Matsaloli da cututtukan da mata kan fuskanta a lokacin jinin al'ada

Wata mace

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Badariyya Tijjani Kalarawi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

A farkon wannan watan ne kasar Sifaniya ta soma shirin samar da wata doka da za ta bayar da hutu ga mata ma'aikata da ke faɗawa mawuyacin hali lokacin da suke jinin al'ada.

Daftarin dokar ya bayyana cewa za a iya bai wa mace hutun kwana uku a duk wata - kuma ana iya tsawaitawa zuwa kwana biyar a wasu lokuta.

Mene ne jinin al'ada?

Jinin al'ada shi ne fitowar jini daga mahaifar mace, hakan na faruwa ne sakamakon wasu sauye-sauye da mata kan fuskanta a kowanne wata ko kwanakin da ba su kai wata guda ba.

Dakta Zainab Dan-Yaya, likita a Federal Medical Centre a Jabi da ke Abuja babban birnin Najeriya, ta ce jinin na fitowa ne a lokacin da mace ta saki kwan haihuwa, wani yakan zama da idan lokacin daukar ciki ya yi ba kuma tare da mace tana amfani da wani nau'i na kayyade iyali ba.

Jinin al'ada dai wani al'amari ne da ke samun kowacce mace da zarar ta kai shekarun balaga.

Wasu matan kan fara ganin jinin al'ada daga shekaru 12 har zuwa 15, ya danganta da yanayin mace.

Sai dai Dr Zainab ta ce saboda sauyawar yanayi da zamani akan samu yara matan da kan fara jinin al'adar suna da shekara tara.

Ma'ana wasu kan fara da kankantar shekaru sai kuma ya dauke ba zai sake dawowa ba sai kuma bayan wasu shekaru, wasu da zarar sun fara shi ke nan zai ci gaba a haka har zuwa shekarun girma da yake daukewa baki daya tamkar mace ba ta taba yi ba.

Yawan kwanakin jinin al'ada ya kasu kashi daban-daban, wasu kan yi kwana huɗu, wasu mako guda, wasu kan yi har makonni biyu.

To amma da zarar wannan lokaci ya haura, ana bai wa mata shawarar zuwa asibiti domin ganin likita da tabbatar da cewa ba wata matsala ko lalura ce ta samu mace ba.

Wasu matan kan fuskanci matsananciyar rashin lafiya, a lokacin da za su fara jinin a karon farko, wasu kuma kan fuskanci matsanancin ciwo a kowanne wata, ko dai kwanaki biyu gabannin zubar jinin ko kuma idan su na tsaka da yi.

Audugar mata mai tsinke

Asalin hoton, PA Media

Hukumar lafiya ta Birtaniya (NHIS) ta bayyana cewa ciwon mara ga mata lokacin al'ada ba sabon abu ba ne, kuma wani ba abin tayar da hankali ba ne.

To amma da zarar an lura da sauyawarsa daga sassauka ma'ana murdawar mara akai-akai, ko kasala ko rashin jin dadin jiki duka ba abun damuwa ba ne.

Amma da zarar sun tsananta, yana da muhimmanci mace ta je asibiti domin duba lafiyarta. Dr Zainab ta yi bayani kan wasu daga cikin nau'ukan ciwon da mata kan fuskanta a lokacin da suke jinin al'ada.

Kadan daga cikin matsalolin da wasu matan, kan fuskanta a lokacin da suke jinin al'ada:

  • Wasu matan kan fuskanci matsancin ciwon baya, da ya kan janyo musu kasa zama sai kwanciya
  • Sukan fuskanci ciwon gaɓɓai, hakan na saukar da kasala da rashin kuzari
  • Matsanancin ciwon kai, da zazzabi, wasu matan kan haɗa da amai
  • Wasu ma kan yi amai da gudawa, ko kuma gudawar gabanni da lokacin jinin al'ada ko kuma bayan sun kammala
  • Wasu kuma lamarin kan zo musu da yawan bacci, duk inda suka samu sai kwanciya
  • Akwai kuma matsancin ciwon mara da ta ke daurewa da hakan kan sanya mace durkushewa da matsa ciki da mara. Ba raggwantaka ba ce idan mace ta yi kuka a wannan yanayin tsananin ciwon kan haddasa takura
  • Sannan wasu kuma za su dinga shiga yanayi na ƙunci da ɓacin rai ne ba gaira ba dalili, ko jin haushin na kusa da su
  • Wasu kuma tashin zuciya da ɗan kwaɗayi-kwaɗayi suke fama da shi kamar irin na masu ciki.

