KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Litinin 11/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka na cikin garari - Trump

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita tsakanin ƙasarsa da Iran na cikin gagarin, bayan ɓangarorin sun ƙi amincewa da dakatar da yaƙin.

    Trump ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya sake nanata iƙirarin samun "cikakkiyar nasara" a kan Iran.

    A cewarsa, Iran ta yi tunanin zai gaji ne ko kuma ya dakata saboda matsin lamba, inda ya ce babu matsin lamba da yake fuskanta a game da yaƙin.

    Ya kuma bayyana daftarin da Iran ta rubuta na tsagaita wuta da "rashin hankali" bayan da farko ya bayyana cewa ba za ta saɓu ba su amince da yarjejeniyar.

    Har yanzu dai farashin man fetur na ƙara hauhawa saboda rashin samun tabbaci kan tsagaita wuta a yaƙin.

  2. Babu ruwana da tantance ƴantakarar gwamnan APC - Wike

    Wike

    Asalin hoton, Lere Olayinka

    Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babu abin da ya shafe shi da tantancewar fitar da ƴantakarar gwamnan jam'iyyar APC da aka yi.

    Wike ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafofin sadarwa na zamani, Lere Olayinka ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa shi ba ɗan APC ba ne, don haka ba shi da ta cewa kan tantancewar, sannan kuma babu abin da ya shafe shi da abin da ya faru.

    "Ni ba ɗan APC ba ne, don haka abin da ke faruwa a wajen tantancewar bai dame ni ba. Ko da sun fitar da sakamakon tantancewar ni babu ruwana. Me zai sa in yi magana kan abin da bai shafe ni ba?"

    Sai dai ya ce haɗakar "Rainbow Coalition" ta jihar Rivers an assasa ta ne domin gabatar da tsare-tsaren fuskantar babban zaɓen 2027, musamman a wuraren da suke da ƙarfi domin ciyar da jihar gaba.

    Ya kuma yaba da ƙoƙarin ƴan kwangila a Abuja, inda tsare-tsarensu na ayyukan da za su ƙaddamar domin bikin taya Bola Tinubu murnar shekara uku na tafiya daidai.

  3. Starmer ya sha alwashin tinkarar ƙalubalen shugabanci bayan koma baya a zaɓe

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya sha alwashin fuskantar ƙalubalen shugabancin da ya taso bayan kayin da jam'iyyarsa ta sha a zaɓen makon da ya gabata, yana mai cewa ba zai yi kasadar jefa kasar cikin rudani ba.

    Starmer ya ce ya fahimci dalilan da suka fusata masu jefe ƙuri'a idan aka yi la'akari da sauyin da ka samu a rayuwar yau da kullum.

    Ya ce za a gabatar da kudurorin doka a wannan makon domin baiwa gwamnati karfi don daukar matakin da ya kamata.

  4. Miliyoyin mutane na iya fuskantar yunwa saboda matsalar mashigar Hormuz - MDD

    Shugaban wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya da aka kafa domin daƘile wata matsananciyar matsalar jin kai ya yi gargadin cewa dubban miliyoyin mutane na iya fuskantar yunwa da fari idan ba a dawo da jigilar takin zamani ta mashigin Hormuz cikin gaggawa ba.

    Jorge Moreira da Silva, babban daraktan Hukumar Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya kuma shugaban tawagar, ya shaida wa kamfanin AFP cewa suna da ‘yan makonni kaɗan ne kawai domin kauce wa wata babbar matsalar jin ƙai.

    Ya ƙara da cewa ana iya fuskantar wani yanayi da zai jefa ƙarin mutum miliyan 45 cikin yunwa da fari.

  5. Afirka ta Kudu ta ayyana matsalar rashin kyawun yanayi a matsayin babban bala'i

    Ruwa ya mamaye titi

    Asalin hoton, Lulama Zenzile/Gallo Images via Getty Images

    Bayanan hoto, Ruwa ya mamaye titi

    Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ayyana matsalar rashin kyawun yanayi da ke shafar larduna da dama na ƙsar a matsayin babban bala'i a ƙasa.

    Hukumomi a Afirka ta Kudu sun ce an ɗauki matakin bayan mamakon ruwan sama da ambaliya da hadari da walƙiya da iska mai ƙarfi da dusar ƙanƙara da suka lalata gine-gine da muhimman ayyuka a yankuna da dama.

    Zuwa yanzu hukumomi ba su yi ƙarin bayani ba kan irin ta;annatin da rashin kyawun yanayin ya haifar.

    Elias Sithole, shugaban hukumar yaƙi da bala'oi a Afirka ta Kudu ta ayyana lamarin a matsayin babban bala'i a ƙasar.

