Yadda aka fara komawa makaranta a Gaza bayan shekara biyu na yaƙi

Dalibai na daukar darasi a cikin wani aji a Gaza
Bayanan hoto, Unicef ta ce an lalata fiye da kashi 97% na makarantu a Gaza a tsawon lokacin da aka kwashe ana gwabza yaƙi
    • Marubuci, Shaimaa Khalil
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 6

A Birnin Gaza, yanzu za ka iya jin sautin yara na koyon darussa.

A yanzu tantunan da ake amfani da su a matsayin ajujuwa na cika da ɗalibai kuma lamurra na tafiya.

Ga malamai suna koyarwa a gaban allo, yayin da wasu daga cikin malaman kan kira ɗalibai zuwa gaban allo domin rubuta wasu kalmomin Larabci.

Duk da cewa ba kamar makaranta ta yau da kullum ba, amma wannan kamar farowa ne daga tushe bayan tsagaita wuta da aka yi tsakanin Isra'ila da Hamas a watan Oktoba.

Bayan shekara biyu ana gwabza yaƙi sautin muryar ɗalibai na tashi, sannan za ka iya jin yara suna surutu a cikin ajujuwa da ke tsakiyar rugurguzazzun gine-gine, a wurin da a baya ya kasance makarantar da ake kira Lulwa Adbel Wahab al-Qatami, da ke unguwar Tel al-Hawa a kudu maso yammacin Birnin Gaza.

A watan Janairun 2024 ne aka kai farmaki kan makarantar, sai dai a watannin da suka biyo bayan harin an riƙa amfani da filin makarantar a matsayin sansanin mutanen da aka tarwatsa daga gidajensu.

Yanzu ta sake komawa a matsayin makaranta, amma ba kamar yadda take ba a baya.

Yara ne sun jera ɗoɗar, inda na baya suka ɗoɗɗora ƙananan hannuwansu kan kafaɗar na gaba, suna murmushi yayin da suka kama hanyar shiga tantunan da aka yi a matsayin ajujuwa.

Wannan ne lokaci na farko da, da dama daga cikinsu suka koma aji da kuma rayuwa mai kama da wadda suka saba yi a shekarun baya.

Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya, wato Unicef, ta ce an lalata fiye da kashi 97% na makarantun Gaza a lokacin yaƙin.

Rundunar sojin Isra'ila ta sha nanata zargin cewa Hamas na amfani da gine-ginen fararen hula kamar makarantu a matsayin mafaka wajen gudanar da ayyukanta, sai dai ba kasafai take bayar da wata ƙwaƙƙwarar hujja kan hakan ba.

Daga cikin yara 658,000 da ya kamata a ce suna zuwa makaranta a yankin, akasarin su ba su taɓa shiga aji ba a tsawon shekara biyu na yaƙin.

A tsawon lokacin babu abin da suka fuskanta face yunwa da gudun hijira da kashe-kashe a rayuwarsu ta ƙuruciya.

Amma a yanzu wannan abu da ba a saba gani ba na dawowa.

 Gaza
Bayanan hoto, Wannan ne karo na wasu daga cikin waɗannan ɗalibai suka koma makaranta tun bayan ɓarkewar yaƙi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Nadeem al-Asmar mai shekara 14 a duniya ya kasance yana zuwa makaranta kafin yaki ya rushe makarantar. Ya rasa mahaifiyarsa a wani harin da Amurka ta kai a lokacin yaƙin.

"Wannan ne lokaci mafi wahala da na taɓa samun kaina a ciki," in ji shi, lokacin da yake magana ƙasa-ƙasa.

Duk da cewa ya yi gudun hijira na tsawon watanni, gidansu na daga cikin ƙalilan da ba su lalace ba a Birnin Gaza. Shi da iyalinsa sun koma gida bayan tsagaita wuta.

"Na yi kewar zuwa makaranta sosai," in ji Naeem wanda ya ce akwai matuƙar bambanci.

"Kafin fara yaƙin akwai ajujuwa na ƙwarai."

"Yanzu kuwa tantuna ne. Darussa hudu kawai ake koya mana. Babu isassun ajujuwa. Koyon ilimi a yanzu ya sha bamban - amma hakan ma na da amfani. A baya makaranta ce ke cinye min lokaci, kuma ina ƙaunar hakan."

Rital Alaa Harb ɗaliba ce da ke aji na tara, wadda take da burin zama likitar haƙori.

"Gudun hijira ya yi illa ga neman ilimina," in ji ta. "Babu lokacin yin karatu. Babu makarantun. Na yi kewar ƙawayena sosai - kuma na yi kewar tsohuwar makarantata."

Hukumar Unicef ce take gudanar da makarantar a yanzu, inda ta hado yara asalin ɗaliban makarantar da kuma ƴan gudun hijira daga wasu yankunan.

