Yadda wata ƴar Rasha ke yaudarar samari daga ƙasashen waje suna shiga yaƙin Rasha a Ukraine

Polina Azarnykh.

Asalin hoton, Telegram

Bayanan hoto, Azarnykh tana yawan saka hotonta da waɗanda ta ɗauka aiki, ciki har da ƙungiyar Syria da Umar ya yi balaguro da ita
    • Marubuci, Nawal Al-Maghafi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior international investigations correspondent
    • Marubuci, Sheida Kiran
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wuta na ci a gefen fasfo ɗin Omar. "Wutar na ci sosai," kamar yadda wata mata da ba a gani da kyau ke faɗa a cikin yaren Rasha a wani bidiyo.

Omar ɗan shekara 26 ɗan asalin Syria, ya kasance a fagen daga na aƙalla watanni tara a yaƙin Rasha da Ukraine, kafin bidiyon ya kai ga wayarsa.

Ya san muryar matar. Sunanta Poina Alexandrovna Azarnykh, wadda ya ce ta taimaka masa wajen saka hannu don yi wa Rasha yaƙi, inda aka yi masa alkawarin aiki mai gwaɓi da samun shaidar zama ɗan Rasha. Amma a yanzu tana cikin fushi.

A cikin jerin sakonnin murya daga Ukraine, Omar wanda ke magana kan halin da yake ciki, ya kwatanta yadda ya maƙale da kuma shiga fargaba a filin daga.

Ya ce Azarnykh ta yi masa alkawarin cewa idan ya biya dala 3,000, za ta taimaka masa wajen ganin bai shiga yaƙi dumu-dumu ba. Sai dai, ya ce an aika shi fagen yaƙi cikin kwanaki goma bayan samun horo, don haka ya ki biyan kuɗin inda ita kuma ta mayar da martani ta hanyar ƙona masa fasfo.

Ya ce ya yi ƙoƙarin nuna turjiya na ƙin shiga yaƙi, sai dai kwamandojinsa sun yi barazanar kashewa ko kuma tura shi gidan yari.

"An yaudare mu... wannan mata babbar maƙaryaciya ce," in ji Omar.

Polina Azarnykh.

Asalin hoton, Telegram

Bayanan hoto, Azarnykh tana yawan wallafa hotunan bidiyo inda take ƙarfafa wa mutane shiga aikin soji a Rasha

Sashen binciken kwakwaf na BBC Eye ya bi diddigin Azarnykh, mai shekara 40 da ta kasance tsohuwar malama, wadda ke amfani da shafin Telegram wajen yaudarar matasa daga ƙasashe matalauta, don zuwa aikin soji a Rasha.

Matar tana faɗa a cikin bidiyoyinta tare da murmushi cewa za a bai wa mutum kwantiragin aikin soji na shekara ɗaya idan ya je Rasha.

BBC ta gano mutum 500 waɗanda ta sama musu takardu, wanda yana a matsayin takardar gayyata da zai bai wa mutum damar shiga Rasha aikin soja. Mutanen sun fito ne - yawanci daga Siriya, Masar da kuma Yemen - waɗanda da alama sun tura mata bayanan fasfo ɗin su domin su samu aikin.

Sai dai waɗanda aka ɗauka aikin sojin da kuma iyalansu sun faɗa wa BBC cewa ta yadauri mutanen cewa ba za su shiga yaƙi ba, da kuma gaza barin ƙasar bayan shekara ɗaya har da barazana ga waɗanda suka kalubalance ta. Ta musanta zarge-zargen lokacin da BBC ta tuntuɓe ta.

Iyalai 12 daga ciki sun faɗa mana yadda wasu matasa da ta ɗauka aikin sojin suka mutu ko kuma suka ɓata.

Sojojin Rasha da aka kashe.

Asalin hoton, ANDREY BORODULIN/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Rasha na rasa dubban sojioji a kowane wata a yaƙin Ukraine
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rasha ta faɗaɗa batun shiga aikin soja na dole, da ɗaukar fursunoni da kuma ƙara kuɗaɗen alawus da take bayar wa don ƙarfafa ayyukanta a Ukraine, duk da irin sojojin ƙasar da ke mutuwa.

An kashe ko kuma jikkata sama da sojojin ƙasar miliyan ɗaya tun fara mamaya kan Ukraine a shekara ta 2022, inda aka kashe soji 25,000 a watan Disamban 2025 kaɗai, a cewar Nato.

Binciken da sashen Rasha na BBC ya yi, wanda kuma ya dogara kan mutanen da suka mutu da alkaluman hukumomi na mace-mace, ya nuna cewa Rasha ta rasa sojoji a Ukraine a shekara da ta gabata fiye da kowane lokaci.

Yana da wahala a iya gano yawan ƴan ƙasashen waje da suka shiga aikin soji a Rasha. Binciken BBC kan ƴan ƙasashen waje da aka kashe da kuma aka jikkata - ya nuna cewa aƙalla sojoji 20,000 ne suka sanya hannu na shiga aikin sojin, ciki har da mutanen da suka fito daga ƙasashen Cuba, Nepal da kuma Koriya ta Arewa.

Ita ma Ukraine ta rasa sojoji da dama, ta kuma ɗauki ƴan ƙasashen waje aikin sojin.

'Gawarwaki a warwatse'

Omar ya fara haɗuwa da Azarnykh ne lokacin da kuɗaɗensa suka kare a filin jirgin sama na Moscow a watan Maris ɗin 2024, tare da wasu ƴan Siriya 14.

Aikin yi ya yi ƙaranci a Siriya, ga kuma rashin biya mai kyau. Omar ya ce wani ya yi musu alkawarin aikin gadi a cibiyoyin mai na Rasha. Hakan ya sa suka tashi zuwa Moscow, sai dai abin mamaki yaudararsu aka yi.

