Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 01 ga watan Satumbar 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Diginza

  1. An kai wa wasu tankokin dakon man Saudiyya hari a mashigar Hormuz

    A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda muka ruwaito, an kai hare-hare kan aƙalla tankokin ɗanyen mai biyu a mashigar Hormuz ta hanyar harba wasu makamai da ba a gano ko su waye suka harba su ba.

    Yanzu an fitar da ƙarin bayani game da lamarin.

    A cewar Reuters, manyan tankokin ɗanyen mai guda biyu da ke ɗauke da man fetur na Saudiyya sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da ba a san ko wa ya harba su ba, a tazarar mintuna kaɗan da juna, yayin da suke wucewa ta mashigin Hormuz a daren ranar Litinin. Kamfanonin tattara bayanan zirga-zirgar jiragen ruwa, Marisax da Kepler, ne suka bayar da wannan bayani.

    A cikin wata sanarwa da Marisax ta fitar, ta ce: "Wadannan hare-hare da suka faru kusan a lokaci guda suna nuna ƙarin tsananta yanayin barazanar tsaro a yankin mashigar Oman."

    Bayanan Kepler sun nuna cewa tankokin biyu sun ɗora gangar ɗanyen mai miliyan biyu na Saudiyya daga tashar Juaima, da ke kudancin gabar Tekun Fasha, a makon da ya gabata.

    Kamfanin mai na Saudiyya, Saudi Aramco, ya koma ɗora da sayar da mai ta mashigin Hormuz ne a watan Agusta da ya gabata, bayan ya dakatar da wasu ayyuka a yankin a baya.

  2. Isra'ila ta ce ta kama wani babban jami'in Hamas a Gaza

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Tsaron Isra'ila ya sanar da cewa an kama wani babban jami'in ƙungiyar Hamas a Gaza.

    Israel Katz ya bayyana hakan ne bayan rahotanni sun bayyana game da wasu hare-hare da dakarun musamman na Isra'ila da kuma wata ƙungiyar Falasɗinawa da ke samun goyon bayan Isra'ila suka gudanar a birnin Gaza.

    A cewar ma'aikatan agaji na yankin, hare-haren sama na Isra'ila sun kashe aƙalla yara biyu da wata mata.

    Sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa sun kai hare-hare kan wurare da dama a Gaza domin, a cewarsu, "kawar da barazanar tsaro," kuma sun ce babu wani soja nasu da ya ji rauni a waɗannan hare-haren.

    Ministan Tsaron Isra'ilar bai bayyana sunan kwamandan Hamas ɗin da aka kama ba, ko kuma yadda aka yi kamen nasa.

    Bayan wata ganawa da mazauna yankin Netiv HaAsara, wanda ke kusa da arewacin Gaza, Mista Katz ya jaddada cewa ayyukan sojojin Isra'ila a yankin na ci gaba ba tare da tangarda ba.

  3. Amurka ta ci gaba da kai hare-hare kan Iran

    Cibiyar da ke kula da ayyukan sojin Amurka ta sanar da ci gaba da kai hare-hare kan wuraren dakarun Rundunar Juyin juya halin Iran.

    Cibiyar Amurkan da ke yankin ta ce waɗannan hare-haren martani ne ga ga hare-haren da Rundunar Juyin juya halin Iran ta kai kan wasu jiragen ruwan kasuwanci a yankin Hormuz da kuma dakarun Amurka da aka girke a yankin.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ya rawaito cewa an ji fashear wasu abubuwa a yankunan Konarak, Chabahar, Bandar Abbas, Sirik, da kuma Qeshm.

    Sai dai a cewer kamfanin dillancin labaran har yanzu Rundunar Juyin juya halin ba ta bayyana inda aka kai hare-haren ba.

  4. Iran ta fara kai harin ramuwar gayya kan Amurka

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Dillancin na Fars ya ruwaito cewa Iran ta fara kai harin ramuwar gayya.

    Kafar yaɗa labaran ta ambato Rundunar Juyin juya halin ta Iran ta fara harba makamai masu linzami da aka samar a Iran.

