Nafilolin da ake son mai azumi ya riƙa yi a watan Ramadan

Masallata

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Addinin musulunci ya kwaɗaitar da Musulmai da ƙara ƙaimi wajen sallolin nafila musamman cikin dararen watan Ramadan.

Sallolin dare na daga cikin ibadun cikin dare da musulunci ya kwaɗaitar da ƙarfafa gwiwar yinsu, musammana a lokacin watan azumin Ramadan.

Cikin Hadisi Manzon Allah (SAW) ya karfafa wa al'ummarsa game da yin sallolin dare a kowane lokaci.

Nau'o'in nafilar dare cikin watan Ramadan

Shekikh Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin masallacin Juma'a na Okene a jihar kogi ya ce akwai nau'ikan sallolin nafila da ake aiwatarwa cikin dare, waɗanda kuma aka ƙarfafa yin su cikin dare a lokacin watan azumi.

Tarawih - Limamin Juma'ar ya ce sallar tarawih ko tahajjud ko ƙiyamu Ramadan duka abu guda ne.

''Waɗannan sallolin dare su ne ake kira da Kiyamullaili, wato Tahajjud ko Tarawihi ko Kiyamu Ramadan,dukkanin su sallah guda ce ba salloli ne mabanbanta ba'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa ''masu tunani ko ra'ayin cewa wanda ya yi sallar Tahajjud ya fi wanda ya yi Tarawihi lada, wannan ba daidai ba ne. Domin a nan sun ɗauka cewa salloli ne daban-daban, alhali ba haka ba ne, sallah guda ce mai sunaye mabanbanta''.

Sai kuma jam'in shafa'i da witiri da ake yi a lokacin Ramadan, wanda shi kuma dama an saba yinsa ko a wajen Ramadan, sai dai a Ramadan ana yin jam'insa, kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya yi a aikace.

Fa'idar sallolin dare

Masallata

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babban limamin Juma'ar na Okene ya ce sallolin dare na da falala sosai, kuma suna da matuƙar muhimmanci ga rayuwar Musulmi.

''Sallar dare wata ibadah ce ta nafilah mai girma kuma mai matuƙar muhimmanci, wadda mumini yana yin ta ne domin neman rahamar Allah, da neman yardar Allah da kuma samun kusanci ga Allah''.

''Ana yin ta ne da neman Allah Subhanahu wa Ta'ala ya biya wa Musulmi buƙatunsa, kuma ya yaye masa wasu matsaloli da suke damunsa. Wannan shi ne kaɗan daga cikin manufofin yin sallolin dare'', kamar yadda malamin addinin ya bayyana.

Ya ƙara da cewa cikin hadisi Annabi (SAW) ya ce "Duk wanda ya yi sallar dare a cikin watan Ramadan, yana mai imani, kuma yana mai fatan samun lada da rahama daga wurin Allah, to za a gafarta masa dukkanin zunubansa da suka gabata." [Bukhari]

''Haka nan Imamu Tirmizi ya ruwaito, Abu Zar Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce"duk wanda ya sallaci sallolin dare tare da liman, har aka kare, to kamar ya sallaci dukkanin dare ne baki ɗaya."

Shehin Malamin ya ce ''wannan a takaice kenan, don haka ko shakka babu, sallolin dare a cikin watan azumin Ramadan, suna da muhimmanci sosai ba kaɗan ba''.

Yaya ake yin sallolin?

Masallata

Asalin hoton, Getty Images

Sheikh Murtadha ya ce ''Annabi (SAW) yakan sallaci sallar dare ta hanyar yin Raka'o'i 11, a lokacin watan Ramadan da kuma wajen sa''.

Amma dai kuma idan mutum ya sallace su fiye da hakan ma bai yi laifi ba, kamar yadda malamin ya yi bayani.

Limamin Juma'ar ya ce an karɓo hadisi daga Abdullahi Dan Umar ya ce, wata rana wani mutum ya tambayi Annabi (SAW) game da sallar dare, sai Annabi (SAW) ya ce: "Sallar dare Raka'a biyu-biyu ce, amma idan mutum ya ji tsoron kusantowar sallar asuba, to sai ya sallaci Raka'a ɗaya, sai ta zamar masa witiri akan sallolin da ya sallata." [Bukhari]

''Don haka irin jayayya da sabani da rashin fahimtar juna da ake samu tsakanin waɗanda suka tsaya a raka'a 11 kawai, da waɗanda suke sallatar fiye da hakan bai dace ba'', kamar yadda malamin ya yi ƙarin haske.

Ana iya barin Ashan saboda Tahajjud??

Malamin addinin ya hori musulmi su jajrice da duka sallolin la'akari da cewa suna da wa'adi (wata guda)

Malamin ya kuma nuna fifikon sallar tarawih fiye da tahajjud.

''Ai hadisin da anabi ke cewa wanda ya yi salla a bayan liman tun daga farko har ƙarshe za a rubuta masa adan ya kwana yana salla, hadisin a kan sallar tarawih ya yi magana ba sallar tahajju'', a cewarsa.

Amma dai duk da haka malamin addinin ya ce yana da kyau musulmi su dage a wannan wata domin samun dacewa da ɗinbim alkairan da ke tattare da sallolin dare.

Yaushe ake yin nafilolin dare?

Sheikh Murtadha Muhammad Gusau ya ce ana yin nafilolin ne bayan gama sallar Isha'i har zuwa kafin fitowar alfijir.

''Wannan duk lokacin ta ne, kuma kowane lokaci mutum ya yi ta daidai ne'', in ji shi.

''Abinda ake buƙata daga wurin bawa shi ne, ikhlasi, yi domin Allah, ƙauce wa riya da ƙauce wa yin abu domin mutane'', in ji babban limamin Juma'ar.

Haka kuma Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ce mutum zai iya nafilolinsa a gida kuma zai iya zuwa masallaci jam'i, sai dai ya ce zuwa masallacin ya fi falala da lada