'Babu sauran kulawa da gwamnati ke bai wa iyalin Tafawa Balewa'

Abubakar Tafawa Ɓalewa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kashe Tafawa Ɓalewa a juyin mulkin soji na farko na Najeriya
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ake cika shekara 60 da juyin mulkin soji na farko a Najeriya, BBC ta kai ziyara inda aka binne gawar mutum mafi girman muƙami da aka kashe a lokacin juyin mulkin.

Abubakar Tafawa Ɓalewa shi ne Firaiministan Najeriya na wancan lokaci, kuma yana cikin waɗanda sojojin suka hallaka a shekarar 1966, baya ga Firimiyan jihar Arewa da na Yamma da kuma manyan sojoji da masu riƙe da muƙaman gwamnati.

Shi ne juyin mulkin da ya kawo ƙarshen jamhuriya ta farko a Najeriya, wadda ta ƙunshi fitattun mutane da suka yi fafutikar samun ƴancin kan ƙasar.

An binne marigayin ne a garin Bauchi da ke jiharsa ta asali a arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin iyalan Tafawa Ɓalewa da BBC ta zanta da su, akwa jikan marigayin, Abubakar (Billy) Tafawa Ɓalewa wanda ya nuna takaici kan halin da kabarin kakan nasa ke ciki da kuma kuma iyalansa.

"Babu", in ji Billy, a lokacin da BBC ta tambaye shi game da kulawar da gwamnati ke bai wa iyalan marigayin.

Ya ƙara da cewa "bayan shekara 50 da rasuwarsa gwamnati ta tsayar da ɗan fanshon da take bayarwa, kasancewar hatta ɗan autan gidan ya wuce shekara 60.

"Idan na kai ka gidan ma za ka ga babu wani gyara. Gyara na ƙarshe da aka yi, gwamnatin jiha ce ta yi, lokacin Abutu (Chris Garba Abutu), sai kuma Ahmed Muazu, waɗanda suka yi (wa gidan) kwaskwarima," kamar yadda jikan na Ɓalewa ya shaida wa BBC.

Sai dai Billy ya ce yana jin daɗin yadda yanzu aka fara ganewa da fahimtar irin rawar da su kakansa suka taka da sadaukarwar da suka yi wajen gyarawa da ciyar Najeriya gaba, "ba kamar yadda ake gani yanzu al'umma na sadaukar wa ga shugabanni ba."

A game da nauyin da yake kansu na kasancewa ƴaƴa ko jikokin tsohon firaministan na Najeriya, Abubakar Billy ya ce nauyi ne babba da suke alfahari da ɗauka.

"Ina yawan faɗa cewa babban nauyi ne. Nauyin ma ya fi gata ko daɗin yawa. Na farko dai ba kuɗi ya bari ba, na biyu bai wawushe kuɗi domin gina kansa ba kamar yadda ake yi a yanzu."

Billy ya ce bai yi kamar ake yi a yanzu wajen ba ƴan'uwan da iyalai kwangila, wajen ba iyalai kwangila, "sannan akwai nauyin zaton ka zama mutumin kirki mai amana," in ji shi.

Rayuwarsa a cikin gida

A game da yadda ya kasance yana rayuwa da iyalansa a gida, Billy ya ce iyayensu sun faɗa musu cewa marigayin mutumin kirki ne mai haƙuri, amma mai fushi idan ya ga rashin gaskiya.

"Kullum yana faɗa musu cewa a riƙe gaskiya. Muma abin da muka ɗauka ke nan saboda riƙe darajar gidan. Shi ya sa har yanzu babu sunan gidanmu a cikin waɗanda suka ɓata Najeriya. Wannan yake ƙara mana kwanciyar hankali."

Ya ce ƙoƙarin da iyayensu suka yi na kare mutuncin gidan ne yanzu ya zama nauyi a kansu na cigaba da kare martabar gidan.

"Mahaifina ne babban ɗansa. Nakan tambaye shi yadda mahaifinsa ya yi da su, inda yake yawan faɗa min cewa ya ja shi a jiki sosai. Yana nuna masa abubuwa da yawa na rayuwa, amma bai taɓa saka shi a harkokin gwamnati ba."

Abubuwan tunawa da shi

Tafawa Balewa

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da abubuwan da ake tunawa da shi a Najeriya, Billy ya ce yana ganin akwai sauran aiki a gaban gwamnati.

"Ni dai gaskiya idan ka bar ni, zan ce Najeriya ba ta yi abin da ya dace wajen tattalin tarihinsu ba. Misali ka ga akwai ƙabarinsa da aka ƙaddamar a 1979. Sai kuma dandali da gwamnatin tarayya ta yi, sai asibitoci da wasu abubuwa na jiha."

Ya ce takardar kuɗi da aka saka shi, yanzu lokaci ya sa ba a amfani da ita. "Naira biyar ce, kuma ba a amfani da ita sosai a yanzu. Amma wannan irin canjin yanayi ne."

