Mene ne hukuncin ɗanɗana abinci ga mai azumi?

Azumin Ramadana

Asalin hoton, KHALED DESOUKI

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist (Multimedia)

Azumin Ramadan lokaci ne da al'ummar Musulmi a faɗin duniya ke zage damtse don yin ayyukan da za su inganta imaninsu tare da kyautata wa ƴan uwa da abokan arziki duk domin neman tsira da samun lada.

Ɗaya daga cikin abubuwan kyautatawa da ke ƙara yawan lada a wannan lokaci shi ne ciyarwa kuma bisa al'ada, mata a gidaje sukan yi tanadi don girka abinci iri-iri da nufin faranta ran mai gida da ƴaƴa har ma da abokan arziki.

Sai dai a lokacin dafa abincin buɗa-baki, wasu mata kan yi shakku wajen tabbatar da ko ɗanɗanon girkinsu ya yi daidai, kasancewar yanayin azumi da suke ciki.

BBC ta tuntuɓi Malaman addinin Musulunci don jin hukuncin ɗanɗana abinci a yayin azumi.

Malama Fatima Laminu, wata malamar addinin Musulunci a Abuja, ta ce babu laifi idan aka ɗanɗana abinci matuƙar "mutum ba zai bari yawun ya wuce zuwa maƙogwaronsa ba."

Ta ce sai dai yin hakan na iya zama kuskure idan aka yi da ganganci har abincin ya wuce maƙogwaro, wanda idan hakan ta faru, toh ya zama dole mutum ya rama azumi.

Ta ce hanya mafi sauƙi ga mai azumin da ke son ɗanɗana girki, ita ce ya furzar da duk abin da ya ɗanɗana kafin ya tafi cikin maƙoshi.

Sai dai ta ce an samu saɓani tsakanin malamai game da mai azumin da ya ɗanɗana abinci har ya wuce maƙogwaro, amma ba da saninsa ba.

A cewar Malama Fatima, "wasu malaman sun ce, mutum zai kai azumin sannan kuma ya rama, wasu kuma sun ce tun da kuskure ne, in dai a kan mantuwa ne, ba abin da ya samu azuminsa, wato dai azuminsa yana nan."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ma, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, babban malamin Musulunci a Najeriya ya tabbatar da rashin laifi idan aka ɗanɗana abinci yayin azumi matuƙar ba a haɗiye shi ba.

Ya kafa hujja da fatawar Abdullahi Bn Abbas wanda Sayyid Sabiq ya kawo cikin Littafin Fiqhus Sunnah, Sheikh Albany a cikin Tamamul Minna - Ta'aliƙin da ya yi wa Fiqhus Sunnah cewa Abdullahi Bn Abbas idan ya je kasuwa zai sayi gari, saboda gari akwai mai tsami, akwai sabo akwai tsoho.

Ya ce "Idan ka je kasuwa za ka sayo, dole ka ɗanɗana ka ji sabo ne ko tsoho, to a nan yakan ɗebi garin sai ya fito da harshensa, ya ɗora a kai, ya ɗanɗana ya ji da tsami ko babu tsami, idan ya gama sai ya furzar,"

"Sai malamai suka ginu a kan wannan fatawa cewa tun da da man ana kurkura ruwa, ruwa kuma yana karya azumi amma ba haɗiyewa ake ba, idan an kurkura waje ake yiwowa da shi,"

"Kuma ana yin burushi, idan an yi da makilin, kurkura baki ake yi , idan ka yi asuwaki ma, itace yana da ɗaci ko bauri, sannan yana da ƴan hakukuwa da suke kakkaryewa, dole idan ka gama dai kurkura baki za ka yi ka zubar." in ji Sheikh Daurawa.

Malam Daurawa ya ƙara da cewa abu uku na shiga cikin baki amma kuma ba sa wucewa zuwa maƙogwaro, shi ya sa ba sa karya azumi - su ne ruwan kurkurar baki da makilin ko asuwaki.

A cewarsa, idan aka ginu a kan fatawar Abdullahi Bn Abbas. "don an ɗanɗana abinci a baki kuma an furzar ba a haɗiye ba, wannan bai karya azumi ba".

Malamin ya kuma ba da misali da mata masu girki inda ya ce "idan mace ta yi girki, yamma ta yi, sai kuma ya zama tana son ta ji cewa girkin ya yi?, to tana iya fito da harshenta sai ta ɗanɗana amma fa da sharadin za ta furzar, kada ta haɗiye."