Lokacin bayyana takarata a zaɓen 2027 bai yi ba - Atiku
Tsohon mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar hamayya ta PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce ba zai iya bayyana ko zai yi takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓen 2027.
Yayin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Atiku ya ce yanzu kafa jam'iyyar ADC ta haɗakar 'yan adawa ce a gabansa.
"Wannan kuma sai lokacin ya zo tukunna, yanzu abin da muka saka a gaba shi ne kafa jam'iyyar ta samu karɓuwa ƙwarai da gaske," in ji Atiku bayan an tambaye shi kan ko zai yi takara.
Mai shekara 78 ɗin wanda ya yi mataimakin shugaban Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007, Atiku ya kuma bayana dalilin da ya sa ya fice daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Atiku Abubakar ya shafe kusan shekara 40 a fagen siyasar Najeriya, inda ya fara neman takarar shugaban ƙasa tun daga shekarar 1993 a jam'iyar SDP.
Ya yi takarar gwamnan jihar Adamawa a shekarar 1990, ya sake yi a 1996 duka ba tare da nasara ba, inda daga baya ya samu nasara a 1998.
Sai dai kafin a rantsar da shi ne kuma tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin abokin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP a 1999.
'Ba zan yi siyasar raba ƙafa ba'

A watan Yulin da ya gabata ne Atiku ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP, wadda ya yi wa takarar shugaban ƙasa sau biyu, yana mai cewa ta "sauka daga kan manufar da aka kafa ta".
Sai dai PDP wadda ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, ta mayar da martani, inda ta haƙiƙance cewa ficewarsa ba za ta haifarmata da wani giɓi ba.
Wasu 'yansiyasar da suka koma PDP tare da shi sun bayyana cewa za su raba ƙafa ne tsakanin PDP da kuma ADC ɗin, kamar yadda Ministan Abuja Nyesom Wike yake a PDP kuma yake cikin gwamnatin Tinubu ta APC.
Da aka tambye shi cewa akwai zargin shi ma zai raba ƙafa, Amma Atiku ya ce ba zai yi hakan ba.
"A'a, ni ba a san ni da haka ba," yana mai girgiza kai. "Idan na ce haka, to haka zan tafi," kamar yadda ya bayyana yana mai nuni da hannunsa cewa mutum ne mai alƙibla ɗaya.
Sauya sheƙarsa daga PDP wani babban sauyi ne a tarihin siyasarsa na ƙoƙarin cimma burinsa na zama shugaban Najeriya.
Ya ce saɓanin ra'ayi ne ya tilasta masa ficewa daga jam'iyyar PDP, tare da zargin cewa " jam'iyyar APC mai mulki ce ta yi ruwa ta yi tsaki ta mamaye PDP."
Taimaka wa matasa
Ya zuwa 2023, karo uku kenan Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasa, kodayake ya shiga zaben fitar da gwani sau uku.
Sai dai a duka takarar da ya yi bai taɓa samun nasara ba.
Yayin hira da BBC, Atiku ya ce zai iya haƙura da takarar shugaban kasa a zaben 2027 domin mara wa matashi baya - amma bisa sharaɗi.
"Idan na tsaya takara, matashi ya kayar da ni, shikenan sai na karɓa," in ji shi.
Ya kuma ce zai ba shi cikakken goyon baya tare da horar da shi dabarun siyasa.
"Jam'iyyar da muka shiga yanzu matasa da mata ne muka sa a gaba," a cewar Atiku Abubakar.












