'Yadda kan iyakar Najeriya da Nijar da Benin ta zama cibiyar ƴanbindiga'

Ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Wani sabon binciken ƙungiyar da ke kula da alƙaluman wuraren da ak gudanar da rikice-rikici ta ACLED ya nuna cewa kan iayakar Najeriya da Benin da kuma Jamahuriyar Nijar na neman zama wata sabuwar cibiyar rikice-rikice a 2025.

Cikin wani sabon rahoto da ƙungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu gagarumar ƙaruwar hare-hare a yankin cikin shekarar da ta gabata.

Ko a cikin makon nan ma sau biyu Lakurawa suna ƙaddamar da hare-hare a jihar Kebbi tare da kashe gomman mutane.

ACLED ta ce rikice-rikicen sun shafi ƙungiyoyin JNIM mai biyayya ga ƙungiyar Al-qaeda da EIS mai biyayya ga ISIS, waɗanda suke da alhakin kashi 86 na ƙaruwar hare-haren idan aka aka kwantata da 2024.

''Haka ma an samu ƙaruwar kashe-kashe da kashi 262 cikin 100'', in ji ACLED.

Daga ina ƙungiyoyin suka fito?

mayaka

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar JNIM da EIS - waɗanda suka jima suna ƙaddamar da hare-hare a ƙasashen yankin Sahel, irin su Mali da Burkina Faso da Nijar - a yanzu sun fara bazuwa zuwa ƙasashen Yammacin Afirka da ke gaɓar teku.

ACLED ta ce an samu ƙaruwar hare-hare a garuruwan Alibori and Borgou da ke kudancin Benin, da yankin Dosso a Jamhuriyar Nijar, da kuma jihohin Kebbi da Sokoto da Neja da Kwara a Najeriya.

Munanan hare-haren masu ikirarin jihadi daga Nijar da Burkina Fasso suka kai wa sojoji a shekarar da ta gabata ya sanya shekarar zama ''shekarar da aka fi samun kashe-kashe'' a Benin, kamar yadda rahoton binciken ƙungiyar ya nuna.

A Nijar, ƙungiyoyin JNIM da EIS sun ƙaddamar da hare-hare masu yawa ciki har da wanda suka kai wa babban filin jirgin ƙasar da ke wajen birnin Yamai a watan Janairun da ya gabata.

'Kokawar neman iko'

Dr Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankinn Sahel ya ce su waɗanan ƙungiyoyi guda biyu JNIM da kuma IES na kokawar neman iko ne a wannan yanki.

''Bayanai na nuna cewa su waɗannan ƙungiyoyin guda biyu gasa suke yi wajen neman ikon mallakar wanna yanki na ƙan iyakar ƙasashen nan uku'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa dalilin da ya sa kowace daga cikin waɗannan ƙungiyoyi ke zafafaf kai hare-hare shi ne fatan kafa daula a wannan yanki.

''Akwai garuruwa a waɗannan ƙasashen uku da waɗannan ƙungiyoyi ke gudanar da harkokinsu na walwala ba tare da wata fargaba daga hukumomi ba'', in ji masanin tsaron.

Me ya sa aka samu ƙaruwar hare-haren?

ɗanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Heni Nsaibia, babban mai sharhi kan al'amuran tsaron Afirka ta Yamma ya ce a shekarar da ta gabata ne JNIM ya ɗauki alhakin harin farko a Najeriya.

Sai dai ya ɗora alhakin karuwar hare-haren kan rashin haɗin kai da ke tsakanin ƙasashen yankin musamman bayan da Mali da Burkina Faso da Nijar suka fice daga ƙungiyar Ecowas.

Ya ƙara da cewa babban dajin da ya ratsa kan iyakokin ƙasashen uku ya taimaka wajen ƙaruwar ayyukan masu ɗauke da makaman a kan iyakar.

Binciken na kamfanin Acled ya kuma gano cewa masu iƙirarin jihadin na ƙarfafa kansu a yankin ta hanyar ɗaukar sabbin mayhaƙa daga ƙabilu daban-daban da ke yankin, kamar ƴanbindiga masu fashin daji.

Haka ma binciken ya ƙungiyoyin ne ke iko da hanyoyin safarar kayyaki, musamman man fetur daga arewacin Najeriya zuwa kogin Nijar da Benin.

Me ya sa ƴanbindigar ke mamaye yankin?

Dokta Kabiru Adamu ya ce ƙungiyoyin sun zaɓi zama a yankin ne saboda yana da yanayin da irin waɗannan ƙungiyoyi ke so.

''Na farko yanki ne mai dazuka masu duhu da mayaƙan ƙungiyoyin ke amfani da su wajen ɓoyewa da gudanar da al'amuransu'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai kuma matsalar tattalin arziki na irin waɗannan yankuna, wanda yana taimaka wa ƴanbindigar damar ci gaba da harkokinsu ba tare da sanya idanun gwamnati.

''Sannan suna amfani da matsalolin da mazauna yankunan ke da su, na rashin sanya su cikin al'amuran gwamnati, wato gwamnati ba ta taimaka musu, ta yadda ƴanbindigar ke jan ra'ayinsu cikin sauki'', in ji masanain tsaron.

Mece ce makomar yankin?

Dr Kabiru Adamu ya ce matsawar gwamnati ba ta yi da gaske ba, to makomar wannan yanki na cikin hatsari.

''Idan aka yi la'akari da ƙaruwar hare-haren da ake samu a wannan yanki, to a iya cewa gwamnatocin ƙasashen uku na dab da rasa iko da wannan yanki, kuma hakan zai kasance abu mai hatsari,'' in ji shi.

Ya ce wannan abu ne da aka sha gani a wasu ƙasashen irin Afghanistan da Syria da sauran ƙasashen da ke fama da ƙungiyoyin masi iƙirarin jihadi.

Me gwamnatocin uku za su yi don kawar da ƙungiyoyin?

Dr Kabiru Adamu ya ce yana da kyau gwamntocin ƙasashen uku su haɗa kai domin yaƙar wannan barazana da ke tunkararsu.

''Su tashi tsaye, wajen ƙarfafa tsaron kan iyakar, musamman gwamnatoicin jihohin yankin su ya kamata su fara,ba sai sun jira gwamnatin tarayya ba'', in ji shi.

Sannan ya ce yana da kyau gwamnati ta ƙarfafa tsaro a dazukan wannan yanki, ta yadda ƴanbindigar ba za su samu damar gudanar da ayyukansu ba.

Haka ma ya ce yana da kyau inganta tattalin arzikin mazauna waɗannan yankuna ta yadda bab u wanda zai zo ya yaudare su.

''A inganta asibitocinsu da makarantunsu da walwalarsa ta yadda ba wanda zai zo ya ja ra'ayinsu da wani abu'', in ji Shugaban kamfanin Beacon Security.

Daga ƙarshe ya ce yana da kyau ƙungiyar ECOWAS ta mayar da hankali wajen kakkaɓe wannan matsala da ke neman samun wurin zama a wannan yanki.