Mene ne amfani da illar jam'iyyu da yawa a siyasar Najeriya?

Asalin hoton, INEC
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
A makon nan ne hukumar zaɓen Najeriya INEC ta sanar da samun buƙatu daga ƙungiyoyi fiye da 100 domin yi musu rajistar zama jam'iyyun siyasa.
Shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Mahmod Yakubu ya ce ya zuwa farkon makon nan hukumar ta samu wasiƙu daga ƙungiyoyi 110 da ke neman rajistar hukumar domin zama jam'iyyun siyasa a ƙasar.
A yanzu haka dai akwai jam'iyyun siyasa 19 a Najeriya, kuma idan har duka waɗannan ƙungiyoyi suka cimma ƙa'idojin rajista da INEC ta shimafa, adadin jam'iyyun siyasa a Najeriya ka iya kai wa kusan 130.
Wannan batu ya janyo suka daga wasu yan ƙasar da ke ganin hakan a matsayin wani abu da zai raba kan ƴan hamayya tare da rage ƙarfinsu.
A gefe guda kuma akwai masu ganin matakin a matsayin alamar bunƙasar dimokradiyyar ƙasar.
Mece ce Jam'iyyar siyasa?

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Abubakar Kari na Jami'ar Abuja, ya ce jam'iyyar siyasa na nufin wata ƙungiya ta gungun wasu mutane masu ra'ayi da aƙida iri guda.
Akan kafa jam'iyyun siyasa ne domin a nemi muƙamai don samun iko, kamar yadda ya yi ƙarin haske
Ya ƙara da cewa jam'iyyar siyasa wata alama ce da ƴan siyasa ke tsayawa takara ƙarƙashin inuwarta.
''Kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi cewa duk wanda zai tsaya takara dole ya tsaya ƙarƙashin inuwa wata jam'iyya'', in ji Farfesa Kari.
Mene ne amfanin jam'iyyu da yawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Kari ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da amfani da tsarin jam'iyyun siyasa masu yawa da a turance ake kira ''Multi-Party System''.
Shi ma Mallam Kabiru Sa'id Sufi, malami a Kwalejin Shere Fagen Shiga Jami'a da Kano, kuma mai shairhi kan al'amuran siyasa ya ce tsarin ''Multi-Party System da Najeriya ke bi ne ya bayar da damar hakan.
Farfesa Kari ya ce tsarin na da alfanu ta fuskar dimokraɗiyya:
Damar sauya gwamnati: Mallam Kabiru Sa'id Sufi ya ce ɗaya daga cikin amfanin jam'iyya masu yawa shi ne samun damar sauya gwamnati cikin sauƙi.
''Koda jam'iyya guda ba za ta iya ba, idan aka yi haɗaka tsakanin jam'iyyun hamayya masu yawa, hakan zai sa a sauya gwamnati cikin ruwan sanyi'', in ji shi.
A tarihin siyasar Najeriya an ga lokuta da dama da jam'iyyun hamayya suka ƙulla ƙawance suka kuma samu nasarar kafa gwamnati.
Damar bayyana ra'ayi: Farfesa Kari ya ce samun jam'iyyu da yawa zai taimaka wajen bai wa masu ra'ayi iri ɗaya damar haɗuwa a ƙarƙashin inuwa guda domin cimma burinsu.
''Masu ra'ayi guda za su iya taruwa cikin jam'iyya guda domin cimma muradunsu ba tare da haɗuwa da wasu masu ra'ayi daban da nasu ba'', in ji shi.
Damar tsayawa takara: Yawan jam'iyyu na bai da ƴan siyasa damar tsayawa takara ko bayyana ra'ayinsu a siyansance, kamar yadda Farfesa Kari ya bayyana.
''Idan jamiyyun suna da yawa ba za a samu matsi ko hana wani ɗan takarar damar tsayawa takara ba'', a cewa malamin jami'ar.
Ƙarfafa hamayya: Haka kuma samun jam'iyyu da yawa wata alama ce ta ƙarfin hamayya a cikin ƙasa.
''Alama ce ta ƙarfafar dimokraɗiyya har ma a samu mutane sun shagala da kafa jam'iyyun siyasa da kuma amincewa da bambancin ra'ayin da ke tsakani'', in ji Kabiru Sa'id Sufi.
Ilimantar da masu zaɓe: Jam'iyyun siyasa kan ilimantar da ƴan ƙasa kan abubuwan da suka shafi ƴancinsu da sanin manufofin kowace jam'iyya.
''Idan zaɓe ya zo jam'iyyun kan shagala wajen neman goyon bayan masu zaɓe, to a wannan yanayi za su yi ƙoƙarin ilimantar da mutane abin da ya shafi siyasa da gwamnati, a ƙoƙarin fito da gazawar wasu jam'iyyun'', in ji Kabiru Sufi.
Mene ne Illar samun jam'iyyu da yawa?