  5. Masoud Pezeshkian ya gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Masoud Pezeshkian ya gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a gefen taron Kungiyar Haɗin Kan Shanghai da aka gudanar a birnin Bishkek na ƙasar Kyrgyzstan.

    A cewar kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA, a yayin ganawar, an duba tare da tantance halin da dangantakar ƙasashen biyu ke ciki a halin yanzu, tare da dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Rasha.

    Haka kuma ɓangarorin biyu sun tattauna hanyoyin ƙarfafa da faɗaɗa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.

    Kamfanin dillancin labaran Rasha na TASS ma ya ruwaito ganawar, sai dai bai bayyana cikakkun bayanai kan abubuwan da aka tattauna ba.

    Jami'in yaɗa labarai na fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce dangane da rawar da Rasha ke takawa wajen shiga tsakanin Iran da Amurka: "Shugaba Medvedev tabbas zai sanar da Mista Putin game da abin da ke faruwa."

    Wannan bayani na nuni da cewa Kremlin na ci gaba da sa ido kan ƙoƙarin diflomasiyya da kuma tattaunawar da ke gudana tsakanin Tehran da Washington.

  6. Iran ta ce za ta mayarwa Amurka da mummunan martani

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Kakakin Rundunar juyin juya hali na Iran ya ce za su mai mummunan martani kan Amurka a matsayin ramuwar gayya na harin da ta kai musu.

    Hossein Mohebi ya yi wa Amurka barzanar sai sun hukunta ta kuma sai ta yi nadamar wannan sabon harin da ta kai.

    Sanarwar da kakakin Rundunar ya fitar na zuwa ne daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi Iran ɗin da ka da ta sake ta mayar wa Amurka da martani.

  7. Majalisar Ƙoli ta Shari'a a Najeriya ta nemi a yi wa El Rufa'i adalci

    ,

    Asalin hoton, Nasir El Rufa'i

    Majalisar Ƙoli ta Shari'a ta Najeriya ta yi kira da a saurari ƙarar tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i, domin a samar masa da adalci a daina riƙe shi ba tare da sanin makomarsa ba.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakatarenta na ƙasa Nafi'u Baba Ahmed, SCSN ta ce a tsarin dokokin Najeriya babu wanda ake ayyanawa a matsayin mai laifi har sai an same shi da aikata laifin.

    SCSN ta ce a kundin tsarin mulki, ko wanne ɗan ƙasar na da 'yancin da ya kamata a mutunta shi, ba tare da duba inda ya fito ba ko addininsa ko kuma jam'iyyar siyasar da yake da alaƙa da ita, bin ƙa'idar aiki da adalci da kuma tsare mutum bisa doron doka ba zaɓi ba ne a ƙasar, suna cikin ginshiƙan na adalci a dokokin Najeriya.

    "Don haka, Majalisar ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su yi aiki da kundin tsarin mulki da dokokin Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa an bi duk matakan doka a kowane mataki.

    Haka kuma, Majalisar ta buƙaci hukumomi da su guji duk wani mataki da za a iya fassara shi a matsayin muzgunawa saboda dalilan siyasa, maimakon haka su nuna cikakken ƙudiri ga adalci, gaskiya da bin doka".

    Sanarwar ta ƙara da cewa haɗin kan Najeriya da kwanciyar hankalinta na dogon lokaci suna da alaƙa kai tsaye da adalcin da hukumomin gwamnati da kuma amincewar da al'umma suka yi da su.Dole ne a samar da adalc.

  8. Tsohon firaministan Birtaniya Starmer ya fice daga majalisar dokokin ƙasar

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa zai sauka daga kujerarsa ta ɗan majalisar dokoki.

    Sir Keir ya sauka daga mukamin firaminista ne a watan Yuni, inda Andy Burnham ya maye gurbinsa.

    Starmer ya ce yanzu yana so ya mayar da hankali kan “harkokin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da tsaro, kasuwanci da kuma fasaha.

