Abu 10 da ke karya azumi

Asalin hoton, Getty Images
Akwai abubuwa da dama da mutane ke tunanin ba sa karya azumi amma kuma bisa haƙiƙa suna karya azumin. Haka kuma akwai abubuwan da jama'a ke tunanin suna karya azumi amma kuma ba sa karyawa.
Ganin yadda ake ci gaba da tattaunawa kan abubuwan da suke iya karya da waɗanda ba sa karyawa ne ya sa muka rairayo waɗannan abubuwa.
Wannan ya sa BBC ta tuntuɓi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, malamin addinin Musulunci a Kano domin jin abubuwan da suke karya azumi.
Shehun malamin ya kuma lissafa abubuwa guda 10 tare da yin bayani ta fuskar bambancinsu dangane da kaffara ko ramuwa.
Jerin abu 10 da ke karya azumi
Sheikh Daurawa ya ce abin da ake kira azumi dama shi ne kamewa daga ci da sha da mu'amalar aure da duk abubuwan da ke karya azumi tun daga ketowar alfijir zuwa zuwa faɗuwar rana.
Ya ce abubuwan da suke karya su ne:
- Cin abinci da gangan
- Shan ruwa da gangan
- Saduwa da iyali
- Ƙaƙaro amai
- Zuwan jinin al'ada ko biƙi
- Rashin ɗauko niyyar azumin
- Yin ƙaho
- Fasa azumin
- Ridda
- Fitar da maniyyi
Bayani kan fitar maniyyi
Sheikh Aminu Daurawa ya yi ƙarin bayani game da fitar maniyyi, inda ya ce akwai abubuwa huɗu ko biyar da ke jawo maniyyi ya fito kamar haka:
- Sumbata
- Rumguma
- Kallo
- Tunani
A cewar shehin malamin, idan maniyyi ya fito a dalilin kowanne daga cikinsu, azumi ya karye.
Ramuwa ko Kaffara?
Malamin ya ce abubuwan da suke karya azumi sun kasu kashi biyu, inda ya ce akwai waɗanda ramawa da kaffara za a yi, akwai kuma waɗanda ramawa kawai za a yi.
Ya ce wanda ya ci abinci ko ya sha abin sha da gangan ya san yana azumin, domin ci da sha kala biyar ne a musulunci, kamar yadda ya lissafo su
- Ganganci
- Mantuwa
- Jahilci
- Tilastawa
- Kuskure
Ya ce wanda ya ci ko ya sha da gangan ne zai yi kaffara, sannan ya yi ramuwa.
"Wannan shi ne abin da Imamu Malik ya tafi a kai. Amma wanda aka yi ittafaƙi cewa za a yi kaffara da ramuwa shi ne saduwa da iyali da gangan. Wannan duk wanda ya yi dole zai yi ramuwa kuma ya yi kaffara," kamar yadda Sheikh Daurawa ya bayyana.











