Ina aka samo kalmar Takutaha kuma me ya sa ake biki a ranar?

Asalin hoton, Abba Hamza
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, da zarar ranar Maulidin Annabi Muhammad ta zo, ta wuce, hankali yana komawa ne kan bikin Takutaha.
Ana dai gudanar da bikin Takutaha ne a ranar bakwai daga ranar Maulidi, wato ranar da Hausawa a al'ada suke yin bikin sunan wanda aka haifa.
A ranar bakwai da haihuwa ne dai aka saba da bikin raɗa suna da yanka da taron bikin na suna idan an samu ƙaruwa.
Bikin na Takutaha dai yana ɗaukar hankali sosai ne, inda mutane da dama suke bukukuwan shagali da dama, akwai dafe-dafe da yanka, sannan ake hawa domin murnar ranar.
Sai dai akwai bukukuwan al'ada da dama da ake aiwatarwa a ranar, sannan kuma akwai abubuwa da suke da alaƙa da ibada.
Asalin kalmar Takutaha
Domin sanin inda aka samo sunan Takutaha, BBC ta tuntuɓi tsohon kwamishinan addini na jihar Kano, kuma masanin harsunan Najeriya da al'adun Hausawa, Dakta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible), wanda ya ce sunan yana da alaƙa da Shehu Usman Ɗanfodio.
Ya ce, "Takutaha idi ne kamar yadda a addinin Musulunci ake da idi ƙarama da babba.
Shi wannan biki ne da ake yi a ranar bakwai da haihuwar Annabi Muhammad. An haifi Annabi a ranar 11 da wata, idan ranar ta zagayo ranar suna kenan. To ranar ce ake kira da ranar bikin Takutaha."
Ya ce yadda sunan ya samo asali shi ne, "a ranar ne a lokacin baya mutane suka fito cikin gari suna ta zagaye suna murna, sai Shehu Usman Ɗanfodio ya fio yana tambayar me ya faru? Sai aka amsa cewa mutane ne suke murnar ranar sunan Annabi."
Baba Impossible ya ce wannan lokacin ne sai Ɗanfodio ya ce, "'ku tai, taku ta'. Wato ku je taku ce. Shi ne sai sunan ya koma Takutaha."
Hawa Dutsen Dala
Bikin Takutaha musamman a jihar Kano yana tumbatsa ne da zuwa hawan dutsen Dala, lamarin da Baba Impossible ya ce al'ada ce wannan da aka shigar cikin asalin ibadar da ake yi a ranar.
Ya ce a lokacin da addinin Musulunci ya isa ƙasar Hausa, ya tarar da Hausawa a wancan lokacin a Kano suna bautar Tsunburbura.
"A lokacin ana zuwa hawan duten Dala duk shekara domin gudanar da ayyukan bauta irin su yanke-yanke da sauransu a duk shekara domin bautar Aljana Tsunburbuwa, sai Musulunci ya zo ya hana.
To a al'ada, idan aka hana mutum wani abu, akan kawo masa wani abu da zai maye masa wannan gurbin ko da kuwa bai kai wancan da aka saba da shi ɗin ba.
Wannan ne ya sa suka mayar da wannan ranar ta Takutaha ta zama ta maye musu wannan ranar ta hawa dutsen Dala," in ji Baba Impossible.
Abubuwan da suka kamata a ranar
Baba Impossible ya ce rana ce ta ibada, don haka ya lissafa wasu ayyuka da ya ce za su yi kyau a aikata kamar haka:
- Karatun Alƙur'ani
- Sadaka
- Zikiri
- Shiga mai kyau
- Zagaye cikin natsuwa
Abubuwan da ba su dace ba
Sai dai Baba Impossible ya yi gargaɗin cewa ana shigar da wasu abubuwa cikin lamarin, waɗanda a cewarsa za su iya yiwuwa su ɓata aikin ranar.
Ya ce ,"Maulidi bai fi shekara 100 ba da zuwa ƙasar Hausa kuma abin da aka saba shi ne karaun Alƙur'ani da karatun Dala'ilu da yabon Annabi da sauransu.
Amma yanzu sabon abu ya zo da ake fareti mata da maza suna kaɗa-kaɗe suna rawa suna girgiza wai duk da sunan Maulidi, wai har ƴan daudun ma'aiki da ƴan gayun ma'aiki duk akwai," in ji shi.
Ya ce irin waɗannan shagulgulan da suka saɓa da addini da al'ada ba sa cikin abubuwan da suka kamata a yi a ranar Maulidi ko Takutaha.
"Wannan ba addini ba ne, kuma ya kamata hukumomi su ɗauki matakin gaggawa wajen hanawa," in ji shi.
Dala tamkar Arfa?
A game da tunanin da mutane da dama suka taso da fahimtar cewa hawa dutsen Dala na iya zama tamkar zuwa dutsen Arfa, Baba Impossible ya ce wannan ma tunani ne na molan ka na mutanen da, amma babu wata madogara a kai.
Ya ce maganganu ne kawai aka taso ana yi ba tare da wata hujja ba daga wasu littafan addinin Musulunci.
"A irin waɗannan maganganun ma akwai wata rijiya da tun muna yara muke zuwa mu leƙa.
An ce idan ka kira sunan mamaci sai biyu, amma bai amsa ba to yana aljanna, idan ya amsa kuma yana wuta," in ji shi inda ya nanata cewa "amma duk waɗannan maganganu ne kawai da babu hujja."
Ya ce zuwa kallon rijiyar da hawa dutsen Dala duk abubuwa ne kawai na al'ada, "sai aka alaƙanta shi da addini saboda an maye gurbin hawa Dala domin bautar Tsunburbura da hawan bikin Takutaha.
"Ai ba zai yiwu a ce hawa dutsen Dala ibada ba ne saboda a Kano ne ake da Dala. Idan ibada ce, sauran ƙasashe da jihohin yaya za su yi ke nan?"











