Adadin waɗanda aka kashe a zanga-zangar Iran ya wuce yadda ake tsammani - Rahotanni

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Rahotanni daga Iran na ƙara nuni da cewa adadin masu zanga-zangar da jami'an tsaro suka kashe ya ƙaru, yayin da zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar ta shiga mako na uku.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Iran mai hedikwata a Amurka (HRANA) ta ce, ta tabbatar da mutuwar kusan mutane dari biyar bayan wasu rahotannin da ba tantance ba sun ce sahihin adadin waɗanda aka kashe zai iya ninka wanda aka sanar.
Kamfanin dillancin labaran Iran Tasnim ya ce an kashe sama da jami'an tsaro 'dari.
Duk da katsewar internet, sashen Fasha na BBC ya samu waɗanda suka tabbatar da adadin.
Wani mutum da aka zanta da shi ya ce munin yanayin ya wuce yadda ake bayyanawa.















