Yadda mai jinin al'ada za ta iya karanta Al-Ƙur'ani da azumi

Mace
    • Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Mata da dama musammam matasansu da kuma waɗanda ba su samu karatun addini mai zurfi ba, kan faɗa cikin taraddadi a irin lokuta na ibada kamar azumi.

Taraddadin yana samun asali ne daga irin hutun da suke samun kansu ciki na al’ada a kowanne wata.

BBC ta tattauna da wani fitaccen malami a Najeriya, Sheik Lawan Abubakar Shu’aib, babban limamin masallacin Sheik Jibril da aka fi sani da Masallacin Triumph a birnin Kano.

Ga kuma bayanansa:

Ramdan

Malamin ya ce; Yarda da barin sallah da sauran ibadu kamar azumi saboda zuwan jinin al’ada shi kan shi ibada ne.

Domin umarni ne na Ubangiji wanda kuma Ya nemi kowacce mace da ta tsinci kanta cikin wannan hali ta yi.

Da a ce mace za ta yi sallah ko azumin a halin da take al’adarta da sai a yi mata hukunci da ta saɓa wa Mahallicinta.

Kasantuwar mace da ta tsinci kanta cikin al’ada, ba ya nufin ta miƙe ƙafafuwanta ba tare da yin ibadun da aka amince mata ta yi domin samun lada ba.

“Malamai da dama sun tafi kan cewa za ta iya karanta AlƘur’ani mai girma, sai dai suna cewa ba za ta ɗauki cikakken Littafin ba.

“Abin da aka amince ko shafi ɗaya ne ta cire gabanin ta fara karatun,” in ji Malam Lawan.

Malan ya ƙara da cewa baya ga karatun Ƙur’ani, mai jinin al’ada za ta iya shiga masallaci ta zauna ko kuma ta ji karatu.

Watan azumi dai lokaci ne na ibada da duk wani Musulmi a fadin duniya ke ƙoƙarin ninka ayyukan da yake yi masu kyau domin dacewa da rahamar da ke cikin watan.