Jerin ƙungiyoyin da ke son zama jam'iyyu a Najeriya da sharuɗɗan da za su cika

Asalin hoton, INEC/X
Batun rajistar sabbin jam'iyyu ya sake tasowa a Najeriya tun bayan da gamayyar wasu ƴan adawa suka fara zargin hukumar zaɓen ƙasar da gaza yi wa ƙungiyarsu ta ADA rajista domin zama jam'iyya.
Lamarin ya tayar da ƙura, inda suka zargi hukumar ta INEC da ƙoƙarin yi musu 'zagon ƙasa' ta hanyar ƙin yi musu rajista da wuri.
Su dai ƴan adawar a baya-bayan nan na ta yunƙuri ne na samar da wata haɗaka da za su yi amfani da ita wajen ƙalubalantar shugaban ƙasar mai ci, Bola Tinubu.
To sai dai hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya, ta ce duk da ta karɓi sunayen ƙungiyoyi sama da 100 da suka nemi a yi musu rajistar, wajibi ne sau sun cika wasu ƙa'idoji kamar yadda doka ta tanada.
Matakan neman rajistar sabuwar jam'iyya
Wajibi ne duk wata ƙungiya da ke son zama jam'iyya ta nuna buƙatar yin hakan ta hanyar cika takardar buƙata ta hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya.
Takardar neman rajistar ita ce ake kira FORM PAI, kuma dole ne jam'iyya ta haɗa takardar da ta cike da takardu da suka ƙunshi bayanai kamar haka:
- Sunan jam'iyyar da ake so a kafa
- Suna da sa hannu da kuma aderishin shugaba da sakataren ƙungiyar da ake so ta zama jam'iyya
- Shaidar biyan kuɗin rajista naira miliyan ɗaya a asusun ajiyar hukumar na banki
- Kwafe 50 na kundin dokokin da kuma kwafe 50 na manufofin jam'iyyar da ake so a kafa.
Sharuɗɗan da dole a cika domin samun rajista
Babu wata ƙungiya da za a yi wa rajistar zama jam'iyya a Najeriya har sai ta cika ƙa'doji kamar haka, waɗanda za a miƙa wa hukumar zaɓen Najeriya ta Inec:
- Suna da adireshin gidaje, da jihohin asali na shugabannin ƙungiya na ƙasa da na jiha da kuma taron da aka yi na zaɓen shugabannin.
- Bayanin taron shugabannin ƙungiyar na ƙasa, ƙunshe da yadda suka amince da amince da suna, da manufofi da kuma tambarin jam'iyyar da suke son kafawa.
- Cikakke da kuma taƙaitaccen sunan jam'iyya wanda: dole ne ya sha bamban da na duk wata jam'iyya da ake da ita ta yadda ba zai haifar da ruɗani ko tababa ga masu zaɓe ba; kada sunan ya zama yana da alaƙa da wata ƙabila, ko addini ko sana'a ko ɓangare; kada alamar jam'iyyar ya nuna cewa ta keɓanta da wani yanki ne kaɗai na Najeriya.
- Jerin sunayen mambobin da ke nuna cewa kowane mutum daga kowane yanki na Najeriya zai iya shigar ta.
- Kwafe na dokoki na manufofin ƙungiyar wanda dole su ƙunshi: Sunan ƙungiyar da tambari da tuta da take da muradu da kuma bayani kan abinda ya bambanta ta da saura da kuma bayani kan tambarin jam'iyyar.
- Bayanin asusun ajiyar kuɗi a banki inda za riƙa tura duk wani kuɗin shiga da ƙungiyar ta samu da kuma za saka wanda za ta samu a gaba da kuma yadda za ta riƙa kashe kuɗaɗenta.
- Adireshin babban ofishin ƙungiyar a Abuja da kuma adersihin sauran ofisoshinta da sunayen ma'aikatanta da kayan amfani da kayan ofis a aƙalla jihohi 24 na Najeriya.
Wata jami'ar hukumar ta INEC da BBC ta tattauna da ita, Zainab Aminu ta ce yanzu haka hukumarsu ta soma nazari da tantace ƙungiyoyi da dama domin tabbatar da cewa sun cika ka'ida da dokokin zama Jam'iyya.
Ta ce," Yana da kyau idan aka yi wa kungiya rajista har ta zama jam'iyya to ta tabbatar jam'iyyar ta yi kokari ta bunkasa har ta kai ta ga samun mukamai a zabukan da za ayi."
