Waɗanne irin bama-bamai Amurka ta jefa wa Najeriya kuma mene ne hatsarin su?

Amurka

Asalin hoton, US Department of Defense

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yadda ake cigaba da yaɗa hotunan mutane suna nuna ɓurɓushin bama-baman da ake tunanin Amurka ta yi amfani da su wajen ƙaddamar da hare-hare a Najeriya na ci gaba da jan hankalin ƴan ƙasar.

A ranar 25 ga watan Disamba ne Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta ƙaddamar da abin da ya kira da wani mummunan hari kan mayaƙan da ya ce ƴan IS ne a arewa maso yammacin Najeriya.

Cibiyar sojin Amurka a Afrika daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto, sannan daga baya aka tsinci ɓurɓushin bam a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya.

Trump ya ce "a ƙarƙashin shugabancina, ƙasarmu ba za ta bar masu tsattsauran ra'ayin Musulunci sun gawurta ba."

Ma'aikatar tsaron Amurka ta wallafa wani gajeren bidiyo da ke nuna wani harin makami mai linzami da aka harbo daga wani jirgin ruwan soji.

Mista Trump bai faɗi lokacin da aka yi kashe-kashen ba da yake magana a kai ba, amma kuma ya yi zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya wanda batu ne da ya yi ta wadari tsakanin masu kaifin ra'ayin Kiristanci a Amurka.

A nata ɓangaren, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce harin wani ɓangare ne na haɗin gwiwar tabbatar da tsaro da aka ƙulla da Amurka.

Sai dai bayan ganin yadda hotunan bama-baman ke karaɗe duniya, ƴan Najeriya sun fara shiga fargabar ko dai akwai illa da za su fuskanta gan gaba saboda hare-haren na Amurka.

Na'ukan makaman

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Domin sanin irin makaman da Amurka ta yi amfani da su da ma illolinsu, BBC ta tuntuɓi Dr. Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, wanda mai bincike ne kan harkokin tsaro a yankin Sahel, inda ya ce makamai ne sanannu.

Ya ce Amurka ta yi amfani da sansaninta ne da ke nahiyar Afirka wajen shiryawa da ƙaddamar da harin.

"Daga tekun Atlantic ne wani jirgi ya harba makamin da ake kira Tomahawk WDU‑25/B unitary warhead. Da shi da sauran nau'ukan makamai wanda ake iya saitawa ta amfani da na'uran GPS ana kiran su GPS-guided munition Joint Direct Attack Munition."

Masanin tsaron ya ce bayan wannan makamin, akwai kuma wasu bama-baman da jirgi mara matuƙi na MQ‑9 Reaper ya jefa. "Ana ana kiran bama-baman da suna AGM‑114 Hellfire II," in ji shi.

Dangane da irin ƙarfin bama-baman, Kabiru Adamu ya ce ya ce Tomahawk WDU‑25/B jirgi ne mai zaman kansa, "wanda nauyinsa ya kai kilogram 450, sannan akwai sinadaran bom kusan 171 a ciki bayan kaskonsa."

Masanin tsaron ya ce makamin zai iya rusa gine-gine, kuma zai iya kutsawa cikin ƙasa saboda a cewarsa, ana iya tura shi zuwa inda ake so saboda tsananin saitinsa.

Ya ƙara da cewa bama-baman da jirgi mara matuƙi na MQ-9 Reaper ya harba, "su kuma nauyinu kusan kilogram 9, sai kuma akwai GBU waɗanda nauyinsu ya kai kilogram 4 zuwa 5."

Kabiru Adamu ya ce makamai na zamani ne da ake fargabarsu, "musamman saboda ganin suna da saiti sosai, kuma da wahala su kauce daga inda aka inda aka harba su."

Shi ma Group Captain Sadiq Garba Shehu (Mai Ritaya), ya ce daga ganin irin hotunan da suke yawo na makaman, makamai ne dangin "GPS-guided munition Joint Direct Attack Munition wato JDAM"

Hatsarin bama-baman

A game da fargabar da ake yi na hatarin makaman, da kuma ko akwai wata matsala da za a gani a nan gaba, Sadiq Garba Shehu ya ce tsintar irin waɗannan makaman na da illa da hatsari.

