Yadda ake zargin amarya ta yi wa angonta yankan rago a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Rundanar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wata amarya da ake zargi da halaka angonta a ranar Talata.
Cikin wata sanarwa, rundunar ta ce tana zargin amaryar mai suna Saudat Jibril 'yar shekara 18 ta halaka angonta Salisu Idris mai shekara 30 ne ta hanyar yi masa yankan rago da wata wuƙa mai kaifi.
Mai magana da yawun rundunar ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Farawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a arewa maso yammacin Najeriya.
"Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:35 na dare a ranar 6 ga watan Mayun da muke ciki, inda wadda ake zargi wato amryar ta yanka mijin nata da wata wuƙa mai kaifi", in ji SP Kiyawa.
Lamarin ya harzuƙa mazauna Kano da arewacin Najeriya, musamman a shafukan sada zumunta, inda mutane ke bayyana alhini.
Hotuna da bidiyo sun nuna wani dandazon mutane da ya taru a kusa da gidan ma'auratan a safiyar Talata domin neman ƙarin bayani game da abin da ya faru.
Hotunan ma'auratan sun yi ta waɗari a shafukan zumunta, kuma bayanai sun nuna cewa kwana 10 kenan da ɗaura auren nasu.
"Muna tsare da ita a sahshen bincken manyan laifuka, inda muke tuhumarta da zargin aikata kisa, wanda da zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da ita a gaban kotu kan zargin kisan kai," a cewar SP Kiyawa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce jami'ansu ne suka kai angon asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda likitoci tabbatar da mutuwarsa.
Babu wani cikakken bayani game da abin da ya jawo rikici tsakanin ma'auratan, amma mahaifiyar Salisu ta faɗa wa wata kafar yaɗa labarai a Kano cewa auren zumunci suka yi.
"Ni da mahaifiyar yaron ubanmu ɗaya. Auren zumunci ne kuma Allah ne ya haɗa su," kamar yadda matar mai suna Binta ta bayyana.
"Shi ne da kansa ya gan ta ya ce yana so bayan wata ta da farko ta ce ba ta son sa. Da na tambaye shi yana son ta ba wani ne ya tilasta masa ba, ya ce min shi ne yake son ta."
Mahaifi da mahaifiyar angon sun faɗa wa 'yanjarida cewa sun yafe wa wadda ake zargin kuma ba za su yi shari'a da ita ba.
Lamarin na zuwa ne kwana ɗaya bayan rudunar yansandan ta Kano ta sanar da mutuwar wani matashi mai suna Shehu Muhammad mai shekara 30 da wasu ƴan fashi suka halaka ta hanyar sara da adda a gidansa da ke unguwar Ɗanbare a jihar.
Sai dai ta ce ta kama ɗaya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Aliyu Umar da ta same shi a wurin da aka yi kisan. Sannan ta samu makamin da aka yi amfani da shi wajen sassara matashin a wajensa.