Ya ce yanzu shugabanni suna ƙoƙarin kafa komai da ma kafa ƴaƴansu a madafun iko saboda gudun kada a watsar da bayansu.

"Ka ga ko ƙabarin, tun bayan ƙaddamar da shi babu wani babban aikin gyara da aka yi, sai dai kwaskwarima kaɗan-kaɗan lokaci bayan lokaci kuma gwamnatin jiha ke yi."

Billy ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki ragamar gidan, "amma dai ina yaba wa shugabannin Najeriya domin sun yi nasu ƙoƙarin. Najeriya ce tana da girma kuma buƙatu sun yi yawa. Amma yana da kyau a riƙa tuna baya."

Ya ce sun yi ƙoƙari wajen shugabanci da ƙoƙari haɗa kan ƙasar, "duk da cewa a lokacin ana fama da duhun saɓani da rashin fahimta, amma suka yi ƙoƙari suka yi mulki."

A game da irin bambancin da yake da shi da sauran ƴansiyasa, Billy ya ce babban burinsa ya zama murya ta samar da daidaito.

"A zamaninsa manyan muƙamai ya ba Yarbawa ba tare da la'akari da ƙabilarsu ba. Amma yanzu ƙabilanci na taka rawar gani sosai wajen naɗa muƙamai a mulki. Sannan suma mabiya suna fifita son shugabannin ɓangarensu ba tare da duba cancanta ba."

'Shahada ya yi domin sadaukarwa ga Najeriya'

Holunansa

A game da batun ko sun yafe wa waɗanda suka kashe musu kaka, Billy ya ce su a wajensu, marigayin shahada ya yi.

"Kowane musulmi yana son irin wannan mutuwar. Mun ɗauka mutuwar za ta zama izini wajen haɗin kan ƙasar ne da zama izini wajen kawo ci gaba mai ɗorewa. Sun sadaukar da rayuwarsu ne domin Najeriya."

Ya ce duk da sun san da ƙulle-ƙullen da ake yi, "amma suka zauna. Da na yanzu ne da guduwa za su yi. Amma wataƙila nan gaba a samu shugabanni irin su."

Ya ce ya yi shekara uku yana neman ko zai samu saɓani da aka taɓa samu tsakanin Tafawa Ɓalewa da Ahmadu Bello, "amma har na gama bincikena ban samu ba. Yanzu kuwa ana yawan saɓani saboda son rai fiye da fifita al'umma."

Yadda iyalansa suke ciki

Billy ya ce Tafawa Ɓalewa ya rasu ya bar mata huɗu da ƴaya 20, "amma yanzu saura ƴaƴa 14, duka mata sun rasu. Jikoki gaskiya ba zan iya ƙididdigewa ba a yanzu."

Sai dai ya ce har yanzu sunan gidan na nan, "Kar ka manta akwai Adamu Tafawa Ɓalewa da ya yi mataimakin gwamna a tsakanin 1979 zuwa 1983, akwai Ambasada Balarabe Tafawa Ɓalewa ya yi takarar gwamnan, kuma babban amsabada."

Ya ƙara da cewa suna cigaba da riƙe gaskiya kamar yadda kakansu ya yi, "duk wani jagwalgwalo ba a samunmu a ciki. Ba ma shiga rashin gaskiya."

A game da irin kula da suke samu daga gwamnatin, Billy ya ce tun kakansu yana shekara 50 da rasuwa aka tsayar da fanshonsa.

"Yanzu babu wani yaro. Ɗan autan ma yanzu ya haura shekara 60 a duniya. Amma gaskiya babu wata kulawa ta musamman. Ya kamata a zo a gyara gidan da ya bari, a mayar da shi ɗakin karatu ko gidan tarihi, sannan a tattara wasu abubuwan tarihi da suka shafe shi a wuri ɗaya."

Tarihin Tafawa Ɓalewa

An haifi Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa a garin Tafawa Ɓalewa da ke jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekarar 1912.

Ya yi karatu a makarantar horon malamai ta Katsina daga ( 1928 zuwa 1933), sannan ya zamo malami, kuma shugaban makarantar Bauchi Middle School.

Ya yi karatu a makarantar horas da malamai ta London daga ( 1945 zuwa 1946), inda ya samu shaidar malunta.

A lokacin yaƙin duniya na biyu ya nuna sha'awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na 'Bauchi Discussion Circle'.

Sannan daga bisani ya shiga siyasar malamai inda aka zaɓe shi mataimakin shugaban ƙungiyar malaman Arewa.

A shekarar 1952 ya zamo ministan ayyuka na Najeriya, sannan ya zama ministan sufuri a 1954, sannan ya zamo jagoran jam'iyyar NPC a majalisar wakilai ta ƙasa.

Ya zamo firaministan farko na Najeriya bayan da ƙasar ta samu 'ƴancin kai a shekarar 1960.

A shekarar 1966, wasu sojoji suka yi yunƙurin juyin mulki inda a nan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe shi.