Akwai aibi idan mutum ya nutsu a watan Ramadana?

- Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Duk da cewa watan Ramadan watan tuba ne da ƙara azama wajen ayyukan alkhairi waɗanda ake yi da waɗanda ma ba a yi a baya, a wajen mutane da dama akwai alamar tambaya ga waɗanda ke nutsuwa a cikin watan domin amfana daga alfarmar da take cikinsa.
Akwai tambayoyi da dama da mutane ke yi game da abubuwan da suka shafi watan Ramadan, don haka BBC ta ɓullo da wani shiri na amsa tambayoyinku, ta hanyar tuntuɓar masana domin jin amsoshinsu.
A wannan karon BBC ta tuntuɓi Malam Ibrahim Kabir wanda aka fi sani da Malam Ibrahim Mai Ashafa da ke birnin Kano domin jin ko akwai wani aibi ga wanda ya nutsu a lokacin wata mai tsarki?.
Malam Ibrahim ya ce ainihi shi watan Ramadan wata ne da Allah yake shela ga masu aikin alkhairi su ninka, waɗanda suka boye sharri a zukatansu kuma su hakura saboda alfarmar watan.

"Idan watan Ramadana ya taho mai kira daga fadar Allah yana kira, yana cewa ya kai ma'abocin alkhairi, yi gaggawar ci gaba da yin alkhairin.
"Ya kai mai neman yin sharri ka kame ka daina yi, watan Ramadana yazo, kamar yadda fiyayyen halitta ya bayyana," in ji Malam Ibrahim.
Shi wannan watan da aka saukar da kur'ani a cikinsa shiriya ce ga mutane, don haka yana da wuya kaga cikakken musulmi da yake aikata abubuwa marasa kyau a wajen wata, kuma watan yazo bai sauya ba ko kaɗan, in ji Malam.
Babu laifi ga mutum idan ya sauya a wannan wata domin dukkan watan, watan shiriya ne.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dama abin da ubangiji yake nema a wajen bawansa a wannan wata, idan bawan yana aikata abubuwan da ba su dace ba, ya ce ya tuba ya daina abin da yake saboda ya samu albarkacin wannan wata mai tsarki.
"Babu yadda za a yi hakan ya zama aibi domin ana zaton idan Ramadana ya wuce zai iya komawa, ai dama shi ɗan adam mai laifi ne. Kuma shi yasa ubangiji ya buɗe ƙofar tuba".
Abin da ba a so shi ne mutum ya ƙudurce cewa shi da azumi ya ƙare zai ci gaba da aikata abubuwan da yake na laifi da ya dakatar domin watan.
"Shugaban halitta wata rana yana hawa mimbari sai sahabbai suka ji ya ce "Amin" sau ɗaya suka ji ya ƙara har sai da aka yi sau uku. Da suka tambaye shi dalilinsa na cewa "Amin" sai ya ce, Mala'ika Jibrilu ne ya yi addu'a kan wanda azumi ya zo har ya fita bai yi abin arziƙi ba idan Allah ya shigar da shi wuta kada ya fito da shi, Shugaba ya ce Ameen.
"Kaga wannan addu'ar ai ba ƙarama ba ce, don haka in mutum ya faɗa cikinta ya halaka," in ji Malam Mai Ashafa.
End of Wasu labaran da za ku so karantawa
Idan mutum ya koma kan laifukan da yake bayan azumi ibadarsa ba ta karɓu ba kenan?
Shi rashin aikata laifi 'ma'asumanci' na annabawa ne, dan mutum ya yi azumi baya nufin ai ba zai ƙara yin laifi ba.
"Dalilin da ya sa aka ce mu riƙa yin istigifari shi ne domin an san mu masu laifi ne," kamar yadda Malam ya bayyana.
Malam ya ce kwata-kwata bai taɓa jin wannan fatawar ba da ake cewa 'alamar an karɓi azumin mutum shi ne ya bar ayyukan da yake yi na laifi, in kuma ya koma musu hakan na nufin ibadarsa ba ta karɓu ba'.
Magana guda da take ta gaskiya shi ne, babu koma baya ga duk mutumin da ya zage dantse ko ya bar ayyukan assha sabo da zuwan Ramadana.
Annabi Muhammad mai kyauta ne, amma idan azumi ya zo kyautarsa na ninkawa sama da yadda aka saba ganin wajen Ramadana, in ji Malam Ibrahim Kabir.
Dan haka kowa ya sake zage dantsensa domin yin ayyukan alkhairi a wannan wata mai albarka.
Kada kalaman abokanka ko ƙawayenki su karya maku gwiwa wajen daina abubuwan da kike yi ko kake yi gabanin azumi, shiriya ta Allah ce, mai yiwuwa bayan azumi mutum ya ɗore kan kyawawan halayansa na gari.










