Hanyoyi daban-daban da ake bikin Maulidi a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Ana baje koli launuka ga kuma ƙaran ganguna, yayin da farin ciki da soyayya suka karaɗe ko ina musulma lokacin da musulmi ke rububin yi masa addu'a. Ana rera waƙoƙin yabo a harussan duniya daban-daban daga dukkan sassan duniya domin murnar zagayowar ranar haihuwar annabin musulunci, Muhammad (S.A.W)
Musulmi daga sassan duniya na gudanar da bukukuwan maulidi ne ta hanyoyi daban-daban, amma yanayin yadda ake ji na da kamanceceniya da juna kuma suna da yanayi na nutsuwa da kwanciyar hankali da ke yaduwa kamar yadda sautin ganguna da na wake-waken yabo ke yaɗuwa.
Kowace al'umma tana da yadda ta ke bikin maulidin Annabi. Duk da cewa musulmi a ƙasashe da dama sun samu saɓani kan halascin gudanar da wannan biki, amma ana ci gaba da gudanar da bukukuwan. Waɗanda suka ziyarci waɗannan kasashe sun shaida yadda ake yi, kuma waɗanda ba su gani ba suna iya ganinsu a shafukan sada zumunta, inda hotunan bikin suka bazu.

Asalin hoton, MAHMOUD ZAYYAT/AFP via Getty Images

Asalin hoton, Faisal Khan/NurPhoto via Getty Images
Abinci na musamman
Musulmai suna shirya abinci na musamman don tunawa da ranar haihuwar Annabi, wanda yawanci kayan zaƙi ne.
Ƴan ƙasar Tunisiya suna shirya "Asida Zgougou" daga ɓangarorin pine na ƙasa, waɗanda aka yi wa ado da busassun ƴaƴan itace, da kuma wasu kayan zaƙi na musamman.
A wasu sassan ƙasar, ƙan kasar Aljeriya na gudanar da bukukuwa ta hanyar girka "Tamina", wani abincin ƙwalama na gargajiya da aka yi da zuma da man shanu.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP via Getty Images
Mutanen Iraqi suna dafa zarda daga shinkafa da sukari da garin cardamom, ana kuma ana yi masa ado da kayan yaji.
A ƙasar Masar, "Halawet El Mawlid" ta shahara a nau'o'i daban-daban, amma waɗanda suka fi shahara a wannan lokaci su ne "ƴar tsanar Maulidi" da "Dawakan Maulidi", waɗanda ake yin su da sukari.
Akwai musulmin da ke girka abincin da ba kayan zaƙi ba don murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, kamar Indonesiya, inda ake dafa curry na gargajiya da yawa ana rarrabawa jama'a.

Asalin hoton, Getty Images
Zikiri da waƙe-waƙen yabo
Musulmi na karrama Annabi Muhammad ta hanyar yabo, wanda yawanci ana karanta su da sautin mandiri. Ana gudanar da bukukuwa da da'irar zikiri da madih, inda masoya Annabi suke lissafta falalolinsa, suna neman cetonsa, da nuna ƙwarin gwiwar ganinsa.
Wasu mutane suna taruwa su zagaye waɗanda ke rera waƙoƙin tarihin Annabi.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Wasu kasuwanni na farfaɗowa yayin bikin
Musulmi na murnar zagayowar ranar haihuwar annabin musulunci da farin ciki, da ado da kuma launuka. Bikin ya sauya yanayin kasuwanni su zama tamkar wasu abubuwa masu ƙayatarwa.
Haka kuma maulidin Annabi wani dama ne tabbatar da zumunci da zamantakewa a kan ka'idojin da musulmin da ke gudanar da maulidin Annabi suka samu daidaito a kai.
Wasu sana'o'in suna bunƙasa ne a ranar maulidin, yayin da buƙatar sayen kayan zaƙi da kayan abinci a musamman da ganguna da kayan ado da tufafin gargajiya, da sauran kayan gargajiya ke ƙaruwa.
Sai dai wasu na ganin cewa maulidin manzon Allah ya zama taron kasuwanci da kuma wata dama ga wasu ƴan kasuwa su samu gagarumar riba.
Wannan ne ya sa wasu ƴan ƙasar Tunisia, alal misali, suka kauracewa "Zgogogo", wanda ake amfani da shi wajen yin faten Maulidi, saboda tsadar sa.

Asalin hoton, SAFIN HAMID/AFP via Getty Images
Mene ne asalin bikin ranar haihuwar annabi?
Dangane da asalin bikin maulidin, majiyoyin tarihi sun bayyana cewa, mutumin da ya fara gudanar da bukukuwan maulidin Annabi akai-akai, shi ne sarkin Erbil, Sarki Abu Saeed Kukburi.
Bayan haka ne Fatimidu suka yi maulidin Manzon Allah (S.A.W) har sai da Khalifa Al-Musta'ali ya yi umarni da a soke bikin a shekara ta 488 bayan hijira.
Bayan haka kuma an takaita bikin maulidin manzon Allah ne a kan raba kayan zaki, da bayar da sadaka, da masu zuwa masallaci.
Tun daga wannan lokacin ne yanayin gudanar da bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W) suka bambanta, tun daga rabon kuɗi ga talakawan musulmi, da waƙe-waƙe a zamanin Ayyubid, zuwa ga manya-manyan bukukuwa masu ƙayatarwa a lokacin daular Ottoman.