Sun haɗu da Azarnykh ne lokacin da suke neman aikin yi ta intanet, inda daga nan suka aika mata sako.

Ta same su a filin jirgin saman bayan sa'o'i kaɗan, inda suka shiga jirgin ƙasa zuwa cibiyar ɗaukar aiki a Bryansk da ke arewacin Rasha, in ji Omar.

A can ne, ta ce za a ba su aiki na shekara ɗaya a cikin rundunar sojin ƙasar, inda za a riƙa biyansu albashin da ya kai dala 2,500 da kuma alawus ɗin saka hannu na dala 5,000 - kuɗaɗen da sai dai su yi mafarkinsu a Siriya.

Omar ya ce an ba su aikin da rubuce-rubuce cikin yaren Rasha, wanda abu ne da dukkansu ba su fahimta ba - ta karɓi fasfo ɗinsu gaba-ɗaya tare da alkawarin samar musu shaidar zama ƴan Rasha. Ta kuma yi alkawarin cewa ba za su shiga yaƙi ba idan kowannensu ya biya dala 3,000 daga cikin kuɗin saka hannu da za a ba su," a cewar Omar.

Hari.

Asalin hoton, Roman Chop/Global Images Ukraine via Getty Images

Bayanan hoto, Omar ya kwatanta yadda suka shiga cikin tsananin yaƙi da kuma ganin tashin bama-bamai a fagen daga

Sai dai, ya ce ƙasa da wata ɗaya, ya tsinci kansa a fagen daga, kwanaki goma da samun horo, ga kuma ba shi da ƙwarewar aikin soji.

"Za mu iya mutuwa babu makawa," kamar yadda ya faɗa cikin ɗaya daga cikin jerin sakonnin murya da ya aika wa tawagar binciken BBC.

"Babu abin da kake gani sai wahala, fashe-fashe da kuma ruwan alburusai. Idan ba ka mutu daga abubuwan fashewa ba, za ka mutu daga ɓaraguzai da ke faɗi a kanka," kamar yadda ya faɗa a 2024.

"Gawarwaki kawai kake iya gani ko'ina.....na taka gawarwaki, Allah ka yafe min," in ji Omar.

"Idan mutum ya mutu, suna saka shi cikin buhu sannan su jefa shi ƙasan wata bishiya, na ga hakan da idona," in ji shi.

Bayan kusan shekara ɗaya, ya gano abin da ya ce Azarnykh ta kasa bayyana musu - wata doka da Rasha ta ɓullo da ita a 2022, an bayyana cewa ana iya ƙara wa soja kwantiragi har sai an kammala yaƙi.

"Idan suka ƙara min kwantiragi, na mutu kawai - wayyo Allah na," in ji shi.

Sai dai, ya yi rashin sa'a, domin kuwa an tsawaita masa kwantiragi.

'Daga Jami'a zuwa aikin soji'

Shafin Telegram na Azarnykh yana da mabiya 21,000. Tana yawan faɗa wa mabiyanta cewa duk wanda ke son shiga aikin soja a Rasha ya aika mata fasfo ɗinsa. Daga nan ta kuma wallafa takardun gayyata, wasu lokuta da sunayen waɗanda aka gayyata.

BBC ta gano takardun gayyata kusan 490 waɗanda ta tura a tsawon shekara da ta gabata ga mutane daga ƙasashen Yemen, Siriya, Masar, Moroko, Iraqi, Ivory Coast da kuma Najeriya.

Polina Azarnykh.

Asalin hoton, Telegram

Bayanan hoto, "Dukkanku kun gane cewa za ku tafi zuwa yaƙi... ba abin da ake yi a kyauta," a cewar Azarnykh a cikin wani bidiyo a 2024

Mun tattauna da mutum takwas ƴan ƙasashen waje da aka ɗauka aikin soji, ciki har da Omar wanda ta ɗauka aiki, da kuma iyalan mutum 12 waɗanda suka mutu ko kuma suka ɓata.

Yawancinsu sun bayyana cewa Azarnykh ta yaudari ƴan uwansu. Sun faɗa mana cewa mazan sun san cewa aikin soji za su shiga, sai dai ba su ɗauka cewa za a tura su fagen daga ba. Da yawansu, kamar Omar, suna jin cewa ba su da isasshen ƙwarewa ko kuma sun ɗauka cewa za a sallame su bayan shekara ɗaya.

A Masar, Yousef - wanda shi ma muka sauya sunansu - ya faɗa wa BBC cewa ɗan uwansa, Mohammed ya fara karatun jami'a a birnin Yekaterinburg na Rasha a 2022.

Sai dai ya fuskanci matsala wajen biyan kuɗin makaranta, a cewar Yousef, inda ya faɗa wa ƴan uwansa cewa wata mata ƴar Rasha mai suna Polina ta fara neman taimaka masa ta intanet, ciki har da tayin shiga aikin soji wanda yake ganin idan ya shiga zai ba shi damar ci gaba da karatunsa.

"Ta yi min alkawarin gida da kuma shaidar ɗan ƙasa... kuɗaɗen alawus kowane wata," in ji shi. "Nan take aka aika shi Ukraine. Ya tsinci kansa a cikin yaƙi," a cewar Yousef.

Magana ta karshe da muka yi da shi shi ne ranar 24 ga watan Janairun 2024, in ji Yousef. Ya ce bayan shekara ɗaya, sun samu sako da shafin Telegram da lambar Rasha, wanda ke ɗauke da hotunan gawar Mohammed. A lokacin ne ƴan uwansa suka gano cewa an kashe shi tsawon shekara ɗaya.