    Matakin da ya ɗauka a yau zai sa a gudanar da zaɓen cike gurbi a mazaɓar Holborn da St Pancras da ke birnin Landan.

    Sanarwar ta biyo bayan hasashen da aka shafe makonni ana yi kan ko Sir Keir zai ci gaba da kasancewa ɗan majalisar dokoki ko a’a.

  9. Muna bibiyar kadarorin Iran a faɗin duniya - Amurka

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce ƙasarsa na bibiyar kadarorin Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) a faɗin duniya, yana mai gargaɗin cewa duk wata hukuma ko kamfani da ke mu'amala da rundunar zai iya fuskantar takunkumi.

    Ya ce Amurka za ta ƙara matsin tattalin arziki kan Iran, tare da sanar da sabbin takunkuman bankuna a cikin kwanaki masu zuwa.

    Bessent ya kuma yi barazanar ƙwace kadarorin jami'an rundunar da ke ƙasashen waje.

    Haka kuma, ya bayyana cewa Amurka ta tattauna da China kan hana Iran mallakar makaman nukiliya da kuma tabbatar da 'yancin zirga-zirga a Mashigar Hormuz.

    Shirin takunkuman da Washington za ta ƙaƙabawa Iran ya shafi ɓangarorin banki, fasaha, jigilar ruwa da sufurin jiragen sama.

  10. Yahudawa ƴan kama wuri zauna sun yi yunƙurin ƙona Masallaci a gaɓar Yamma

    Mahukunta a fannin addini na Falasɗinawa sun ce wasu yahudawa yan kama wuri zauna sun yi ƙoƙarin ƙona wani masallaci a arewacin Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

    Hotuna daga masallacin Nur al-Din Zanki da ke garin Bazzar-yah kusa da Nablus, sun nuna alamun ƙonewa a kusa da wata taga, da kuma saƙonnin barazana da aka rubuta da harshen yahudanci a jikin bango.

    Wani mazaunin yankin ya ce mutanen da ake zargin sun tsere, wanda ya sa mazauna garin suka samu damar shawo kan wutar kafin ta bazu.

    A cewar Ma’aikatar Harkokin Addini ta Falasɗinu, an kai hare-hare kan masallatai 13 daga yan kama wuri zauna ko kuma sojojin Isra’ila tun daga farkon wannan shekara.

  11. Najeriya ta kama bindigogi 204 da aka ɓoye a cikin kwantena a tashar jirgin ruwan Legas

    ,

    Asalin hoton, NCS

    Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta kama bindigogi kirar pump-action 204 da aka ɓoye a cikin wani kwantena da ya isa tashar jirgin ruwa ta TinCan Island da ke Legas daga ƙasar Turkiyya.

    An ɓoye makaman ne a tsakanin kayayyakin gida kamar kujeru, firinjoci, na'urorin hasken rana da kuma garin sabulu.

    Jami'an kwastam sun ce sun gano su ne bayan bayanan sirri da suka samu suka sa aka yi cikakken bincike kan kwantenan.

    Hukumar ta bayyana cewa bindigogin nau'in MAS 49 Alter Magnum pump-action rifles ne, kuma an gano wasu kayayyakin bindiga tare da su.

    Wannan ne karo na biyu cikin makwanni ƙalilan da aka kama irin waɗannan makamai a tashar, bayan da aka gano wasu bindigogi 399 a wani kwantena a watan Agusta.

    Jami'ai sun ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka shigo da makaman da kuma waɗanda aka nufa a kai musu.

  12. Isra'ila ta ce ta kama wani babban jami'in Hamas a Gaza

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya sanar da cewa dakarun ƙasarsa sun kama wani babban jami'in ƙungiyar Hamas a Gaza.

    Sanarwar ta zo ne bayan rahotannin da suka bayyana cewa dakarun musamman na Isra'ila tare da wata ƙungiyar Falasɗinawa da Isra'ila ke marawa baya sun gudanar da ayyuka a birnin Gaza.

    A cewar ma'aikatan agaji na yankin, hare-haren sama da Isra'ila ta kai sun kashe yara biyu da wata mata.

    Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare ne kan wurare da dama domin kawar da barazana, kuma babu wani soja nata da ya jikkata.

    Ministan bai bayyana sunan jami'in Hamas ɗin da aka kama ko yadda aka kama shi ba.

    Ya kuma jaddada cewa ayyukan sojojin Isra'ila a yankin Netiv Hasara da ke kusa da arewacin Gaza na ci gaba ba tare da tsayawa ba.

  13. Farashin man fetur ya ƙara tashi a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu ƙarin farashin man fetur a gidajen mai a sassan Najeriya tun daga farkon wannan mako, lamarin da ya sa masu motoci da sauran al'umma ke fuskantar ƙarin kashe kuɗaɗe wajen gudanar da harkokinsu.

    Rahotanni daga gidajen mai daban-daban sun nuna cewa sabon hauhawar farashin ya fara aiki a wasu jihohi tun daga Litinin.

    Masana na cewa tashi da saukar farashin man a kasuwannin duniya na ɗaya daga cikin abun da ya haddasa wannan lamarin.

    Sun ce hauhawar farashin ɗanyen mai na ƙara wa kamfanonin shigo da mai nauyin kudi, abin da ke tilasta musu daidaita farashin da ake sayar da man fetur a cikin gida.

    Tun bayan sanar da sabon farashin, al'umma da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda lamarin zai ƙara tsananta matsin rayuwa.

  14. Putin da Pezeshkian sun tattauna dangantakar Iran da Rasha a Kyrgyzstan

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a gefen taron kungiyar Shanghai Cooperation Organization (SCO) da aka gudanar a birnin Bishkek na ƙasar Kyrgyzstan.

    Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA ya ce shugabannin biyu sun duba halin da dangantakar kasashensu ke ciki tare da tattauna hanyoyin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.

    Shi ma kamfanin dillancin labaran Rasha TASS ya tabbatar da ganawar, amma bai bayyana cikakkun bayanan tattaunawar ba.

    A wani bangare, kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce shugaban ƙasar zai samu bayani kan abubuwan da ke faruwa dangane da batun shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka.

  15. 'Babu wata ƙungiyar Musulmi da ke shirin kafa hukumar Hisbah a Filato'

    ...

    Asalin hoton, Jama’atu Nasril Islam/X

    Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jihar Filato ta musanta rahotannin da ke cewa akwai wata ƙungiyar Musulmi da ke shirin kafa hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

    Sakataren ƙungiyar jihar, Dr Salim Musa Umar, ya ce babu wata ƙungiyar Musulmi da ta sanar da irin wannan shiri, yana mai cewa labarin ya samo asali ne daga wasu hotuna da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI aka yaɗa a kafafen sada zumunta.

    Ya bayyana cewa ba za a iya kafa Hisbah a hukumance ba sai da dokar Majalisar Dokokin Jihar Filato, kuma babu irin wannan doka da gwamnati ta kafa.

    Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati da masu amfani da shafukan sada zumunta su riƙa tantance bayanai kafin yaawa domin kauce wa tayar da hankula da kuma kare zaman lafiya a jihar.

  16. An kai hari kan tankokin man Saudiyya biyu a mashigar Hormuz

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce an kai hari kan manyan tankokin dakon mai guda biyu na Saudiyya yayin da suke bi ta mashigar Hormuz a daren Litinin.

    Kamfanonin sa ido kan harkokin jiragen ruwa, Marisax da Kepler, sun bayyana cewa wasu makamai masu linzami da ba a gano waɗanda suka harba su ba ne suka kai wa tankokin hari a tazarar mintuna kaɗan tsakaninsu.

    Bayanan Kepler sun nuna cewa tankokin sun ɗauki ganga miliyan biyu na ɗanyen man Saudiyya daga tashar Juaima da ke gaɓar Tekun Fasha a makon da ya gabata.

    Lamarin ya ƙara tayar da hankula game da tsaro a yankin mashigar Hormuz, wadda ke ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya.

  17. Ina aka samo kalmar Takutaha kuma me ya sa ake biki a ranar?

    ....