A yanzu ba a koyar da dukkan darussan da aka saba - sai dai wadanda suka fi muhimmanci kawai, kamar Turanci da Larabci da Lissafi da kuma darasin Kimiyya.

Shugaban makarantar Dr Mohammed Saeed Schheiber ya shafe shekara 24 yana aiki a ɓangaren ilimi. Ya karɓi jagorancin makarantar ne a tsakiyar watan Nuwamba.

"Mun mayar da hankali sosai a lokacin da muka fara." in ji shi, "domin ganin ko za mu iya maye karatun da ɗalibai suka yi hasara."

Dr Mohammed Saeed Schheiber
Bayanan hoto, Dr Mohammed Saeed Schheiber ya ce ɗalibai da dama na fama da matsananciyar damuwa

Yanzu haka makarantar na koyar da ɗalibai maza da mata wadanda yawan su ya kai 1,100, inda ake yin makarantar sau uku a rana, ɗalibai maza na zuwa a ranaku daban da na mata.

Malamai 24 ne kawai a makarantar.

Dr Schheiber ya ce "kafin yaƙin dalibai na yin karatu ne a ajujuwa masu kyau da kuma cikakkun kayan aiki - da ɗakunan bincike, akwai sadarwar intanet da duk wasu kayan karatu. Yanzu duk babu waɗannan."

Babu lantarki, babu intanet, sannan ɗalibai da dama na fama da damuwa.

Fiye da ɗalibai 100 a makarantar sun rasa ɗaya daga cikin iyayensu, an lalata muhallinsu, ko kuma sun ga yadda aka kashe mutane a gabansu. Baki ɗaya dai, babu wanda yaki bai shafa ba a cikinsu, a cewar Dr Schheiber.

Yanzu akwai wani mai bayar da shawarwari da ke kula da ɗaliban yana taimaka musu, yana ƙoƙarin ganin halin da suka shiga bai dagula musu rayuwa ba.

Sai dai suk da ƙoƙarin da ake yi, abin da ake da shi ba zai isa ba, ko kaɗan.

Dr Schheiber ya ce "muna da ɗalibai sama da 1,000 a yanzu, amma ajujuwa shida kawai muke da su. Akwai wani makeken sansanin yan gudun hijira a kusa da makarantar wanda ke ɗauke da mutane da suka fita daga arewaci da kuma gabacin Gaza. Yara da yawa na son su shiga makarantar. Amma ba za mu iya ɗaukan su ba."

 Gaza
Bayanan hoto, Iayaye da dama sun ce ƴaƴansu sun yi asarar shekarun karatu

Ga iyaye, sake bude makarantar abin farin ciki ne da kuma fargaba a gare su.

Huda Bassam al-Dasouki, wadda ke da ƴaƴa biyar kuma take gudun hijira daga kudancin Rimal, ta ce ilimi ya zama wani babban ƙalubale.

Ta ce "Ba wai ba za a iya samun ilimi ba ne, a'a, amma samun ilimin ne ya yi matuƙar wahala."

Tun ma kafin a fara yaƙin makarantu na fama da ƙarancin kayan aiki, in ji ta. Yanzu kayan aikin ba su samuwa, ko kuma sun yi matuƙar tsada.

Ta ce "kafin yaƙin ana sayar da littafin rubutu kan kudi shekel ɗaya amma yanzu ya kai shekel biyar. Yarana biyar."

Jonathan Crickx
Bayanan hoto, Jonathan Crickx ya ce hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza ya yi wa makarantu illa

Hukumar Unicef ta ce dokokin da aka sanya na hana shigar da agaji sun sa lamurra sun yi muni.

Jonathan Crickx, jami'i mai magana da yawun hukumar wanda ke tsaye a ƙofar makarantar ya yi bayani kan abubuwan da ke ƙaranci.

"Takardun rubutu, alƙalami, abin goge rubuta da rula... mun sha magana kan cewa a ƙyale a shigo da waɗannan kaya cikin Gaza, amma abin ya gagara. Haka nan ma batun kayan da ake amfani da su wajen koya wa yara karatu ta hanyar wasa - wadanda ake iya amfani da su domin cire damuwa a ƙwaƙwalwar yara," in ji shi.

Wani jami'in sojin Isra'ila ya tura mu ofishin Firaminista don neman bahasi, amma ba su amsa buƙatar neman bayani da BBC ta tura musu ba.

Isra'ila ta ce tana cika ƙa'idojin tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ta hanyar bari kaya na shiga Gaza. Amma Majalisar Dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin bayar da agaji sun musanta hakan, inda suka zargi Isra'ila da ci gaba da hana shigar da kayan amfanin buƙata zuwa yankin.

Duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, Isra'ila ta ci gaba da jefa bamabamai a Gaza - inda take kai hari a kusan kowace rana - bisa dogaro da abin da ta bayyana a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta daga Hamas.