Yanzu haka dai hukumar zaɓen ta Inec, ta samu buƙata daga ƙungiyoyi sama da 100 waɗanda ke son a yi musu rajistar zama jam'iyyun siyasa, kamar yadda shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana a ranar Laraba.
Jerin ƙungiyoyin da ke son zama jam'iyyun siyasa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
1. Key of Freedom Party (KFP)
2. Absolute Congress (ABC)
3. All Grassroots Party (AGP)
4. Congress Action Party (CAP)
5. United Social Democrats (USDP)
6. National Action Congress Party (NACP)
7. Great Alliance Party (GAP)
8. New Nigeria Congress (NNC)
9. United Peoples Victory Party (UPVP)
10. Allied Conservative Congress (ACC)
11. Peoples Freedom Party (PFP)
12. All Nigerians' Party (AND)
13. Abundant Social Party (ASP)
14. Citizens Party of Nigeria (CPN)
15. National Freedom Party (NFP)
16. Patriots Party (PP)
17. Movement of the People (MOP)
18. Peoples National Congress (PNC)
19. African Union Congress (AUC)
20. Alliance of Patriots (AOP)
21. Socialist Equality Party (SEP)
22. About Nigeria Party (ABNP)
23. African Reformation Party (ARP)
24. Accelerated African Development Association (AADA)
25. Obidient Peoples Party (OPP)
26. Zonal Rescue Movement (ZRM)
27. Zuma Reform (ZR)
28. Party for Socialist Transformation (PST)
29. Liberation People's Party (LPP)
30. Progressive Obedients Party (POP)
31. Great Nigeria Party (GNP)
32. National Youth Alliance (NYA)
33. National Reform Party (NRP)
34. Patriotic Congress Party (PCP)
35. Community Alliance Party (CAP)
36. Grassroot Alliance Party (GAP)
37. Advance Nigeria Congress (ANC)
38. All Nigerians Alliance (ANA)
39. Team New Nigeria (TNN)
40. All Labour's Party (ALP)
41. New Green Generation Coalition Party (NGOCP)
42. New Green Congress (NGC)
43. New Green Coalition Party (NGCP)
44. About All (Nigerian)
45. Nigerian Liberty Movement
46. National Democratic Party
47. Citizen United Congress
48. All Gender Party
49. Polling Unit Ambassadors of Nigeria
50. Village Intelligence Party
51. Great Transformation Party
52. Alliance Social Party
53. Nigeria Democratic Alliance
54. New National Democratic Party
55. Obedients Peoples Party (Not Provided)
56. Nourish Democratic People's Congress
57. All Youth Reclaim Party
58. LA RIBA Multipurpose Cooperative Society
59. Alliance Youth Party of Nigeria
60. The True Democrats
61. Democratic Peoples Congress
62. National Democratic Movement
63. Economic Liberation Party
64. Grassroot Ambassador's Party
65. All For All Congress
66. People Democratic Alliance
67. United National Youths Party of Nigeria
68. Peoples Liberation Party
69. Democratic Union for Progress
70. Citizen Democratic Alliance
71. African Action Group
72. Patriots Alliance Network
73. Democratic Leadership Party
74. Pink Political Party
75. Young Motivation & Awareness for Development Forum
76. Access Party
77. Youth Progressive Empowerment Initiative
78. Grassroot Ambassadors' Party
79. Republican Party of Nigeria
80. Sceptre Influence Party
81. Young Democratic Congress
82. Patriotic Nigerians Party
83. Far-Right Party
84. Democratic People's Party
85. United Citizens Congress
86. Reset Nigeria
87. New Nigeria Democratic Party
88. Save Nigeria People Party
89. Above All
90. Alliance for Youth and Women Party
91. Rebuild Nigeria Group
92. Citizen Progressive Party
93. Good Guardian Party
94. Abiding Greatness Party
95. Patriotic Peoples' Party
96. Development & Freedom Party
97. Peace, Unity & Prosperity Culture
98. The Populist Party
99. New Nigeria Leadership Party
100. All Allies Alliance
101. National Action Network
102. Coalition for Nigerian Democrats
103. Republican Party of Nigeria
104. Abundance Africa Alliance
105. Freewill Humanitarian Party
106. Peoples Emancipation Party
107. Peoples Liberation Congress Party
108. Peoples Democratic Congress
109. All Democratic Alliance
110. Advanced Democratic Alliance (ADA)