Wasu matan kan fara ciwon kafin lokacin al'adar, da kuma lokacin da suke yi, wasu kuma sai sun kammala.

Akwai wasu nau'in matan da suke yin ciwon tun kafin su fara da tsakiyarsa har zuwa karshe.

Dakta Zainab ta ce wasu matan na danganta ciwon mara lokacin jinin al'ada da kuma ciwon nakuda, sakamakon yadda ko ina a jikinsu ke amsawa tun daga kugu da baya, da mara da kafa da dukkan gabban jiki.

Wannan layi ne

Shin mece ce alaƙar haihuwa da ciwon mara lokacin jinin al'ada?

Wasu matan kan dangantaka ciwon mara da cewa da zarar sun yi aure, sun dauki ciki da haihuwa komai ya zo karshe.

Ta kara da cewa ciwon na faruwa ne yayin da kwayoyin halittar mace ke sauyawa, dalilin da ya sa sauyin ya ke zuwa nau'i daban-daban.

Dr Zainab ta ce lamarin ba haka yake ba: ''Batun gaskiya shi ne lamarin ba haka ya ke ba, wasu matan idan suka fara wannan ciwon marar sukan danganta shi da ciwon haihuwa.

"Kuma abin damuwar shi ne ko an ba su maganin rage raddin ciwo kamar Boscopan, ko Feldin ko Pracetamol ba lallai ya yi aiki ba.

"Shi ya sa an fi sanya musu allurar rage radadin ciwon a cikin ruwan da ake kara musu ta jijiya."

Bayanan bidiyo, Bidiyo: 'Ina jin kamar na kashe kaina idan ina haila'
Audugar Mata

Asalin hoton, Getty Images

Ita ma hukumar lafiya ta Nirtaniya NHIS, ta ce ciwon kan zo da tsanani, ya danganta da yanayin, wasu yana zuwa da tsananin ciwon mara, yadda za ta dinga murdawa har wasu matan kan kwatanta hakan da matsar da ake yi wa tufafi idan an wanke su za a shanya.

Wasu matan kan fuskanci matsanancin ciwon baya, ko kuma ƙugu.

Wasu kuma su kan yi fama da ciwon ƙafa, ko dai daga gwiwa zuwa dunduniya, ko kuma ƙafafun su yi nauyi.

Wasu kuma kan hada duka ukun, da ciwon mara, da baya da kuma ƙugu.

Sai dai NHIS ta ce, lokacin kan sauya kamar yadda wani jinin al'adar kan sauya, misali daga zuba da yawa zuwa matsakaicin zuba, rage ranaku ko karawa.

To haka lamarin yake ga ciwon mara ga mata lokacin da suke jinin al'adar, ba kuma kowanne wata mace kan fuskanci ciwon ba.

Don haka babu wata alaƙa tsakanin ciwon mara da aure ko haihuwa, ciwo ne da ke zuwa ga mace cikin yanayi da nau'i daban-daban, a iya cewa ya na rikiɗa.

Abubuwan da ke haddasa ciwon mara lokacin jinin al'ada

  • Matsanancin ciwon mara na faruwa ne a lokacin da fatar da ke jikin mahaifar mace ke tsukewa
  • Ciwon yana tasowa ne daga cikin mahaifa, wani ya kan zo da tsanani wani kuma dan kadan kamar dai murdawar ciki
  • A lokacin da mace ke jinin al'ada, bangon mahaifarta na budewa da kuma tsukewa domin taimakawa idan ta fara fitar da kwayaye. Da zarar hakan ta faru jinin kan fara zuba kadan-kadan, wani kuma ta karfinsa yake fita
  • A lokacin da jinin ya fara fita, akwai wata iskar Oxygen da ke tura shi, da zarar wannan iskar ta dauke ko ragu, shi ne mata suke fuskantar wannan matsanancin ciwon
  • Har yanzu bincike bai gano dalilin da ya sanya ciwon yake sauyawa daga mace zuwa wata ba. Sannan kowacce mace da na ta nau'in ciwon.
Wannan layi ne

Tsananin ciwo da ƙunci

Wata matashiya mai suna Aisha, ta shaida min cewa tana fara ciwon ne a ranar da za ta fara ganin jinin al'ada.

