Jam'iyyar haɗaka ta 'yan'adawa

Asalin hoton, Social Media
A 'yan makonnin da suka gabata ne wasu jiga-jigan 'yanhamayya a Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) suka tabbatar da wata haɗaka mai ƙarfi da nufin kawar da gwamnatin Bola Tnubu ta jam'iyyar APC.
Tun a farkon shekarar nan ne ƴan'adawar suka fara tunanin kafa haɗaka domin cimma wannan ƙudiri nasu, inda a yanzu suke neman hukumar zaɓe Inec ta yi wa ƙungiyar All Democratic Alliance' (ADA) rajista a matsayin sabuwar jam'iyar siyasa.
A rana 19 ga watan Yuni ne shugaban ADA na ƙasa Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo suka aika wa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wasiƙar neman kafa jam'iyar.
Ƙawancen haɗakar na ƙunshe da jiga-jigan hamayya a fagen siyasar Najeriya, waɗanda suka fito daga ɓangarori daban-daban da kuma mabambantan addinai da ƙabilu.
Ko haɗakar tasu za ta iya maye gurbin PDP a matsayin babbar jam'iyyar da za ta ƙalubalanci APC a zaɓen na 2027? Lokaci ne kawai zai ba da tabbaci.
Wani abu da masu kaɗa ƙuri'a za su ƙagu su gani shi ne mutanen da jam'iyyun adawar za su tsayar a matsayin 'yantakara a zaɓen da za a yi nan da shekara biyu masu zuwa.