    Sithole ya yi kira ga gwamnati da ta samar da tallafi ga hukumar don ta samu damar aiwatar da tsare-tsarenta na ganin ta magance matsalolin yanayin.

  6. WHO ta tabbatar da masu cutar Hantavirus bakwai a wani jirgin ruwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu mutum bakwai da aka tabbatar sun kamu da cutar Hantavirus wadanda ke cikin wani jirgin ruwa da aka samu yaɗuwar ƙwayar cutar.

    Wata mata ƴar Faransa ita ce ta baya-bayan nan da aka tabbatar ta kamu da cutar bayan killace ta a birnin Paris.

    Marar lafiyar na kwance a asibitin da ake kula da wadanda suka kamu da cutar inda aka dauki matakai masu tsanani domin ganin an dakile yaduwar cutar.

    Matukin jirgin ya saki wani bidiyo da yake yabawa da jarumtar da fasinjojin jirgin suka nuna a lokacin da suka samu kansu cikin yanayi mai wahala.

  7. Isra’ila ta ce harin ƙungiyar Hezbollah ya jikkata sojojinta uku

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa an jikkata sojojinsu uku a wani hari da aka kai da jirgi mara matuƙi a kudancin Lebanon, sai dai ba su bayar da ƙarin bayani ba.

    Tun da farko,ta sanar da cewa ta kai hari kan wurin da sojojin Isra’ila suka taru a yankin Tayyiba da ke kudancin Lebanon, tana mai cewa an yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen kwashe waɗanda suka jikkata.

    A safiyar yau ma, Isra’ila ta sanar da cewa an kashe ɗaya daga cikin sojojinta a wani hari da aka kai da jirgi mara matuƙi a wani yanki kusa da iyakar Lebanon.

    A gefe guda kuma, Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Lebanon ya ruwaito cewa Isra’ila ta kai hari ta sama a ƙauyen Aba da ke arewacin ƙasar da safiyar yau, inda mutum biyu suka mutu sannan biyar suka jikkata.

    Rahoton ya kuma ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hare-hare sau biyu cikin ƙasa da sa’a guda a yankin Kafr Roman da ke kudancin Lebanon.

  8. Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu - Koriya ta Kudu

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasar Koriya ta Kudu ta bayyana cewa za ta mayar da martani kan harin da aka kai wa wani jirgin dakon kaya mallakin kamfanin ƙasarta a Tekun Fasha, bayan bincikenta ya gano waɗanda ke da hannu a harin.

    A cikin wata sanarwa da Koriya ta Kudu ta fitar, gwamnatin ƙasar ta yi Allah-wadai da harin tare da cewa tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ƙwararrun Koriya ta Kudu sun gudanar da binciken farko domin tantance irin ɓarnar da aka yi wa jirgin. Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Kudu ta kuma wallafa hotunan jirgin da ya lalace sakamakon harin da aka kai masa a yankin Tekun Fasha.

    Jirgin dakon kayan mai suna HHM Namo, wanda kamfanin sufurin ruwa na HMM ya mallaka, ya fuskanci hari ne da wasu makamai guda biyu da ba a san ko su waye suka harba ba a ranar 4 ga watan Mayu yayin da yake wucewa ta mashigar Hormuz.

    Rahotanni sun ce babu wanda ya rasa ransa a harin.

    Tun da farko dai Iran ta musanta hannu a harin da gobarar da ta tashi a cikin jirgin.

  9. Babu tattaunawa har sai an kawo ƙarshen yaƙi ta ko wanne fanni - Iran

    ....

    Asalin hoton, tasnim news agency

    Kwamandan hedikwatar rundunar juyin juya halin Iran ya bayyana cewa Iran ba za ta ci gaba da tattaunawa ba har sai an kawo ƙarshen yaƙi ta ko wanne fanni.

    Mohammad Ali Jafari ya ce dole ne a fara cika wasu sharudda kafin komawa teburin tattaunawa, ciki har da ɗage takunkumi, sakin kuɗaɗen da aka ƙwace, da kuma biyan diyya kan barnar da yaƙi ya haifar. Ya kuma jaddada cewa dole ne a amince da ikon Iran kan mashigar Hormuz.

    Ya ƙara da cewa shugaban Amurka ya shiga wani hali na rashin tabbas saboda gazawa wajen cimma manufofinsa, yana mai cewa ana ƙoƙarin maye gurbin nasarar da ba a samu a yaƙi da matakan diflomasiyya.

  10. Shugaba Ramaphosa ya yi allawadai da cin zarafin baƙi a Afirka ta Kudu

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi tur da rikicin baya-bayan nan da miyagun ayyuka da ake aikatawa kan bai a wasu yankunan ƙasar.

