Jam'iyyun da aka soke za su kai INEC kotu

Asalin hoton, Getty Images
Wasu jam'iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta soke rijistarsu sun ce za su maka hukumar a kotu domin matakin da ta dauka ya sabawa doka.
Matakin na INEC -- wanda ya rage yawan jam'iyyun siyasar kasar daga 92 zuwa 18 -- bai zo wa da jam'iyyun ta dadi ba.
Jam'iyyar People Trust wadda daya ce daga cikin jam'iyyun da aka soke rijistarsu ta ce INEC ta danne musu 'yanci.
A cewar Shugaban jam'iyyar, Ibrahim Barde, "matakin da INEC ta dauka ya yi hannun riga da tanadin da kundin tsarin mulkin kasa ya yi na bai wa kowa 'yancin hada kungiya."
"Yanzu uwar jam'iyyarmu za ta tattauna kuma a karshe za mu daukaka maganar zuwa kotu," in ji shi.
Ya bayyana cewa a baya ma an yi maganar rage yawan jam'iyyun Najeriya inda a zamanin tsohon shugaban INEC Farfesa Attahiru Jega aka soke wasu jam'iyyu.
Sai dai a cewar Barde "jam'iyyun sun je kotu kuma da suka ce kotu sun yi nasara."
Ya kuma ce "kotu ce za ta fassara ko abin da INEC ta yi ya yi dai-dai ko bai yi dai-dai ba."
Kazalika, shugaban gamayyar kananan jam'iyyu a Najeriya (IPAC) reshen jihar Kano, Alhaji Isa Inuwa Isa ya ce INEC ta yi gaggawa wajen rushe jam'iyyun.
A cewarsa abin da ya kamata a yi ba shi ne soke yawan jam'iyyun ba, kamata ya yi a gyara tsarinsu da kuma ingancinsu.
Ya bayyana cewa "a Amurka, suna da jam'iyyu akalla sun kai 70 ko dari kuma kowacce da hiuruminta."
Ya kuma musanta zargin da ke cewa gwamnati na bai wa jam'iyyu gudummawa inda ya ce "a haka gwamnati ta kafa wata doka ta tantance jam'iyyu."
"Kuma mun cika ka'idojin zama jam'iyyu." a cewarsa.
A ranar Alhamis ne dai Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da matakin hukumar na rushe jam'iyyun.
Ya ce INEC ta dauki matakin ne bisa damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ta na yi wa jam'iyyu rijista, da kuma soke rijastar jam'iyyu.