Kassara hamayya: Yawan jam'iyun siyasa na kassara manyan jam'iyyun hamayya a cikin ƙasa a cewar Farfesa Kari.
''A lokacin da a aka yi zaɓen 2023 a Najeriya, manyan jam'iyyun hamayya na PDP da LP sun ce ba za su amince da sakamakon zaɓen ba, amma sai aka samu wasu ƙananan jam'iyyun hamayya suka yi taron manema labarai nan take suka nuna amincewarsu da sakamakon'.
Mallam Kabiru Sufi ya ce galibi wasu jam'iyyun ma ana kafa su ne da wata manufa, ba aininin manufar da suka bayyana a lokacin yi musu rajista ba.
Rarrubuwar kan ƴan hamayya: Wata matsala da yawan jam'iyyu ke haifarwa a Najeriya shi raba kan ƴan hamayya, wanda kuma hakan na taimaka wa jam'iyya mai mulki.
''Idan kan jam'iyyun hamayya ya rabu, ƙuri'unsu za su karkasu, ta yadda cikin sauƙi jam'iyya mai mulki za ta samu nasarar cin zaɓe''.
''A wasu lokutan ma akwai zargin da ake yi cewa jam'iyya mai mulki ce ke ɗaukar nauyin wasu jam'iyyun da nufin kassara jam'iyyun hamayya'', in ji farfesa Kari.
Rikita masu zaɓe: Masanin kimiyyar siyasar ya ce wata babbar matsala da yawan jam'iyyun siyasa ke haifar wa ita ce rikita masu zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri'a.
''A baya an taɓa yin lokacin da aka samu jam'iyyu masu yawa, masu zaɓe da dama sun riƙa shan wahala kafin su gano alamomin jam'iyyunsu'', in ji shi.
Najeriya dai na da yawan masu zaɓe da ba su iya karatan sunayen jam'iyyunsu ba, sai dai su gane su ta hanyar alamomi, kuma yawan jam'iyyun zai iya rikita su, su kasa gane alamomin jam'iyyunsu.
Yawan kashe kuɗaɗe: Yawan jam'iyyun siyasa na janyo wa hukumar INEC kashe kuɗaɗe masu yawa wajen kula da jam'iyyun a lokacin zaɓuka.
''Kundin tsarin mulki ya ɗora wa hukumar INEC sanya idanu kan jam'iyyun siyasa, lokacin zaɓen shugabanninsu da zaɓukan fitar da gwani da kuma lokacin babban zaɓe, kuma duka wannan yana buƙatar kuɗi'', in ji Farfesa Kari.
Tara jam'iyyu marasa amfani: Maƙasudin kafa jam'iyya shi ne domin ƴan siyasa su tsaya takara cikinsu, domin samun muƙamai, kamar yadda Masanin Kimiyyar siyasar ya bayyana.
''To amma galibi wasu jam'iyyun Inna rududu ne, ba su da wani amfani, za ka samu wata jam'iyyar ko kansila ba ta da shi, amma tana kiran kanta jam'iyya, wanda wannan ɓata wa kanta lokaci ne, saboda ba ta cimma muradin kafa ta ba''.
Me ya fi dacewa da Najeriya?

Asalin hoton, @OpeyemiAkinyod2
Farfesa Abubakar Kari ya ce tsarin da ya fi dacewa da siyasar Najeriya shi ne samun jam'iyyu da dama, amma kada su wuce kima.
''A ƙasa irin Najeriya yana da kyau a yi jam'iyyu da dama, amma kuma yana da kyau a samar da dokoki masu tsauri ta yadda ba za su yi yawa ba su zama Inna ruddudu''. in ji shi.
Kabiru Sa'idu Sufi ya ce tsarin jam'iyyun da dama shi ya fi dacewa da Najeriya, domin gudun danne wa wasu ƴanƙasar dama.
''Rashin bayar da damar kan sa wasu su riƙa yi wa dimokraɗiyyar zagon ƙasa... amma dai yana da kyau a kula kada jam'iyyun su yi yawan da za su zama matsala'', in ji shi.
Me dokar INEC ta ce kan wanzuwar jam'iyyu?

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar INEC ta shimfiɗa wasu ƙa'idoji da duk wata jam'iyyar da ta yi wa rajista, kuma ta kasa cikawa to za ta soke rajistarta.
Kakakin hukumar Hajiya Zainab Aminu ta ce ''Akwai ƙa'idoji masu yawa da hukumar INEC ta shimfiɗa, daga ciki akwai tanadin cewa duk jam'iyyar da ta kasa cin ko da kujerar majalisar tarayya ko ta jiha, to za a soke rajistarta'', in ji ta.
Ta ƙara da cewa ''duk jam'iyyar da ta gaza cin ko da jiha guda a zaɓen shugaban ƙasa, kuma ta gaza cin ko da ƙaramar hukuma guda a zaɓen gwamna ta kuma gaza cin ko da kujerar kansila a zaɓen ƙaramar hukuma, to ita ma za a soke mata rajista''.