    Cikin wata sanarwa, Shugaba Ramaphosa ya ce sam ba ya cikin tsare-tsaren gwamnati tare da yin kira ga mutane da su zama masu bin doka da oda a ƙasar.

    Shugaba Ramaphosa ya ce ba za a lamunci irin miyagun laifukan da ake aikatawa ba.

    A baya-bayan nan Afirka ta Kudu ta fuskanci matsin lamba daga Ghana da Najeriya bayan da ƴan ƙasashen suka fuskanci cin zarafi.

    Hukumomi a Ghana da Najeriya sun ce suna kwashe ƴan ƙasarsu da suke son komawa gida.

  11. An kubutar da ƴan Ghana 28 da aka yi yunƙurin safararsu

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana ta ce an kuɓutar da ƴan ƙasar 28 da aka yi ƙoƙarin safararsu inda aka kwaso su daga Ivory Coast.

    An kuɓutar da mutanen ne bayan wani samame da aka kai a Abidjan kuma suna taimakawa wajen zurfafa bincike.

    Ma'aikatar harkokin wajen Ghana cikin wata sanarwa ta nuna cewa an kwaɗaitar da mutanen ne da alƙawuran samun damarmakin aiki a Turai sannan an zaƙuli kuɗaɗe masu yawa a hannunsu.

    Ministan harkokin waje Samuel Okudzato Ablakwa, a wani saƙo da ya wallafa a X ya yi kira ga matasan Ghana da su zama masu taka tsan tsan don kaucewa faɗawa hannun miyagu.

    A watan da ya gabata, jami'an shige da fice a Ghana sun kuɓutar da fiye da ƴan ƙasashen yammacin Afirka 300 ciki har da yara fiye da 100 a wani samamen daƙile ayyukan masu safarar mutane a Accra.

  12. Narendra Modi ya nemi ƴan Indiya su taƙaita tafiye-tafiye saboda yaƙin Iran

    Narendra Modi

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Narendra Modi

    Firaiministan Indiya Narendra Modi ya yi kira ga Indiyawa da su farfaɗo da tsarin yin aiki daga gida sannan su rage siyan zinare su kuma taƙaita tafiye-tafiye zuwa ƙasashe don magance tsadar makamashi saboda rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Modi ya ce matakan za su rage yawan man da Indiya ke amfani da shi.

    Masu sharhi sun bayyana kiran da Modi ya yi a wani taro da aka yi a Hyderabad da ke kudancin ƙasar a matsayin mafi tsanani zuwa yanzu.

    Modi ya shawarci mutane da su riƙa amfani da motocin gwamnati tare da kira ga manoma da su rage yin amfani da taki.

  13. Ana fargabar kisan gomman masunta ƴan Najeriya a hare-haren Chadi

    Masunta

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana fargabar an kashe gomman masunta bayan hare-hare ta sama da sojojin Chadi suka kai wuraren mayaƙan Boko Haram a tafkin yankin Chadi, a cewar wani shugaban ƙungiyar masunta.

    Hare-haren sun faru ne kwanaki bayan da Boko Haram ta ƙaddamar da hare-hare biyu kan sansanin sojin Chadi da ke kusa da tafkin, abin da rahotanni ke cewa ya yi sanadin mutuwar aƙalla sojoji 24 da wasu manyan janar-janar biyu.

    A wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumunta, Fadar Shugaban Chadi ta ce sojojinta sun kai hare-hare kan cibiyoyin Boko Haram a Tafkin Chadi a matsayin martani kan hare-haren ranar 4 da 6 ga watan Mayu.

    Shugaban ƙungiyar masunta ƴan Najeriya a yankin, Abubakar Gamandi Usman, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya rutsa da farar hula da dama saboda mayaƙan Boko Haram sun daɗe suna aiwatar da miyagun laifuka a Tafkin Chadi.

    Usman ya ce a lokacin da jirage suka fara shawagi, mayaƙan Boko Haram sun tsere sannan wasu masunta sun tsere a ƙananan jiragen ruwa.

    A cewarsa, an shiga tashin hankali a yayin da mutane ke neman wajen tsira.

    Wannan ba shi ne karon farko ba da ayyukan sojojin Chadi a yankin ke janyo zarge-zargen kisan farar hula.

    A Oktoban 2024, an zargi rundunar sojin Chadi da kashe masunta ƴan Najeriya da dama a wasu hare-hare ta sama da aka kai kan mayaƙan Boko Haram a tsibirin Tilma da ke Tafkin Chadi.

