Yadda Barcelona za ta iya farke cin da Atletico ta yi mata

Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

A gobe Talata, 3 ga watan Maris ne za a fafata wasan zagaye na biyu na wasan gab da na gasar cin kofin Copa del Rey da za a buga tsakanin Atletico Madrid da Barcelona a gidan Barca.

A wasan na farko da aka fafata a filin wasa na Metropolitano, Atlético Madrid ce ta lallasa ƙungiyar Barcelona da ci huɗu da nema.

Jim kaɗan bayan wasan ne kocin Barcelona ya bayyana cewa ƙungiyar za ta iya farkewa, ta ma doke Atletico a zagaye na biyu na wasan.

Wannan ya sa ake ganin akwai wasu dalilai shida da ake gani a matsayin abubuwan da ke ƙarfafa gwiwa a wasan na zagaye na biyu.

1 - Sakamako 12 a ƙarƙashin Flick

Tun bayan da kocin ɗan Jamus ya karɓi ragamar horas da ƴanwasan, ƙungiyar ta samu nasara a wasa 12 da ƙungiyar ta ci nasara da ƙwallo huɗu ko sama da haka. A cikin wasa 12 ɗin, guda takwas ƙwallo huɗu ta zura, sauran huɗun ta lallasa Valladolid da ci 7 da nema, sannan ta lallasa Young Boys da ci 5, dai wanda ta lallasa Valancia da ci 6, sai Olympiacos da ci 6 da 1.

2 - Warkewar zaratan ƴanwasa

Idan abubuwa suka tafi yadda ƙungiyar ke so, Barcelona na sa ra zaratan ƴanwasanta irin su Pedri da Raphinha da Rashford duk sun warke sun koma taka leda.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan shi ma zai taimaka wajen ƙara ƙarfafa gwiwar ƙungiyar domin tunkarar Atletico Madrid.

3 - Magoya baya

Daga cikin abubuwan da ƴanwasan suke sa ran za su taka rawa, akwai irin goyon bayan da ƙungiyar take sa ran samu daga masu kallo.

A kakar bana, Barcelona ta lashe dukkan wasanninta na gida tun bayan da ta koma taka leda a filin wasa na Spotify Camp Nou, inda ta samu nasara a wasa 8 da ta buga.

4 - Wattsakewa

Yadda Barcelona ta samu nasarar ƙarewa a ta biyar a wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun turai, wanda ya sa ta samu gurbi a wasannin ƴan 16 kai-tsaye ya taimaka mata wajen samun hutu na ɗan lokaci daga wasannin turai.

Ita kuma Atletico ta buga wasanni uku na neman cike-gurbi. Wannan ya sa ake tunanin gajiya ma za ta taka rawa.

5 - Ta taɓa farke ci huɗu da nema a baya

An taɓa lallasa Barcelona da huɗu da nema a Paris, a wasan zagaye na biyu, Barca ta samu nasara da 6 da ɗaya.

wannan ya sa wasu suke ganin tamkar ƙungiyar za ta iya maimaita abin da ta yi a baya.

6 - Tuna baya

A kakar 1996/97, an yi wani wasa da ya shiga cikin tarihin wasannin ƙwallon ƙafa da suka fi ɗaukar hankali. An tashi 2-2 a wasan farko a Madrid, amma a wasan zagaye na biyu, tun kafin hutun rabin lokaci Milinko Pantic ya zura ƙwallo rigis a ragar Barcelona, inda ya koma ana doke ta da ci biyar da biyu.

Ana komawa hutun rabin lokaci ne Ronaldo ya zura ƙwallo biyu a minti uku, amma Pantic ya ƙara zura ƙwallo ta huɗu. Amma daga bisani Figo da Ronaldo da Pizzi suka zura ƙwallo, inda Barcelona ta samu nasara da ci 5-4 a wasan.