Kungiyoyi 93 na neman rajistar zama jam'iyyu - INEC

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da babban zaɓenta a shekarar 2027 ke ci gaba da karatowa a Najeriya sama da ƙungiyoyi cassa'in da uku (93) ne suka miƙa buƙatar zama jam'iyyun siyasa gare ga hukumar zaben kasar INEC.
Sai dai mika wannan bukatar, ya sa wasu daga cikin manyan jam'iyyun hamayya a Najeriyar cewar, ƙara yawan jam'iyyun zai iya wargaza shirinsu na haɗewa wuri guda domin ganin sun karbe mulki daga hannun jam'iyya APC a zaɓen na 2027.
Mai magana da yawun hukumar zaben a Najeriya ta INEC Hajiya Zainab Aminu ta ce 'kawo yanzu hukumar ta karbi kusan kungiyoyi 93 da suka mika bukatarsu na son a yi musu rajistar zama jam'iyya.
sannan ta ce har yanzu su na nan su na ci gaba da karba, tare da duba yiwuwar yi musu rajistar, idan har sun cika ka'idar
Haka zalika ta ce doka ta bayar da dama ga dukkan wata kungiya damar su nemi a yi musu rajista, idan kuma sun cika ka'idar su shiga a fafata da su a zabe.
"Akwai wadatattcen lokaci, idan har sun cika ka'idojin da ake bukata, kuma abu ne da ba zai dauki lokaci ba, wajen tatancesu," a cewar Zainab Aminu mai magana da yawun hukumar ta INEC.
Sashe na 225A kundin tsarin mulkin kasar ya na cewa INEC na da ikon soke rijistar duka wata jam'iyya bisa wadannan ka'idojin:
- Idan jam'iyya ta kasa cike sharuddan yin rijista.
- Idan jam'iyya ta kasa samun kashi 25% na kuri'un da aka jefa a zaben shugaban kasa ko a karamar hukuma daya a zaben gwamna.
- Kasa cin zabe a kalla mazaba daya a zaben shugaban karamar hukuma, ko kujera daya ta dan majalisar dokokin jiha ko ta kasa ko kuma kujerar kansila guda daya.
Abin da masana ke cewa
Masanan harkokin siyasa a Najeirya irin su Farfesa Kamilu Fagge na cewar a tsarin dimokaradiyya irin na turai, hakan abin ci gaba ne.
Sai dai ya ce a ce a njam'iiyu kusan casa'in abu ne d azai haifar da rudani a wajen gudanar da zabe a Najeriya.
"Idan aka zo zabe wacce irin takarda dangwale zaai amfani da ita, a sa alamomin jam'iyya har guda casa'in. In ji Frfesa Kamilu Faggen
Sannan ya ce 'a yawancin masu zaben mu basu da ilimi da wayewar da za su iya bambance jam'iyyun su kansu, yawancin irin wadan nan jam'iyyun na jeka na yi ka ne, wato a akwatin yan takarar suke, babu ofis, ko wani abu da zaa ce na jam'iyya ne," a cewar Farfesa Kamilu Fagge.
Farfesa Kamilu Faggen ya ce sau da dama manyan ya siyasa ne kan kirkiro irin wadan nan jam'iyyu don bata wa abokin hamayyar su ruwa.
Sannan Farfesan ya ce 'a wasu lokutan musamman za kaga wata karamar jam'iyya su ko a kasa ba ita, idan aka yi zabe, sai kaga ta tafi kotu ta kawo matsaloli daban daban, wand idan a ce jam'iyyun za su kasance hudu ko biyar to da lamarun za su yi sauki,' in ji shi.
Me manyan jam'iyyun Najeriya ke cewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babbar jam'iyya hamayya a Najeriya ta PDP ta ce adadin masu neman rajistar jam'iyyun da INEC din ta karba abu ne da ke sake futo da rashin hadin kan da ke tsakanin shugabanin hamayyar kasar.
Ita ma jam'iyyar NNPP ta ce hakan ya sake futowa da gazawar jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC.
Sai dai a bangare guda ita kuwa jam'iyyar Labour maraba ta yi da yunkurin, amma ta ja hankalin hukumar zaben ta INEC da ta yi bin cike mai karfi akansu kafi ta yi musu rajista.
Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC, ta duk da zargin da ta ke yi na wasu daga cikin manyan masu hamayya da gwamantinsu ne ke da hannu wajen kitsa neman rijatsar sabbbin jam'iyyun, sannan suna da yakinin cewar su ne za su sake lashe zaben kasar na 2027 da ke karatowa.
A cikin shekarar 2020 ne dai hukumar zaben Najeriya ta soke wasu daga cikin jam'iyyun siyasar kasar daga 92 zuwa 18.
INEC din dai ta ce, ta dauki matakin ne bayan nazari a kan jam'iyyun kasar da yadda suka tabuka a zaben da ya gabata.