"Wajen haɗa irin waɗannan makaman, ana amfani da ƙarafuna masu ƙarfi wasu lokutan ba sa fashewa. Idan ka lura da hotunan da ake yaɗawa, za ka ga ba su fashe ba."

Sai dai ya ce akwai matsala ne da zarar an fara tsintarsu, "akwai wasu sinadarai a ciki waɗanda da zarar an ƙona su, za su iya fashewa. Kuma kasan masu gwangwan za su iya kwasa, ko kuma yara su tsinta."

Ya ce bayan ƙonawa, ko buga musu wani ƙarfe aka yi za su iya fashewa, kuma su fitar da ƙananan ƙarafuna da sinadarai.

"A ɗaya ɓangaren kuma, idan suka faɗa cikin ruwa, za su iya gurɓata ruwan, sannan kifi da sauran halittun cikin ruwan za su iya mutuwa. Sannan idan suka nutse a cikin ƙasa ma, suna lalata ƙasar noma."

A nasa jawabin, Kabiru Adamu ya ce bayan gurɓata muhalli, "babban abin da ya damuwa shi ne bama-baman da ba su fashe ba. Domin za su iya fashewa daga baya, sannan su haifar da matsala," in ji shi.

Tarihin makamin

Domin sanin tarihin wannan makamin, mun garzaya shafin The Royal United Services Institute (RUSI), inda suka wallafa cewa an fara amfani da makami dangin Joint Direct Attack Munition (JDAM) ne a shekarar 1991.

An yi amfani da makamin ne lokacin da Amurka ta jagoranci aikin soji na musamman domin fatattakar Iraqi daga Kuwait.

Amurka ta fara amfani da makamin ne bayan fahimtar akwai buƙatar samar da makamin da zai jure yanayin sanyi ko damuna da sauransu.

Sai dai JDAM dangin makamai ne, wanda a cikinsa ne akwai Tomahawk wanda ake tunanin Amurka ta harba a Najeriya.

Kisan kiristoci a Najeriya

Tun da farko, ɗan majalisar dokokin ƙasar Amurka, Sanata ted Cruz ne ya zargi gwamnatin Najeriya da bari ana yi wa Kiristoci "kisan kiyashi".

Sanata Ted Cruz dai ya gabatar da ƙudirin ne a gaban majalisar dattawan Amurka a watan Satumba, inda ya yi zarge-zargen.

A ranar Talata ta 8 ga watan Oktoban ne kuma Ted Cruz ɗin ya wallafa a shafinsa na X cewa ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi a Najeriyar sun kashe Kiristoci 50,000 daga shekarar 2009 kawo yanzu a faɗin ƙasar, sannan sun lalata makarantun mabiya addinin Kiristan 2,000 da coci 18,000.

Shi ne sai Ted Cruz ya nemi majalisar dokokin Amurkar ta ƙaƙaba wa jami'an gwamnatin Najeriya waɗanda ya zarga da "kawar da kai da ma wani lokacin taimakon masu ɓarnar, takunkumai.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen na Sanata Ted Cruz, inda ta ce ƙungiyoyn da suke yin hare-haren suna harar ƴan Najeriya ba tare da banbanci ba, sannan ta kuma amince da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar amma ta ce ana samun ci gaba.

Gwamnatin ta kuma musanta zargin cewa ba sa yin komai wajen hana kisan Kiristocin.

Ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙari wajen ƙoƙarin fattakar ƙungiyoyin ƴanta'adda a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyin ƴanƙasar, kuma ana ganin sakamakon hakan.

Daga baya Trump ya saka baki kan lamarin, inda ya ce ko dai Najeriya ta ɗauki mataki, ko kuma ya ɗauki mataki da kansa.

Ana cikin tattauna barazanar ta Trump ne, sai kwatsam shugaban na Amurka ya sanar da ƙaddamar da hare-hare a ƙaar.