"Ina farawa da matsanancin ciwon kafa, kuma ta dama, tun daga tafin kafar har zuwa ƙuguna.

"Na kan ji kamar an dora min dutse a tafin kafata, ga matsanancin ciwon mara, sannan ina jin bacin rai da bakin ciki.

"Na kan ji haushin komai kankantar abin da akai min. Ga wani mahaukacin kwadayi kamar mai shigar ciki, sam ba na son cin abinci sai kayan kwadayi,'' in ji ta.

Wata mace kwance a gado

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu matan kan yi kuka don tsananin ciwon da suke ji

Aisha ta ce, wasu lokutan da ta ji alamun da ta bayyana a farko, ta san ba za a dauki awa daya zuwa biyu ba jinin zai fara zuba.

Amma ciwon na daukewa da zarar jinin ya fara zuba, a wasu lokutan kuma sai an dangana ga asibiti an sanya mata ruwa mai dauke da allurar sinadarin rage radadin ciwo.

Ta kara da cewa; "da zarar na fara jinin da kamar kwana daya zuwa biyu, sai ciwo ya dauke tamkar ban taba yi ba.

"Sai kuma bacci da kwadayi su ce salamu alaikum (dariya) kwadayi kamar mai yaron ciki. Wannan allura da ake sanyawa cikin ruwan drip da ake sanya min ta na taimakawa wajen narkar da jinin da wala'alla ya daskare.

"Sannan na kan samu tawul na sanya shi cikin ruwan zafi tare da gasa marata da shi, wannan ma ya na taimakawa.

"Amma duk yadda za a yi miki bayani kan zafin ciwon mara ba za ki fahimta ba, matukar ba kin taba yi ba.

"An taba sanyawa na samu bangaren tukunyar kasa na sanya shi a garwashin wuta ya yi jajur, sannan na cefa cikin ruwan sanyai na shanye wai duk da sunan maganai.

"Babu abin da ya sauya, kuma babu wani tartibin magani da zan ce ya yi min aiki musamman lokacin da na ke ganiyar 'yan matanci."

Duk da cewa a likitance babu wata alaka tsakanin ciwon mara da haihuwa, Aisha ta ce ita dai da aka yi mata aure ta yi haihuwar fari sai ciwon ya dauke kamar ba ta taba yi ba.

Amma Dr Zainab ta sake nanata cewa babu alaka kan hakan.

Wannan layi ne

Ciwon marar da nau'o'in magungunan ƙayyade iyali ke haddasawa

Hukumar lafiya ta Birtaniya da mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, sun bayyana cewa akwai ciwon mara lokacin jinin al'ada da kan faru sakamakon amfani da wani nau'i na tsarin kayyade iyali da mata kan yi amfani da su, wadannan abubuwa sun hada da;

  • Robar da ake sanyawa mata da ke rufe bakin mahaifa da ake kira IUD, wanda ke hana ƙwan haihuwa shiga cikin mahaifa
  • Wannan nau'i na tsarin kayyade iyali kan zo da matsalolin da suka hada da ciwon mara, zubar jini da sauransu
  • Mace za ta iya banbance ciwon marar da take yi gabanni ko bayan fara amfani da wani nau'in tsarin iyali musamman shan kwayar magani.
  • Misali ciwon kan tsananta a farkon fara amfani da hanyar, ko kuma lokaci zuwa lokaci koma baki dayan lokacin da mace ke amfani da shi
  • Sannan jinin al'adar kan yi wasa, wato sauya lokacin zuwa, ko daukewarsa
  • Zubar jini mai yawa, tsakanin wata zuwa wani
  • Fitar farin ruwa kamar koko, mai kauri. Wani yakan zo da ƙarni ko wari ko yauki, ko haka nan. Ya kan kuma sauya launi daga fari zuwa dorawa-dorawa
  • Fuskantar tsananin zafi, lokacin jima'i.
Wannan layi ne

