Yadda ake sukar gwamnatin Katsina kan shirinta na sakin waɗanda aka kama da zargin zama ɓarayin daji

Hoton Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda

Asalin hoton, Umar Dikko Radda

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya gamayyar kungiyoyin arewacin kasar ta CNG, ta nuna rashin gamsuwarta kan matakin da ake cewa gwamnatin jihar Katsina na dauka na sakin wasu barayin daji da ake rike da su.

Gwamnatin za ta sake su ne duk da cewa suna daga cikin wadanda ake zargi da kai hare-haren da suka hallaka jama'a da dama a jihar.

Su dai hukumomin jihar na cewa sakin barayin dajin na daga cikin yarjeniyoyin da al'ummar wasu kananan hukumomin na jihar ta Katsina suka amince da su domin samun zaman lafiya mai dorewa.

To amma shugaban gamayyar kungiyoyin ta CNG Jamilu Aliyu Charanci, a tattaunawarsa da BBC, ya ce hakan ba komai ba ne illa nuna rashin sanin ya-kamata:

''Babu wani shugaba ko kuma wata kasa ko wata al'umma wadda take cikin hankalinta, wadda ta san abin da ya kamata, a ce an samu wani tsagera, danta'adda, ya koma daji ya kwashe shanun al'umma, ya hana mutane zuwa gona, a ce kuma wai shugaba ya zo ya ce wadannan mutane yake son a zauna a sake su bayan gwamnati ta kama su.''

Dangane da maganar cewa al'ummar jihar ne suka nemi a yi sasancin, sai shugaban gamayyar ya ce:

''Babu wani sasanci da gwamnati za ta yi da mutumin da ba shi ya nemi sasancin nan ba. A ce wani mutum ana binshi, ana lallaba tai, ana mishi dadin baki, cewa ya zo a yi sasanci, ban taba ganin inda aka yi shi ba.

''Kuma sasancin nan ba yau aka fara yinshi ba. A Zamfara Matawallen Maradun ya yi sasancin, bai yi amfani ba.

''Mutanen nan ba su da amana. Duk irin yanda za ka yi da sasanci da su, in za su dauki Al Qur'ani su dafa wallahi gobe sai sun ci amanarka.

''Gwamna bai kalli yawan 'yansandan da aka kashe ba. Bai kalli yawan mutanen da aka kashe ba. Bai kalli dimbin biliyoyin kudin da al'umma suka biya na fansa ba. Bai kalli kukan dimbin mutanen da suka rasa 'yan uwansu ba.

''Kuma wannan yana nuna cewa idan ka zama danta'adda a Najeriya ka zama mutumin da ka gagari kowa. Ka zama mutumin da gwamnati za ta rika lallabarka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangane da batun cewa an samu sauki a wasu wuraren da aka yi sasanci da barayin dajin, Jamilu Caranci ya ce, samsam ba haka abin yake ba domin babu wani sauki da aka samu, ganin yadda sai an sanar da cewa an yi sasancin amma barayin su sake kai hare-hare.

Ya bayar da misalin inda ya ce, barayin dajin sun kai hari kan masu maulidi, da inda suka tare hanya suka kwashi mutane yayin da ake maganar an yi sasanci da su.

''Yau kauye nawa ne mutane suke biyan kudin fansa a tsakanin Katsina da Zamfara da Naija da Kaduna?

''Kauye nawa ne mutane ba sa iya kwana a garuruwansu? Yau in ka je garuruwan nan kusan an kwashe duka shanunsu, suna hannun 'yanbindigan nan.''

Shugaban gamayyar kungiyoyin na Arewa, ya ce abin da suke son gani kawai shi ne, gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi su hada karfi da karfe, su tabbatar da cewa sun fito sun yaki mutanen nan dari bisa dari. Su tabbatar da cewa sai sun kai mutanen nan karshe, 'yan kalilan din da suka rage, in ma za a dauko su a ce a ajiye su sai a ajiye su;

''Gwamnatin jihar Katsina da Arewa gabakidaya su gaggauta watsar da wannan magana ta cewa ka je ka kama mutumin da aka je aka kai shi kotu da sunan barawon daji ko danta'adda, ka je ka ce za ka sake shi.

''Wannan karan-tsaye ne ga shari'a, da kaskanta jami'an tsaro da kuma iyalan jami'an tsaron da suka rayukansu a wannan wuri.

''Saboda haka mu ba mu yarda da wannan al'amarin ba, ba ma goyon bayanshi, kuma muna kira ga su kansu gwamnoni da duk wani mai ruwa da tsaki a arewacin Najeriya, ya tabbatar da cewa ya fito ya yi Allah-wadarai da wannan abin.''