Matata ta yi fama da mummunan ciwon ciki kafin rasuwarta - Mijin matar da aka 'manta almakashi' a cikinta

Asalin hoton, Abubakar Muhammad
Aishatu Umar, wata ƴar Najeriya, ta rasa ranta bayan zargin barin almakashi a cikinta lokacin da aka yi mata tiyata a wani asibiti da ke Kano, a arewacin Najeriya, kamar yadda mijinta ya shaida wa BBC.
Bayanai sun ce matar, mai ƴaƴa biyar ta rasu ne ranar Lahadi yayin da likitoci ke shirye-shiryen sake yi mata tiyata domin ciro almakashin da ke cikinta, wanda aka ce an manta sa'ilin tiyatar da aka yi mata a baya.
Abubakar Mohammed, wanda shi ne mijin marigayiyar ya shaida wa BBC cewa matar ta kwashe watanni tana fama da mummunan ciwon ciki bayan tiyatar da aka yi mata a wani asibiti a cikin watan Satumban 2025.
Mohammed ya ce ta kwashe kimanin wata huɗu tana fama da raɗaɗi kafin daga baya suka ziyarci asibitin Aminu Kano inda aka yi mata gwaje-gwaje da hoto, kwanaki kadan kafin rasuwarta.
Sakamakon likitoci ya nuna cewa an bar wani abu daga cikin kayan tiyata a cikinta a lokacin da aka yi mata aikin fiɗa a watan Satumba.
"An yi mata tiyata ne a asibiti cikin watan Satumba. Daga nan ne ta fara kokawa kan ciwon ciki mai tsanani na tsawon watanni," in ji Mohammed.
"Amma kwana biyu da suka wuce sai ciwon cikin ya yi tsanani, ba za ta iya jurewa ba, sai muka yanke shawarar zuwa asibitin Mallam Aminu Kano inda aka yi mata hoton ciki, daga nan ne likitoci suka gane cewa akwai almakashi a cikinta."

Asalin hoton, Abubakar Muhammad
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A baya tana ta fama da ciwon cikin amma tana jurewa har sai zuwa ranar Juma'a, lokacin da ciwon ya yi tsanani, har ya kasance abin ya yi yawa, daga nan muka garzaya da ita asibiti cikin hanzari."
Ya ce matar ta rasu kafin a fara tiyata domin cire almakashin.
"Daga nan sai aka hanzarta domin a yi mata tiyata a cire, amma sai ta rasu. Tun kafina a fara aikin ta rasu. Sun shiga da ita ɗakin tiyata kenan sai ta rasu," in ji Mohammed.
Ya bayyana matarsa a matsayin mace ta gari wadda kowane namiji zai so ya samu.
"Mace ta gara, kuma duk wanda ya yi hulɗa da ita ya san hakan. Babban abin da zan yi kewa game da ita shi ne mace ce mai kirki, tana da kula, kuma mace ce mai tausayi da kowane mutum zai so ya samu," in ji shi.
Mohammed ya ce ya yi amannar inda an ɗauki matakan da suka dace da ƙila bai rasa matarsa ba.
"Na yi imanin cewa in da ta samu kulawa da kyau, da yanzu tana raye. Shi ya sa nake kira ga gwamnati ta gyara ɓangaren lafiya, ta yadda za a kauce wa faruwar irin haka a kan wani a nan gaba."

Asalin hoton, Abubakar Muhammad
Yanzu haka gwamnatin Kano ta haramta wa mutane ake da ake zargi da hannu kai-tsaye a lamarin duk wani aiki da ya shafi kula da lafiya.
Matakin na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano, Samira Sueiman ta fitar a ranar Talata.
Haka nan hukumar ta miƙa batun ga kwamitin tabbatar da bin ƙa'idojin aikin kula da lafiya na jihar Kano domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin hukunci daidai da tsarin doka.
"Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano na miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar tare da taya su alhinin rashin. Muna tabbatar wa al'umma cewa ba za a amince da sakaci ba, ta kowace hanya," in ji sanarwar.
"Hukumar na son sanar da al'umma cewa bayan binciken da shugaban hukumar Mansur Mudi ya bayar da umarnin yi, an gano cewa lamarin da ya shafi batun Aishatu Umar ya faru ne a cibiyar lafiya ta Abubakar Imam Urology Centre."
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta dakatar da mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin.
"Bisa ga ƙudurinmu na tabbatar da adalci da ƙwarewa da kuma kiyaye marasa lafiya, hukumar ta dakatar da mutane uku da ke da hannu kai-tsaye a lamarin daga duk wani aiki da ya jiɓanci kiwon lafiya, nan take."







