Yadda aka tilasta min shan ruwan wankan gawar mijina

Asalin hoton, Imo State/ Facebook
A wani ƙauye da ake kira Awo-Omamma a ƙaramar hukumar Oru a jihar Imo da ke Najeriya, muhawara ta kaure bayan wasu iyalai sun tursasa wa wata mata kwankwaɗar ruwan da aka wanke gawar mijinta.
Chika Ndubuisi ta shiga cikin wannan yanayi ne bayan mutuwar maigidan nata.
Iyalin mijinta sun tsare ta, inda suka zarge ta da kisan kai, sannan suka tursasa mata shan ruwan da aka wanke gawar domin tabbatar da cewa ba ta da hannu a mutuwar mijin nata.
Lamarin ya kai ga gwamnatin jihar ta tura wakilai daga ma'aikatar mata ta jihar domin zuwa su ceto matar.
Me gwamnatin Jihar Imo ta ce?
Gwamnatin jihar Imo ta bakin kwamishinar mata da ci gaban al'umma, Nkechinyere Ugwu ta yi tir da lamarin bayan samun nasarar ceto matar daga hannun iyalin mijinta.
A cikin wata takardar sanarwa, ma'aikatar ta bayyana abin da iyalin mijin suka yi wa Chika a matsayin zalunci kuma abin takaici.
"Wannan babban al'amari ne. Ya saɓa wa doka kuma abu ne da ba za a lamunta ba," kamar yadda sanarwar gwamnatin ta bayyana.
Ka za a ɗauki mataki kan lamarin?
Kwamishinar mata ta Imo Nkechinyere Ugwu ta ce nan ba da jimawa ba waɗanda suka aikata wannan abu a kan Chika za su gane cewa doka tana aiki, in ji sanarwar da ta fitar.
Ta ce "mutanen za su gurfana a kotu domin bayar da bahasi kan abin da suka aikata."
Sannan ta ƙara da cewa gwamnatin jihar a shirye take ta kare hakki da mutuncin mata a jihar.
Wane hali Chika Ndubuisi take ciki?
Ma'aikatar mata ta jihar Imo ta tabbatar da cewa an kwantar da Chika Ndubuisi a asibiti domin duba lafiyarta bayan faruwar lamarin.
Haka nan ma'aikatar ta sanar da cewa matar na a wani wuri da za a ƙarfafa mara gwiwa, da duba lafiyar tunaninta da lafiyarta tare da ba ta shawarwari.
Kuma hukumomin sun sanar cewa jami'an ƴansanda sun fara gudanar da bincike a kan abin da ya faru.
Ko akwai dokar da ta hana irin haka?
Wata sananniyar lauya a jihar Enugu da ke Najeriya, Nnenna Anozie ta ce waɗanda suka tursasa da kuma wadanda suka taimaka wajen tilasta wa Chika Ndubuisi shan ruwan da aka wanke gawar mijinta sun aikata abin da ya saɓa wa doka.
Anozie ta yi ƙarin bayani kan cewa dokar hana cin zarafin mutane ta Najeriya )VAPP) ta tanadin hukunci ga wadanda aka kama da irin wannan laifi.
Ta ƙara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi bayani kan haramcin yin danniya ga wani ɓangare na al'umma.
Ta ƙara da cewa a halin da ake ciki "za a iya ɗaure waɗanda suka aikata wannan laifi na tsawon shekara biyar a gidan yari ko kuma a tilasta musu biyan tara".
Dokar hana cin zarafi ta Najeriya
Nnenna Anozie ta an samar da dokar haramta cin zarafin al'umma ta Najeriya ne a shekara ta 2015 a lokacin mulkin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
"Wannan doka ta haramta duk wani cin zarafi a kan mata, ciki har da cin zarafi mai nasaba da al'ada."
"Tilasta wa mace ta sha ruwan da aka wanke gawa na daga cikin abubuwan da doka ta ta haramta idan aka duba da kyau, domin za ka ga cewa ruwan ba ya da tsafta kuma yana cike da sanadarai masu cutarwa waɗanda za su iya kashe mutum.
"A sani cewa dokar haramta cin zarafi ta ƙunshi hana faruwar laifuka kamar duka, hana wa mutum abinci, hana mutum hanyar sufuri ko yin fyaɗe, da dai sauran su."
Anozie ta ƙara da cewa dukkanin gwamnatocin jihohin arewa maso gabashin Najeriya sun sanya hannu kan dokar hana cin zarafi.
Ta ƙara bayani kan cewa jihar Anambra ta amince da dokar a shekara ta 2017, Enugu kuma a 2019, Imo a 2021, Ebonyi a 2021 yayin da Abia ta amince da dokar a shekarar 2020.