    Asalin hoton, Abba Hamza

    Wannan maƙala ce da aka rubuta kuma aka wallafa a ranar 12 ga watan Satumban 2025. Yanzu kuma an sake wallafa ta saboda dacewar ranar.

    A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, da zarar ranar Maulidin Annabi Muhammad ta zo, ta wuce, hankali yana komawa ne kan bikin Takutaha.

    Ana dai gudanar da bikin Takutaha ne a ranar bakwai daga ranar Maulidi, wato ranar da Hausawa a al'ada suke yin bikin sunan wanda aka haifa.

    A ranar bakwai da haihuwa ne dai aka saba da bikin raɗa suna da yanka da taron bikin na suna idan an samu ƙaruwa.

    Bikin na Takutaha dai yana ɗaukar hankali sosai ne, inda mutane da dama suke bukukuwan shagali da dama, akwai dafe-dafe da yanka, sannan ake hawa domin murnar ranar.

    Sai dai akwai bukukuwan al'ada da dama da ake aiwatarwa a ranar, sannan kuma akwai abubuwa da suke da alaƙa da ibada.

  18. An sami Duane "Keffe D" Davis da laifin kashe Tupac Shakur bayan kusan shekaru 30

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Las Vegas, jihar Nevada ta Amurka, ta samu tsohon shugaban ƙungiyar 'yan daba Duane "Keffe D" Davis da laifin kashe shahararren mawaƙin rap Tupac Shakur, wanda aka harbe a shekarar 1996.

    Alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan shari’ar da ta ɗauki makonni ana sauraron shaidu da hujjoji.

    An same Davis mai shekara 63 da laifin kisan kai na matakin farko tare da amfani da makami.

    Masu gabatar da ƙara sun ce shi ne ya shirya harin da aka kai wa Tupac bayan wata arangama da ta haɗa mawakin da dan uwansa Orlando Anderson a daren da aka kashe shi.

    Tupac Shakur, ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan hip-hop a duniya, ya samu raunuka ne yayin harbin da aka yi masa daga cikin wata mota a Las Vegas a ranar 7 ga Satumban 1996.

    Ya rasu kwanaki shida bayan harin yana da shekara 25 kacal, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da hasashe tsawon shekaru da dama ba tare da an kama wani ba.

    An sake farfaɗo da binciken kisan ne bayan Davis ya bayyana wasu bayanai a cikin tarihin rayuwarsa da aka wallafa a shekarar 2019.

    Bayan hukuncin kotun, an bayyana cewa zai iya fuskantar ɗaurin rai da rai, yayin da ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

  19. EFCC ta kori ma'aikata sama da 40 kan tafka cin hanci

    ...

    Asalin hoton, EFCC/X

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce ta kori ma'aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata saboda hannusu a cin hanci da sauran laifukan kuɗi.

    Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce fiye da mutum biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari'a a kotu, yayin da ake shirya gurfanar da wasu.

    Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙaddamar da sabbin matakan tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin ma'aikatanta, yana mai cewa EFCC ba za ta iya yaƙar cin hanci yadda ya kamata ba idan nata jami'an suna aikata irin wannan laifi.

    Haka kuma ya ce hukumar ta ƙwace sama da naira tiriliyan 1.23 da wasu manyan kuɗaɗen ƙasashen waje tsakanin Oktoban 2023 da Yunin 2026.

  20. Tinubu ya yaba da ceto 'yan bautar ƙasa da aka sace a Kogi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jinjinawa jami'an tsaro bayan ceto mutum 21 da aka sace a jihar Kogi, ciki har da mambobin bautar ƙasa 15.

    Shugaban ya ce haɗin gwiwar sojoji, 'yansanda, jami'an DSS da kuma masu sa-kai ne suka gudanar da aikin ceton, inda aka kuɓutar da waɗanda aka sacen daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Ofu.

    Tinubu ya ce jami'an tsaro na ci gaba da farautar masu garkuwar, yana mai jaddada cewa duk wanda ke da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa doka.

    Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.