Gwamnatin Sokoto ta amince da kafa cibiyar jami’an tsaro a yankin Tidibale

Asalin hoton, Sokoto State Government
Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da amincewa da kafa cibiyar tabbatar da tsaro a yankin Tidibale da ke jihar, inda ake zargin ‘yan bindiga da yi wa al’umma barazana tare da tursasa ma wasu barin muhallansu.
Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun Abubakar Bawa, shugaban sashen yada labaru na ofishin gwamnan jihar.
Sanarwar ta ce samar da cibiyar tabbatar da tsaron za ta taimaka wa ayyukan wata irin ta a karamar hukumar ta Isa.
Haka nan sanarwar ta karyata wani bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta da ke cewa mutanen yankin Tidibale ne da ‘yan bindiga suka kora daga kauyukansu.
A cewar sanarwar mutanen da aka gani a bidiyon, su ne wadanda gwamnati ta kwashe daga kauyukan yankin na Tidibale zuwa cibiyar karamar hukumar bayan samun bayanai na tsaro.
“Tabbas mutanen Tidibale ne, amma ba yan bindiga me suka koro su ba,” a cewar sanarwar.
“Mutane ne da aka kwashe su na wucin-gadi zuwa cibiyar karamar hukuma bayan rade-radi game da yiwuwar fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga.
“Haka nan kuma an riga an mayar da mutanen zuwa kauyensu na Tidibale, inda kuma jami’an tsaro ke aikin tabbatar da doka da hana ayyukan ‘yan bindiga,” a cewar sanarwar.
A baya-bayan nan ne rahotanni daga jihar ta Sokoto suka bayyana yadda mutane ke guje wa kauyukansu sanadiyyar barazanar ayyukan ‘yan bindiga.
Sokoto na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro ta kungiyoyin ‘yan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.










