Me ya sa aka hana mata tsayawa takara a zaɓen shugaban Uganda?

Wani matashi marar riga ya tsaya a saman wani ƙaramin tudu, yana ɗaga tutar Uganda. A bayansa akwai dandazon jama'a a wani gangamin da ɗan adawa Robert Kyagulanyi Ssentamu ya jagoranta.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai goyon bayan jagoran adawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar National Unity Platform (NUP), Robert Kyagulanyi Ssentamu, wanda aka fi sani da Bobi Wine, yana riƙe da tutar Uganda a taron yaƙin neman zaɓen jam'iyyar na ƙarshe gabanin babban zaɓen shekarar 2026 a Kampala a ranar 12 ga watan Janairun 2026.
    • Marubuci, Swaibu Ibrahim
  • Lokacin karatu: Minti 6

A watan Agustan shekarar da ta gabata, wata lauya kuma ƴar gwagwarmaya ƴar Uganda Yvonne Mpambara, ƴar shekara 34, ta miƙa takardar neman takara da nufin tsayawa takarar shugabancin ƙasarta.

Yaƙin neman zaɓen nata ya mayar da hankali ne kan gudanar da mulki da ya haɗa da ingantacciyar hidima ga al'umma, da kuma yi wa ɓangaren shari'a garambawul.

Amma a ranar 24 ga watan Satumba, 2025, ta gano cewa ba ta cikin waɗanda aka bai wa izinin tsayawa takara. Mpambara ta soki hukumar zaɓen Uganda, inda ta zarge ta da dakatar da ƴan takara mata daga shiga zaɓen.

"Wannan kai tsaye laifin yadda ake tafiyar da ƙasa ne," in ji ta.

"Muna da mata uku masu basira da za su iya shiga zaɓen, amma muna ganin tsarin ƙasa ya taka masu birki, ba mu samu damar yin hakan ba, kuma mun yi imanin cewa hukumar zaɓe ba ta da tsarin tantancewa na gaskiya.

Yayin da ƴan Uganda ke zaɓen shugaban ƙasa, masu kaɗa ƙuri'a za su zaɓi daga cikin jerin ƴan takara maza ne kawai.

Shugaban ƙasar mai ci Yoweri Museveni, mai shekaru 81, na neman wa'adi na bakwai a jere bayan shekaru arba'in yana mulki.

Babban mai ƙalubalantar sa ​​shi ne mawaƙin ɗan siyasa Robert Kyagulanyi Ssentamu, mai shekaru 43, wanda aka fi sani da Bobi Wine.

Sauran ƴan takarar shugaban ƙasa shida - Frank Bulira da Robert Kasibante da Joseph Mabirizi da Nandala Mafabi da Mugisha Muntu, da Mubarak Munyagwa - dukkansu maza ne.

Yayin mayar da martani kan sukar da Mpambara ta yi wa hukumar zaɓen, kakakinta Julius Mucunguzi, ya ce hukumar ta bi duk ƙa'idojin da aka gindaya a lokacin tantance ƴantakaran.

"Idan babu wata ƴar takara mace da ta gabatar da kanta kuma ta samu nasarar cika ka'idojin da aka gindaya, hukumar ba za ta saɓa ƙa'idojinta ba, mai yuwa ne a samu ƴan takara mata zalla, ko maza zalla, ko kuma gwauraye," in ji shi.

Magoya bayan shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni yayin gangamin farko na Museveni bayan tantancewar da hukumar zaɓen ƙasar masa don tsayawa takarar shugabancin ƙasar karo na bakwai a ranar 23 ga Satumba, 2025.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni yayin gangamin farko na Museveni bayan tantancewar da hukumar zaɓen ƙasar masa don tsayawa takarar shugabancin ƙasar karo na bakwai a ranar 23 ga Satumba, 2025.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar hukumar zaɓen, duk wanda ke da niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa dole ne ya kasance ɗan ƙasar Uganda tun haihuwarsa, mai shekaru aƙalla 18 da haihuwa, kuma mai rijistar katin zaɓe. Ana kuma buƙatar masu neman takarar shugaban ƙasa su biya kuɗin tsayawa takara na shilin ɗin Uganda miliyan 20 kwatankwacin fam 4,200.

Domin tantancewa don tsayawa takarar shugaban ƙasa, ƴan takara na buƙatar gabatar da sa hannun aƙalla 100 daga kashi biyu bisa uku na gundumomi 146 da ke ƙasar .

A batun Yvonne, ta ce hukumar zaɓe ba ta bayyana dalilin da ya sa aka ƙi amincewa da takararta ba.

"Lokacin da na yi ƙoƙarin miƙa fom ɗin magoya baya na, sun ce ƙarya ne kuma an yi su ne ba tare da bin ƙa'idojin da suka dace ba wurin tabbatar da ko na ƙarya ne ko a'a," in ji ta.

Uganda ta fara tsarin siyasar jam'iyyu da yawa a shekara ta 2005 bayan zaɓen raba gardama wanda sama da kashi 90 cikin 100 na masu kaɗa ƙuri'a suka goyi bayan tsarin.

Zaɓuka huɗu da aka gudanar tun daga wancan lokaci kowacce ta samu aƙalla mace ɗaya da ta tsaya takarar shugaban ƙasa.

Matar tsohon shugaban ƙasa Miria Kalule Obote ta tsaya takara a shekarar 2006; Beti Kamya ta yi takara a 2011; Maureen Kyalya ta fito a zaɓen a shekarar 2016; sannan Nancy Kalembe Linda ta kasance mace tilo a zaɓen 2021.

