Wane ne Abba Atiku, ɗan jagoran adawar Najeriya da ya koma APC?

Atiku da Abba Atiku

Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Alhamis ne Abubakar Atiku Abubakar (Abba) ya sanar da matakinsa na komawa jam'iyyar APC da kuma shan alƙawarin goyon bayan Bola Tinubu a zaɓen 2027, bayan ficewa daga jam'iyyar PDP, wadda a ƙarƙashinta ne mahaifinsa Atiku Aubakar ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Hakan ya zo wa al'umma da dama da mamaki ganin adawar da ke tsakanin mahaifin Abba, wato Atiku Abubakar da shugaban ƙasa mai ci Bola Tinubu.

Abba Atiku ya sanar da matakin nasa ne a wata ziyara da ya kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Barau Jibril.

A lokacin jawabin nasa, Abba Atiku ya ce ya koma APC ne saboda salon shugabanci da jajircewa na mataimakin shugaban majalisar dattawan.

''Don haka zan yi aiki da Sanata Barau domin tabbatar da nasarar sake zaɓen Tinubu a karo na biyu'', in ji Abba Atiku kamar yadda Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na X.

Wane ne Abba Atiku?

Abba Atiku

Asalin hoton, Social Media

Cikakken sunansa shi ne Abubakar Atiku Abubakar, wanda ake yi wa laƙabi da Abba Atiku.

Abdulrashid Shehu, ɗaya daga cikin masu magana da yawun Atikun ya ce Abba ɗaya ne daga cikin manyan ƴaƴan jagoran adawar ƙasar.

''Shi ne ɗansa na huɗu, kuma shekarunsa sun kai aƙalla 47'', in ji shi.

Bayanai sun nuna cewa Abba Atiku na ɗaya daga cikin matasan da ke kan gaba a gwagwarmaya siyasar mahaifin nasa.

A shekarar 2022, ya kafa wata ƙungiya mai suna Haske Atiku Oraganisation domin tallafa wa yaƙin neman zaɓen mahaifin nasa.

Me Atiku ya ce?

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

Jagoran adawar Najeriyar - wanda a yanzu ke jam'iyyar ADC - ya ce matakin ɗan nasa na ƙashin-kai ne, kuma yana da damar bin ra'ayinsa.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, jim kaɗan bayan matakin Abban, Atiku ya ce wannan ba abin mamaki ba ne a tsarin dimokuraɗiyya.

''A matsayina na ɗan dimokuraɗiyya, ba zan tilasta wa ƴaƴana kan abin da suke da ra'ayi ba, kamar yadda ba zan tilasta wa kowane ɗan Najeriya ba'', in ji shi.

Haka kuma Abdurrashid Shehu Sharaɗa ya ce a shekarun Abba Atiku ya wuce a yi masa dole, yana da damar bin tsarin da yake so a duk lokacin da yake so.

Ya ƙara da cewa abin da yake gabansa a yanzu shi ne ceto Najeriya ta hanyar karɓe mulki daga APC, ba komawar ɗan Atiku APC ba.

Gazawa ce ga Atiku?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu na kallon matakin lamarin a matsayin tazgaro ga Atiku Abubakar, idan har jam'iyyar APC mai mulki za ta yi zawarcin ɗansa ta kuma yi nasara.

Sai dai Dokta Ibrahim Baba Shatambaya, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa na Jami'an Usmanu Danfodiyo dake Sokoto, ya ce wannan ba gazawa ba ce fagen siyasa.

Ya ce duk da cewa wannan ba abu ne da aka saba gani a siyasar Najeriya ba, amma a fagen dimokuraɗiyya wannan gagarumin ci gaba ne.

''Wannan wata manuniya ce cewa ta wani ɓangaren tafiyar dimokuraɗiyyarmu muna samun ci gaba'', in ji shi.

''Dama ba zai yiwu ba a ce idan kana tafiyar siyasa dole abokanka da danginka da duka ƴan garinku sai sun shiga jam'iyyar da kake ba, wannan ba dimokuraɗiyya ba ne'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a tsarin dimokraɗiyya kowa na da ƴancin yin jam'iyyar da yake so.

''Bambancin ra'ayi shi ke nuna karfin dimokuraɗiyya a tsakanin ƙasashe'', in ji Dokta Shatambaya.

A nasa ɓangare shi ma Abdurrashid Sharaɗa ya ce sam wannan ba gazawa ba ce, ra'ayi ne, kuma hakan yana ƙara tabbatar wa ƴan Najeriya cewa Atiku mutum ne da ke girmamma ra'ayi.

''Hakan ya nuna cewa Atiku mutum ne da zai bai wa kowa damar bayyana yancinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar'', in ji shi.

Wane tasiri komawarsa APC zai yi?

Kashim da Tinubu

Asalin hoton, Kashim Shettima/X

Dokta Shatambaya ya ce ɗaya daga cikin tasirin da Abba Atiku zai yi shi ne kasancewarsa ɗaya daga cikin ƴaƴan ciki na jagoran adawar a jam'iyya mai mulki.

''Ya kasance ɗa na ciki ga jagoran adawar ƙasar - wanda ya yi takara mai ƙarfi da shugaba mai ci, wannan ci gaba ne ga ita jam'iyyar mai mulki'', in ji shi.

Cikin jawabin da ya yi bayan sanar da matakinsa na komawa APC, Amma Atiku ya ce ya buƙacii jagororin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Atiku da yake jagoranta da su bi shi jam'iyyar APC tare da mara wa Tinubu baya.

Wani abu da wasu ke ganin zai yi tasiri ga ita jam'iyyar APC mai mulkin.

Sai dai Abdurrashid Shehu Sharaɗa ya ce babu wani giɓin da hakan zai yi wa tafiyar Atiku.

Ya ƙara da cewa ba wata rawa da Abba ya taka a baya a tafiyar siyasar mahaifin nasa.

''Bana tunanin akwai damuwa game da ficewar tasa, siyasa ce kuma muna yi masa fatan alkairi'', in ji shi.