Matakan da suka kamata mata masu ciwon mara su dauka lokacin jinin al'ada

Talauci kan hana wasu mata samun auduga lokacin jinin al'ada

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Talauci kan hana wasu mata samun auduga lokacin jinin al'ada

Dr Zainab Dan-Yaya ta ce, kamar yadda wasu matan kan fada tabbas amfani da robar nan mai kama da danko da ake zuba mata ruwan zafi tare da dorawa akan marar (hot water bottle), wasu kan yi amfani da tawul su danna mararsu da shi su na samun sauki.

"Sukan ce da zarar sun samu wannan zafin ya hau kan marar, jinin da ya dakare na samun damar narkewa da fita cikin tsanaki. "

Duk da cewa a likitance ba a yi bincike mai zaman kan shi kan hakan ba, amma tun da har suna samun sauki kuma ba hanya ce ta cutarwa ba, za a iya yin hakan sai dai a kaucewa amfani da tafasasshen ruwa saboda zai iya kona fata cikin mace wanda hakan shi ne abin damuwa,'' in ji ta.

Dakta Zainab ta ce a likitance suna bai wa mata shawarar indai su na fuskantar irin wannan ciwon, to su dinga samun isasshen lokaci su na hutawa, da rashin kwaramniya.

Hutu yana da matukar muhimmanci, su yi amfani da maginin da ke rage radadin ciwo wanda likita ko jami'an lafiya suka ba su.

"Ina kara nanatawa hutu ya na da matukar muhimmanci, a lokaci irin haka daga wurin aiki har makaranta ya kamata mace ta samu hutu, saboda ba za ta je wurin aiki ta na kwanciya ko makaranta ba ko kin yin magana," a cewar Dakta Zainab.

Mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, ta ce amfani da magungunan rage radadin ciwo da jami'an lafiya suka bayar da na taimakawa.

  • Shan ƙwayar maganin ibuprofen da aspirin na taimaka rage radadin ciwo. Sai dai idan mace na fama da cutar Asma, ko ciwon ciki, ko ciwon koda, ko hanta bai kamata su sha ibrupfoen da aspirin ba. Kuma duk macen da shekarun ta ba su kai 16 ba, lallai kar ta sha wadannan magungunan
  • Shan maganin farasitamol ya na taimakawa, sai dai binciken da jami'an lafiya suka gudanar sun gano farasitamol baya rage radadin ciwon mara idan aka kwatanta da ibuprofen ko aspirin
  • Idan magungunan rage radadin ciwo ba su yi aiki ba, ya kamata a koma wajen likita domin ba da wani maganin da ya fi wadannan karfi, misali naproxe.
Wannan layi ne

A ranar 12 ga watan Mayu 2022 ne, kafar yada labaran Sifaniya, ta rawaito cewa gwamnati ta fara shirin bai wa mata hutu a lokacin da suke jinin al'ada

Tuni aka rubuta daftarin kudurin dokar, wanda aka kwarmatawa kafafen yada labaran kasar suka.

Kantin saida audugar mata

Asalin hoton, Getty Images

Idan aka amince da shi, Sifaniya za ta zamo ta farko a kasashen turai da suka fara bai wa mata hutu lokacin da suke jinin al'ada.

Daidaikun kasashen duniya ne suke da wannan doka. Kafafen yada labaran da suka ce sun ga daftarin, sun ce hutun ya kama daga kwanaki biyu zuwa uku, kuma nan ba da jimawa ba zai zama doka.

Likitoci a sassa daban-daban na duniya musamman wadanda suka kwari a fannin cutukan da suka shafi mata, sun dade suna kiran a sassautawa mata a wuraren aiki ko makarantu, musamman wadanda sukan yi fama da matsanancin ciwon mara lokacin jinin al'ada.

Wannan layi ne