  14. Mutum biyu sun kamu da hantavirus bayan sauka daga jirgin da aka samu ɓarkewar cutar

    Ƙwayar Cutar Hantavirus

    Asalin hoton, Reuters

    Wani Ba'Amurke da ɗan Faransa da suka koma ƙasashensu bayan sauka daga wani jirgin ruwa da aka samu yaɗuwar ƙwayar hantavirus sun kamu da cutar, kamar yadda hukumomi suka shaida.

    Ma'aikatar lafiya ta Amurka ta ce wani Ba'Amurke shi ma ya nuna alamun ya kamu da cutar sai dai alamomin ba su tsananta ba.

    Ministan Lafiya na Faransa Stephanie Rist ta ce akwai wata mata da ke killace a Paris sannan tana fama da rashin lafiya. An kuma gano mutum 22 da suka yi mu'amala da ita.

    A yanzu ana kwashe fiye da fasinjojin jirgin 90.

    Fasinjoji uku da suka shiga jirgin - ma'aurata ƴan Netherlands da wata ƴar Jamus - sun mutu daga baya.

    An tabbatar mutum biyu cikinsu sun kamu da cutar.

    Hantavirus ƙwayoyin cutuka ne da ɓeraye da dangoginsu ke yaɗawa, inda ɗan'adam kan iya ɗaukar cutar ta hanyar shaƙarta a iska daga busasshen ɓurɓushin kashin ɓera.

    Cutar na yaɗuwa ne a lokacin da ƙwayoyinta daga fitsari, kashi ko kuma yawun ɓera suka shiga cikin iska, kamar yadda Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Amurka (CDC) ta bayyana.

  15. An sake tsige mataimakiyar shugaban Phillipine karo na biyu

    Sara Duterte

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sara Duterte

    Majalisar wakilai a Phillipine ta kaɗa ƙuri'ar tsige Mataimakiyar Shugabar ƙasar Sara Duterte karo na biyu, lamarin da ke barazana ga burinta na son tsayawa takara a 2028.

    A yanzu batun ya koma ga majalisar dattijai inda idan aka same da laidi, Sara wadda ƴa ce ga tsohon Shugaban Ƙasa Rodrigo Duterte za ta rasa damar riƙe wani muƙamin gwamnati.

    A yanzu Sara, mai shekara 47 ce kan gaba a ƙuri'ar jin ra'ayina maye gurbin babban abokin adawarta, Shugaba Ferdinand Marcos Jr.

    Batun tsigewar ya taso ne kan zargin mataimakiyar shugaban ƙasar da wadaƙa da kuɗin gwamnati da kuma barazana ga Marcos, da matarsa da ɗan'uwansa wanda tsohon kakakin majalisar ne.

    Kan dalilan ne aka tsige Duterte a 2025 sai dai Kotun Ƙoli ta toshe yunƙurin. Bara ne kuma aka sake ɗago batun.

    A makon jiya ne, wani kwamitin majalisar da ya yi nazari kan shaidun da aka gabatar kan mataimakiar shugaban ƙasar ya yanke cewa akwai gamsassun dalilai na tsige ta.

    Duterte ta ƙi bayyana gaban kwamitin lamarin da ta ce akwai siyasa a ciki.

  16. Gwamnati ta tilasta yi wa ɗaliban sakandare gwajin ƙwaya a Najeriya

    Ministan Ilimi a Najeriya, Dakta Tunji Alausa

    Asalin hoton, @DrTunjiAlausa

    Bayanan hoto, Ministan Ilimi a Najeriya, Dakta Tunji Alausa

    Gwamnatin Najeriya ta bijiro da wasu sabbi kuma tsauraran matakai na yaƙi da ta'ama'li da miyagun ƙwayoyi a makarantun sakandare ciki har da tilasta yi wa ɗalibai gwajin ƙwaya da kuma dakatar da waɗanda aka gano sun ci gaba da shan ƙwaya bayan gyaran halin da aka yi masu.

    A ƙarƙashin sabon tsarin, za a riƙa yi wa duk sabbin ɗalibai a makarantun sakandare gwajin ƙwaya.

    Matakin na ƙunshe cikin wata takarda da ta bayyana wasu jerin matakai da aka ɗauka kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi a makarantun sakandare da ke Najeriya kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    A cewar takardar, an bijiro da tsarin domin samar da yanayi mai kyau na koyarwa da koyo a makarantu ta hanyar rage mummunan tasirin da ta'amali da miyagun ƙwayoyi ke yi kan lafiyar ƙwaƙwalwa da ƙwazon ɗalibai.

