Yadda mutum miliyan 55 ke fuskantar barazanar yunwa a yammacin Afrika

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan miliyan 55 ne ke fuskantar barazanar yunwa a kasashen yammacin Afirka da ke fama da tashe tashen hankula.
Rahoton hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu daga cikinsu musamman a arewacin Najeriya za su fada cikin bala'in yunwa.
Fadace-fadacen da ake fama da shi a yankin shi ke haddasa matsalar yunwar da ake fama da ita da kuma janye tallafin da kungiyoyin agaji ke ba wa yankin a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Hukumar Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ta ce dole aka rage tallafin da ya ke kai wa yankin saboda karancin kudaden tafiyar da shirin.
A yammaci da kuma tsakiyar Afirka, mutane miliyan 55 za su fuskanci karancin abinci a tsakanin watannin Yuni da Augustan 2026, in ji wani jami'i nahukumar Jean-Martin Bauer.
Adadin mutanen da ke cikin bukatar agajin gaggawa ya rubanya tun daga 2020, inda ya kai miliyan uku, in ji jami'in.
Kazalika Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 15 a yankunan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ke cikin yanayi na bala'in yunwa.
Jami'in Majalisar Dinkin Duniyar, ya ce dalili shi ne jihar na fama da hare-haren masu ikirarin jihadi wanda suka fara kai hare hare tun a 2009.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yakin da sojojin Najeriya ke yi da mayaka masu da'awar jihadin ya yi sanadin rasa rayukan mutum fiye da dubu 40 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu.
Mr Bauer, ya ce a damunar da ta gabata a yamamcin Afirka an samu damuna mai albarka wato kayan amfanin gona sun samu tagomashi.
Matsalar karancin abinci a yankunan kasashen Afirka, ta kara tsananta ne saboda rage tallafin da gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi, bayan da ya umarci kungiyoyin agajin Amurka da su rage tallafin da suke ba kasashen mabukata.
Mr Bauer ya ce a 2025, hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da samar da tallafi ga kusan yara a dubu 300 a Najeriya, saboda dakatar da tallafin Amurka, inda a Kamaru ta dakatar da ayyukanta ga mutane dubu 500 saboda rashin isassun kudade.
A watan Fabrairun 2026, Hukumar Samar da abincin na shirin samar da tallafi ga mutum dubu 72, inda a irin watan a 2025 ta samar da tallafi ga mutane kusan miliyan daya da dubu 300.
Mr Bauer, ya ce." Katse bayar da tallafin shi ne ya kara ta'azzara halin yunwar da ake ciki a kasashen Afirka."
Ya ce, nan da watanni shida masu zuwa hukumarsu na bukatar dala miliyan 453 domin gudanar da ayyukanta a yankunan Afirka.
Ya ce," Idan har ba a samu kudade ba to abin da za a gani a gaba sai ya fi wanda ake gani a yanzu."