Masu sharhi dai na ganin rashin samun ƴar takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ake yi a yanzu yana kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na ciyar da mata gaba a harkokin siyasa da mulkin dimokraɗiyya.

Duk da haka, Uganda ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke da mata masu yawa a kan mukaman shugabanci. Shugaban majalisar dokokin ƙasar a halin yanzu, da mataimakiiyar shugaban ƙasa, da Firaminista duk mata ne, kuma kashi 45 cikin 100 na majalisar ministocin ƙasar mata ne. Bugu da ƙari, an keɓe kujeru 146 na majalisar wakilai ga mata na gunduma.

Matasa masu zaɓe a Uganda

Ba mata ne kaɗai ke jin an ware su daga wannan zaɓen ta shugaban ƙasar ba.

Ƙuri'ar ta zo ne a cikin matsin tattalin arziki da raguwar amincewa da hukumomin gwamnati. Ga matasa da yawa na Uganda, zaɓen ba wani lamari ne na siyasa kawai ba, amma wani gwaji ne na ko tsarin zai iya ba da damammaki.

Fiye da kashi 75 cikin 100 na al'ummar Uganda ƴan ƙasa da shekaru 30 ne, kuma yawancin matasa na yin kira da a ƙarfafa tattalin arziki a kuma daina nuna wariya.

Gloria Nawanyanga ƴar shekara 28 tana neman wakiltar matasa a matsayin ƴar majalisar dokoki a yankin tsakiyar Uganda.

"Idan aka bai wa matasa ƴancin tattalin arziki, Uganda za ta iya kai wa matsakaicin matsayi a bangaren tattalin arziki, ko ma ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka ci gaba a duniya cikin ƙanƙanin lokaci saboda mu ne mafiya rinjaye," in ji ta.

Har ila yau an duba batun yadda ake samar da kuɗaɗen gudanar da al'amuran siyasa, inda masu suka suka yi alla-wadai da yadda siyasa ta zama tamkar kasuwanci. Yvonne Mpambara ta yi gargaɗin cewa tsadar zaɓe na da nasaba da daƙile shigar matasa da sauran al'ummomin da ake nuna wa wariya.

"Bana tunanin wani daga cikinmu zai iya shiga harkar zaɓe nan gaba, siyasa ta yi tsada sosai, kuma wariya ce tun farko. Ta yaya mutum zai iya biyan shillings ɗin Uganda biliyan uku na tsayawa takarar ɗan majalisa?" in jin ta.

Magoya bayan madugun ƴan adawar Uganda kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar National Unity Platform (NUP) Robert Kyagulanyi Ssentamu, wanda aka fi sani da Bobi Wine

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan madugun ƴan adawar Uganda kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar National Unity Platform (NUP) Robert Kyagulanyi Ssentamu, wanda aka fi sani da Bobi Wine a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe na ƙarshe na jam'iyyar gabanin babban zaɓen 2026, a Kampala ranar 12 ga Janairu, 2026.

A duniya baki ɗaya, shigar matasa a harkokin siyasa ya sauya sosai. Wani sabon salon fafutuka da ake kira Gen Z ya sanya matasa suna gudanar da zanga-zangar neman shugabanci nagari, da bin doka da oda, da samar da ayyukan yi a ƙasashe irin su Kenya da Bangladesh da Madagascar da Nepal, da Morocco.

Bisa ƙididdigar da aka yi a ƙasar Uganda a shekarar 2024, matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa a ƙasar na ci gaba da ƙaruwa, inda mutane miliyan 9.4 ne kacal ke da aikin yi daga cikin waɗanda ke cikin shekarun aiki guda miliyan 25.1.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, shugaba Museveni ya buƙaci matasa da su yi amfani da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar domin cin gajiyar shirye-shiryen inganta rayuwar matasa na gwamnati. Ya kuma ƙara musu ƙwarin gwiwa da su sauya daga ɗabi'ar jiran ayyukan gwamnati zuwa fafutukar samar da arziki.

A halin da ake ciki kuma, jam'iyyar adawa ta National Unity Platform, ƙarƙashin jagorancin Bobi Wine, ta yi alƙawarin samar da ayyukan yi miliyan goma nan da shekara ta 2032, a cikin shirinta na "A New Uganda Now", da magance matsalar cin hanci da rashawa, da kuma ɗaura tattalin arzikin Uganda kan tafarkin fasaha.

Ga jagororin matasa kamar Gloria Nawanyanga, lokacin canji ya yi.

"Lokaci ya yi da matasa za su karɓi ragamar tafiyar da ƙasar nan saboda mu ne mafiya rinjaye," inji ta.

Yayin da Uganda ke shirin kaɗa ƙuri'a, ana sa ran ƙuri'ar matasan za ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara shugabancin ƙasar.

Atuhire Vandah ƴar shekara 24 mai sana'ar kifi a Luzira da ke wajen birnin Kampala, ta ce za ta so shugabannin ƙasar su magance matsalar cin hanci da rashawa.

"Ina roƙon waɗanda aka zaɓa su tabbatar da cewa kuɗaɗen inganta rayuwar matasa sun isa gare mu. Mun ji an sako kuɗin, amma da yawa daga cikinmu ba su taɓa karɓa ba saboda zamba," in ji ta.

Halimah Mutesi, ƴar shekara 38, ƴar kasuwa ce, ta yi kira ga shugabanni da su ba da fifiko wajen ƙarfafa gwiwar mata.

"Ina kira ga hukumar zaɓe da ta ci gaba da bai wa mata ƙwarin gwiwa har zuwa manyan matakai domin mu uwayen al'umma ne, kuma a mafi yawan lokuta, mun fi ne aka fi nunawa wariya," in ji ta.