  17. Iran ta saki ƴar fafutukar da ta taɓa cin lambar yabo ta Nobel

    Narges Mohammadi

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Narges Mohammadi

    Hukumomin Iran sun saki 'yar fafutukar nan - Narges Mohammadi - wadda ta taɓa cin lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.

    An sake ta ne, a matsayin beli ganin yadda yanayin lafiyarta ke ta taɓarɓarewa.

    A makon da ya wuce magoya bayanta suka yi gargaɗin cewa za ta iya mutuwa a gidan yari, bayan da ta gamu da matsalar bugun zuciya har sau biyu a farkon shekarar nan.

    An mayar da ita daga gidan kaso a Zanjan da ke arewacin Iran ɗin, zuwa babban birnin ƙasar, Tehran, kuma an ƙyale likitocinta su yi mata magani.

    A shekara ta 2023 ne, aka ba ta lambar yabo ta Nobel - bayan an tsare ta a gidan sarƙa a kan fafutukar da take yi ta tabbatar da 'yancin mata da kuma neman a soke hukuncin kisa.

    Ta shafe yawancin lokaci a cikin shekara ashirin da ta gabata - a ciki da wajen gidan yari.

  18. Tinubu ya isa Kenya don halartar taron ƙoli na Afirka da Faransa

    Shugaba Tinubu da Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu

    Asalin hoton, @Dolusegun16

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi.

    Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami'i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare.

    Akwai kuma Ministar harkokin waje ta Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Jakadan Kenya a Najeriya, Amb. Isaac Parashina.

    Taron zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Najeriya na zurfafa alaƙa da kuma haɗin kai da sauran ƙasashen Afirka da kuma Faransa.

    Shugaba Tinubu na samun tarba

    Asalin hoton, @Dolusegun16

    Shugaba Tinubu na gaisawa da jami'an da suka tarbe shi

    Asalin hoton, @Dolusegun16

  19. Shugabannin Afirka na halartar babban taron ciyar da nahiyar gaba a Kenya

    Shugaba Emmanuel Macron da takwaransa William Ruto

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Bayanan hoto, Shugaba Emmanuel Macron da takwaransa William Ruto

    Shugabanni daga sassa daban daban na Afirka na hallara a Kenya domin halartar wani gagarumin taron ƙoli da Faransa haɗin gwiwa da gwamnatin Kenya ke karɓar baƙunci.

    Taron na ciyar da Afirka gaba mai taken Africa Forward zai samu halartar shugabannin ƙasashe kusan 30 daidai lokacin da Paris ke ƙoƙarin inganta alaƙarta da nahiyar bayan koma-bayan da ta fuskanta a yammacin Afirka.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Kenya Wiiliam Ruto ne ke karɓar baƙuncin taron na yini biyu da ya haɗa shugabannin Afirka da masu hannun jari da manyan ƴan kasuwa.

    Taron zai mayar da hankali kan kasuwanci da makamashi mara gurɓata muhalli da fasaha da tsaro.

    Sai dai ana kallon taron a matsayin wata alama ta sauyi a a yadda Faransa ke tafiyar da al'amuranta a Afirka.

    Shi ne babban taro irinsa na farko tsakanin Faransa da ƙasashen Afirka da za a gudanar a ƙasar da ake magana da harshen Turanci.

    Masu sharhi sun ce Faransa na ƙoƙarin sake dasa kanta a matsayi mai kyau a Afirka ta hanyar dogaro kan ƙawancen kasuwanci da zuba jari.

  20. Sojojin Najeriya sun musanta rahoton kisan farar hula a hare-haren Neja

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, JORIS BOLOMEY/AFP via Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe farar hula a wasu jerin hare-hare da aka kai ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

    A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce ta kai hare-hare ta sama kan wuraren ƴanbindiga da ke sassan jihar.

    Kakakin rundunar, Manjo Janar Micheal Onoja ya ce an kai hare-haren ne kan ƙauyukan Katema da Bokko da Kusasu da Kuduru kuma an kai samamen ne bayan bayanan sirri da aka samar.

    Ya kuma yi watsi da rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka yaɗa cewa hare-haren sun shafi farar hula.

    Janar Onoja ya ce saɓanin rahotannin da ak yaɗa, hare-haren sun shafi yankunan ƴanbindiga ne kawai inda kuma aka kashe mayaƙa 70 a Kusasu kaɗai.

    An daɗe ana zargin rundunar sojin Najeriya da kashe farar hula a samamen da take kai wa kan ƙungiyoyin ƴanbindiga da mayaƙa masu iƙirarin Jihadi duk da cewa hukumomin sun sha faɗin cewa mutuwar farar hular abu ne da ba a yi niyya.