Yadda aka ƙona uwargida da amarya a gidan aurensu a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce tana binciken domin gano waɗanda ake zargi da hallaka wasu matan aure - uwargida da amarya - ta hanyar cinna musu wuta a ɗakunan aurensu.
Lamarin ya auku ne ranar Alhamis da rana, lokacin da maigidan baya nan kuma babu zirga-zirgar mutane a unguwar.
Al'amrin ya faru ne a unguwar Tudun Yola cikin ƙaramar hukumar Gwale da ke tsakiyar birnin na Kano.
CSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, inda ya ce ba zai faɗaɗa bayani ba, "don kada a samu matsala a binciken" da suke yi.
Kakakin ƴansandan ya ce jami'ansu sun gano wasu wayoyin hannu guda biyu - da suke tsammanin na waɗanda suka aikata laifin ne.
CSP Kiyawa ya ƙara da cewa sun kuma fahimci cewa maharan sun jikkata uwargidan kafin su banka mata wuta.
Yadda abin ya faru
Wani makusancin magidancin ya shaida wa BBC cewa maharan sun haura gidan ne tun kafin dare ya yi, amma ba a fahimci hakan ba.
Anas Sha'aibu, ɗaya daga cikin ƴaƴan maigidan ne, ya shaida wa BBC cewa yana gida da daddare, mahaifinsa ya kira shi tare da sanar da shi cewa ya gaggauta zuwa gidansa saboda an yi gobara.
''Bayan zuwanmu kuma sai muka tarar da wani abu daban, domin kuwa mun tarar da ɗaya daga cikin matan nasa na ci da wuta, ɗayar kuma ta kulle kanta a ban-ɗaki'', in ji shi.
Ya ce sun ta ƙoƙari domin ganin sun buɗe ƙofar, sai daga baya suka samu nasarar ɓalle sakatar ban-ɗakin.
''Bayan ɓalle sakatar sai muka tarar da gawarta, ita ma ta mutu, abin da muka fahimta shi ne ita ma an kunna wuta a tabarma, tare da tura wutar ta ƙofofin fitar da iskar ban ɗaki'', a cewarsa.
'Tun 12:30 na rana suka shiga gidan'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Anas ya ƙara da cewa akwai makwabcinsu da yake da kyamarar tsaro ta CCTV, kuma da suka bincika an lura cewa lokacin da maharan suka isa kofar gidan babu mutane.
''Daga abin da muka gani a kyamarar, mutanen sun zo ƙofar gidan ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana, kuma tun daga lokacin suke cikin gidan'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa babu wanda ya fahimci mutanen suna cikin gidan har sai bayan sallar magariba.
''Bayan sallar Magariba, ɗaya daga cikin yaran gidan ya dawo, amma sai ya tarar da ƙofar gidan a kulle ta ciki, ya yi ta bugu domin a buɗe masa, amma babu wanda ya buɗe masa''.
Ya ce da yaron ya ga haka, sai ya kira wayoyin iyayen nasa, amma babu wadda ta ɗauka, daga nan sai ya kira maigidan domin sanar da shi halin da ake ciki.
''Sai maigidan ya ce masa ai kuwa suna nan babu inda suka je domin ba su sanar da shi za su je wani wuri ba, nan take sai mahaifin namu ya garzayo gida, inda kuma ya tarar da wannan iftila'i'', a cewar Anas.
'Har kan gadon ɗayansu aka watsa fetur'

Asalin hoton, Getty Images
Anas ya ce da farko sun yi zaton gobara ce ta auku, amma da suka duba sosai sai suka fahimci da gangan aka kunna wutar.
''Sai da muka duba sosai, sai muka fahimci cewa babban falonsu babu abin da ya same shi''.
''Mun kuma ga jarkar fetur, sannan muka tarar da injin janaretonsu an tuntsurar da shi tare da tsiyaya fetur'', in ji Anas.
Ya ƙara da cewa bayan da suka shiga gidan sun tarar an cinna wuta a kan kujerar ɗaya daga cikin matan.
'Ɗayar kuma har cikin ɗakinta aka watsa fetur, domin kuwa har a kan gadonta duka fetur ɗin ne'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa duka gadon matar sun tarar da shi a ƙone, sakamakon wutar da aka kunna wa ɗakin nata.










