Jinin haila: Scotland ta fara raba wa mata audugar al'ada kyauta

sanitary products

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Claire Diamond
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Scotland News

Scotland ta zamo ƙasa ta farko a duniya da ta samar da audugar al'ada ta mata kyauta ga kowa.

Ƴan majalisar dokoki sun amince da ƙudurin dokar samar da audugar kyauta a ranar Talata.

A yanzu doka ta sa ya zama wajibi kan dukkan hukumomin ƙasar da su tabbatar da samar da dukkan nau'ukan audugar ga duk mai buƙatar su.

Ƴar majalisa ta jam'iyyar Labour Monica Lennon ce ta gabatar da ƙudurin. Tun a shekarar 2016 take fafutukar ganin an kawo ƙarshen talaucin da ya baibaye mata a wannan fannin.

Ta ce wani ƙudurin doka ne na ci gaba da za a iya aiwatar wa kuma mai muhimmanci sosai saboda annobar cutar korona.

"Al'ada ba ta dakatawa saboda annoba kuma ba a taɓa mayar da hankali kan muhimmancin inganta tare da samar da audugar ba," a cewarta.

Talaucin da ya baibaye mata

A nan ana maganar yanayin da mata kan samu kansu na talauci ta yadda ba sa iya sayen audugar da za su yi amfani da ita lokacin al'ada.

Mata na buƙatar kashe a ƙalla fam takwas kwatankwacin naira 4,000 a Scotland don sayen auduga a duk wata, don tsaftace kansu a tsawon a ƙalla kwana biyar ga mafi yawan mata na al'ada, kuma mata da dama ba sa iya saye.

Yaya girman matsalar?

Young woman shopping for sanitary products

Asalin hoton, Getty Images

Wani bincike da wata ƙungiya Young Scot ta yi a kan fiye da mutum 2,000 ya gano cewa kusan duk mutum ɗaya cikin mutum huɗu da aka tambaya a makaranta ko kwaleji ko jami'a a Scotland na shan wahala sosai wajen samun sayen audugar.

Haka kuma kusan kashi 10 cikin 100 na ƴan mata a Birtaniya ba sa iya sayen audugar; kashi 15 cikin 100 kuwa da ƙyar suke iya saye; kashi 19 cikin 100 sun haƙura suna sayen mai araha sosai, a cewar bincike.

Baya ga magance matsalar talaucin sayen auduga a tsakanin mata, ƙudurin dokar zai kuma magance matsalar nuna ƙyama ga masu haila. Masu bincike sun ce wannan matsala ce da ta shafi ƴan mata.

An gano cewa kashi 71 cikin 100 na ƴan mata da ke tsakanin shekaru 17 zuwa 21 suna jin kunya sosai wajen sayen auduga.

Sannan tasirin da hakan ke yi kan ilimi shi ma wani ɓangare ne da dokar ke son magancewa - bayan da masu bincike suka gano cewa kusan rabin ƴan matan da aka yi hira da su suka ce su kan shafe kwanaki ba sa zuwa makaranta saboda haila.

Wane tasiri dokar za ta yi?

Dokar ta Period Products (Free Provision) (Scotland) Bill ta sanya wajibci kan dukkan hukumomin ƙasar da su tabbatar duk mai son sayen audugar haila ya same ta kyauta.

Yanzu ya rage wa yankunan ƙasar 32 da su tsara yadda za a tabbatar da cewa kowa ya samu, amma dai "ya zama wajibi a bai wa duk mai buƙata" damar samun duk nau'in audugar da yake so "cikin sauƙi da mutuntawa."

Condoms

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana bayar da kwaroron roba kyauta a Scotland

Wasu bayanai na tuntuɓa sun bayar da shawarar gyara tsarin a kan wani tsari na lafiya da ake da shi inda ake raba kwaroron roba kyauta.

Alal misali, a Hukumar Lafiya ta yankin Greater Glasgow da kuma Clyde, duk wani mai buƙatar kwaroron roba kyauta kan tambaya ne a wuraren da suka haɗa da asibitoci da kantunan sayar da magani da kwalejoji da jami'o'i - ko kuma su cike wani kati ta yadda ba sai sun tambaya da baki ba.

Me ake yi don magance talaucin sayen auduga tsakanin mata?

A yanzu haka dai ana bayar da audugar mata a makarantu da kwaleji da jami'o'i kyauta a Scotland.

Gwamnatin Soctland ta samar da kuɗi fam miliyan 5.2 don tallafar shirin, inda aka ware fam 500,000 ga gidauniyar FareShare don ta samar da audugar kyauta ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.

An sake ware fam miliyan huɗu ga yankunan ƙasar don samar da audugar a wuraren taron mutane, da kuma fam 50,000 don samar da ita ga ƙungiyoyin wasanni.

A wasu wuraren da suka haɗa da kantunan cin abinci tuni aka tanadar wa mutane audugar kyauta.

A ina kuma ake yin irin haka?

Gwamnatin Birtaniya tana da nata kwamitin na magance matsalar talaucin sayen auduga a tsakanin mata, da nufin magance ƙyama da ke shafar ilimi ga masu al'ada.

Tana kuma son inganta hanyoyin samar da audugar kyauta.

A watan Janairu ne aka ƙaddamar da shirin samar da audugar a makarantun firamare da na sakandare a Ingila.

Sannan wasu jihohin Amurka kaɗan ma sun gabatar da ƙudurin dokokin samar da audugar al'ada kyauta a makarantu.

sanitary products

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, A wasu wuraren da suka haɗa da kantunan cin abinci tuni aka tanadar wa mutane audugar kyauta