Yadda 'sakacin likitoci' ke jefa rayuwar mutane cikin haɗari a asibitocin Najeriya

Abubakar Muhammad

Asalin hoton, Abubakar Muhammad

    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Aiko rahoto daga, Abuja
    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

A Najeriya an sha samun raɗe-raɗi da zarge-zargen cewa sakacin likitoci da sauran ma'aikatan asibiti a Najeriya na jefa mutane da dama cikin haɗari a ƙasar, inda a wasu lokuta ake rasa rayuka.

A kwana-kwanan nan, fitacciyar marubuciya, Chimamand Ngozi Adichie ta rasa ɗaya daga tagwayen jariranta mai wata 21 a duniya, inda ta yi zargin mutuwarsa na da alaƙa da sakacin likitoci.

Bayan zargin, ma'aikatar lafiyar ƙasar ta tabbatar "ƙalubale da ma'aikatan jinya ke fuskanta" sannan ta sanar da kafa kwamitin kar-ta-kwana domin "tabbatar da kula da marasa lafiya da bin tsare-tsare masu inganci a asibitoci."

Iyalan marubuciyar sun ce jaririnta, Nkanu Nnamdi ya rasu ne a makon jiya a wani asibiti mai zaman kansa a Legas bayan fama da jinya na ɗan lokaci.

Sun yi zargin cewa ba a saka wa jaririn na'urar ƙara numfashi ba wato oxygen a lokacin da ya dace, sannan an tula masa maganin barci, lamarin da suka ce ya jawo zuciyarsa ta buga.

Sai dai asibitin ya miƙa "jajensa," amma ya nanata cewa ma'aikatansa ba su yi wani kuskure ba, inda asibitin ya nanata cewa suna aiki ne da tsare-tsaren da suka yi daidai da na kiwon lafiya na duniya.

Tuni gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin a gaggauta bincike bayan karaɗe shafukan sada zumunta da labarin ya yi.

Ana cikin batun ne kuma aka samu labarin mutuwar wata mai suna Aisha Umar, mahaifiyar yara biyar da ta rasu bayan zargin likitoci sun manta da almakashin da aka yi mata tiyata a cikin cikinta.

Ƴan'uwanta sun ce an mata tiyatar ne a wani asibiti a Kano, "amma bayan tiyatar sai ta riƙa fama da zafi da raɗaɗi a cikinta, amma sai aka riƙa ba ta maganin rage raɗaɗi," in ji ƙanin mijinta, Abubakar Mohammed a zantawarsa da BBC.

"Da aka yi hoton cikin ne sai aka ga akwai almakashi a cikinta da likitoci suka manta da shi," in ji shi, inda suka yi zargin akwai sakacin likitoci.

Tuni gwamnatin Kano ta dakatar da "ma'aikatan asibiti guda uku da suka yi aikin, sannan ta buƙaci a gudanar da bincike tare da alƙawarin ɗaukar mataki."

Ƴan'uwan Aisha Umar sun yi zargin akwai sakacin likitoci

Asalin hoton, Abubakar Mohammed

Bayanan hoto, Ƴan'uwan Aisha Umar sun yi zargin akwai sakacin likitoci
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Waɗannan matsalolin guda biyu manya sun sake dawo da maganar zargin likitoci da sauran ma'aikatan asibiti da sakacin da ke jefa rayuwar mutane cikin haɗari.

Wata mai suna Josephine Obi mai shekara 29 ta ce mahaifinta ya rasu a 2021 a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas, lamarin da ta yi zargin likitoci ne suka yi kuskure wajen yi masa tiyatar belu.

Ta ce daga baya babban likitan ya ba su haƙuri, inda a cewarsa ya nanata cewa sun yi kuskure.

Ta ce iyalanta ba su shigar da ƙara ba ne domin tsoron ɗaukar lokaci mai tsawo ana shari'a, "sannan za a kashe kuɗi sosai, kawai sai muka haƙura," in ji Obi.

BBC ta tura wa asibitin saƙon neman bahasi ta imel, amma asibitin bai amsa ba. BBC ta kuma kira lambobin wayar da aka rubuta a shafin intanet na asibitin, amma ba sa shiga.

A jihar Kano, wani ma'aikacin gidan yari na cigaba da jimamin matarsa, Ummu Kulthum Tukur, wadda ta rasu tana da shekara 27 bayan ta haifa tagwaye a asibitin Aminu Kano.

Ya ce da a ce an yi mata tiyata da sauri, da wataƙila ta sha.

"Ta ɗauki sama da awa 24 tana naƙuda, inda ta zubar da jini sosai kafin ta rasu," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa har yanzu asibitin bai bayar da takardar rasuwarta.

BBC ta yi yunƙurin neman ƙarin bayani daga asibitin, amma hakan bai samu ba, inda mai magana da yawun asibitin Hauwa Inuwa ta shaida wa BBC cewa tana hutu.

Sai dai ta turo lambar wata wadda ta ce abokiyar aikinta ce, amma lambar ba ta shiga.

Shi ma Joe Abah, tsohon shugaban hukumar yi wa aikin gwamnati gyare-gyare ya yi rubutu a kafar X, inda a ciki ya yi iƙirarin cewa wani asibiti a Abuja ya dage sai an masa tiyata saboda wata jinya.

Ya ce da ya je wani asibiti a ƙasar waje, sai aka ce masa ba ya buƙatar tiyata.

A nata bayanin, Dr Fatima Gaya da ke aiki a wani asibiti mai zaman kansa a Kano, ta ce, "asibitocin kuɗi sun fi kula da marasa lafiya idan aka kwatanta da asibitocin gwamnati, amma sai dai suna da tsada, inda marasa ƙarfi ba sa iya biya."

Ƴan Najeriya sun fi zuwa asibitin gwamnati saboda sauƙi

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Ƴan Najeriya sun fi zuwa asibitin gwamnati saboda sauƙi

A nasa jawabin, shugaban likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya Dr Mohammad Usman Suleiman ya bayyana wa BBC cewa bai kamata a riƙa ɗaura laifi kan ɗaiɗaikun mutane.

"A Najeriya, ana nuna wa ɗaiɗaikun mutane ne yatsa, maimakon a bayyana matsalolin da ɓangare ke fuskanta baki ɗaya domin a lalubo hanyoyin magance su," in ji Suleiman a zantawarsa da BBC.

A wasu ƙididdiga guda biyu daban-daban da NOIPolls da mujallar African Research Journal of Medical Sciences suka yi, sun gano cewa kusan kashi 43 na ƴan Najeriya sun taɓa fuskantar kuskuren ma'aikatan jinya.

Sai dai ma'aikatan jinya da masu sharhi kan al'amuran lafiya sun ce likitocin ƙasar na shan wahala saboda yawan adidin marasa lafiya da likitocin ƙasar ke dubawa.

Ƙungiyar likitocin Najeriya NMA ta ce kusan likitocin ƙasar guda 15,000 ne suka bar ƙasar a cikin shekara biyar da suka gabata.

Da yake sanar da kwamitin kar-ta-kwana na lafiya a Najeriya, ministan lafiyar ƙasar Muhammad Ali Pate ya tabbatar da cewa "ɓangaren lafiya a ƙasar na fama da matsaloli."

Kwamitin zai yi aiki wajen sa ido da bibiya domin tabbatar da ana ba marasa lafiya kula da suke buƙata a ƙasar baki ɗaya.

Ya ce kwamitin zai yi aiki na wata 12 da farko, kafin a duba yiwuwar tawaita aikinsa.