Me ya sa ake zargin cewa ana yin kisan-ƙare dangi a Najeriya?

Bola Tinubu, zaune a ofishinsa

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

Lokacin karatu: Minti 6

Gwamnatin Najeriya ta yi kakkausan Allah wadai da nesanta kanta da wasu rahotonnin da ke cewa ƴanbindiga na aikata kisan ƙare-dangi a ƙasar.

Wasu kafofin yaɗa labaran intanet na ƙasashen waje da fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta ne suka yi ta yaɗa zargin cewa ƴanbinga a ƙasar na yin wani tsari da suke aikata kisan ƙare-dangi kan mabiya addinin Kirista a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ma'aikatar yaɗa labaran ƙasar, ta ce, zarge-zargen ba su da tushe balle makama, kuma an ƙirƙire su ne domin raba kan al'ummar ƙasar.

''Jingina matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta kan wani keɓantaccen addini, babban kuskure ne da kuma ɓoye gaskiya'', in ji sanarwar.

Ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce Najeriya kamar sauran ƙasashen duniya na fama da matsalar tsaro da suka ƙunshi ayyukan ƴanta'adda da masu aikata laifuka, amma jingina hare-haren kan wani addini ɗaya ba gaskiya ba ne.

Mohammed Idris ya ce yin hakan babban kuskure ne da zai yi wa ƙasar mummunan illa.

''Ayyukan ƙungiyoyin ƴanta'adda ba su da alaƙa da wani addini ko ƙabila, waɗannan ƙungiyoyi kan farmaki duk wanda ba ya tare da aƙidarsu, ba tare da la'akari da addini ko ƙabila ba, da Musulmai da Kirista da ma waɗanda ba su da addini ba wanda bai sha wahalar waɗannan ƙungiyoyi ba.'' in ji ministan.

Me ake cewa kan kisan ƙare dangi a Najeriya?

Dakta Kabiru Adamu Shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce ƙasashen Yamma na fakewa a ƙarƙashin burinsu na yaɗa dimokraɗiyya da yancin walwaha ciki har da addini, suna zargin wasu ƙasashen da rashin barin wannan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''To a ƙarƙashin wannan ne suke fitar da rahoto, lokaci zuwa lokaci, inda a ciki suke zargin cewa a Najeriya ba a barin walwalar addini, ma'ana ƴancin addaini yana da rauni'', in shi.

Ya ƙara da cewa sukan bayar da rahoton cewa ana kai wa mabiya wani addini ɗaya hare-hare.

''Sukan bayar da hujja daga bayanan da wasu limamai da jagororin addinan ke bayarwa, cewa lallai ana kai wa wani ɓangaren addini hare-hare a ƙasar'', in ji shi.

Dakta Kabiru Adamu ya bayar da misali da cibiyar USCRIS a Amurka da ke ƙoƙarin haɓɓaka addini tsakanin ƙasashe, wadda a wasu lokutan ya ce takan bai wa gwamnatin Amurka shawarar saka wa Najeriya takunkumi, saboda rashin walwalar addini.

Sai dai masanin tsaron ya ce bayan binciken kamfaninsa na Beacon Security ya gano cewa akwai rauni sosai a cikin shaidun da cibiyar ta Amurka ke bayarwa.

''Kusan ɓangaranci kawai ake nunawa a cikin bayanan shaidun da take samu, saboda suna ƙarfafa cewa kamar addini guda ne kawai ake kai wa hare-hare a ƙasar, wanda kuma ba haka batun yake ba'', in ji shi.

Shin ana yin kisan ƙare-dangi a Najeriya?

Kabiru Adamu ya ce daga bayanan da suke da shi ba addini guda kawai ake kai wa hare-hare ba a Najeriya.

'"Amma saboda wasu manufofi na siyasa ko na cimma wani buri daban, sai ka ga ana yayata cewa addini guda ake kai wa hare-hare'', in ji shi.

'Bayanan gwamnati ne ke ruruta batun'

Inuwar ƴanbindiga suk ɗaga bindigogi sama

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Dakta Kabiru Adamu ya ce gwamnatin Najeriya ce ke fitar da bayanai waɗanda za a iya fassara su a matsayin "ana yin kisan ƙare-dangi a ƙasar."

Ya ce hukumar kula da ƴancin ɗan'adam ta ƙasar, wato Human Right Commission, wanda ɓangare ce ta gwamnati, ta fitar da irin wannan bayani.

''Rahoton da Human Right Commission ta fitar a baya-bayan nan ya ƙarfafa irin wancan rahoto da Amurka ke fitarwa, kuma wannan kuskure ne'', a cewar Dakta Kabiru Adamu.

Masanin tsaron ya ce duk wanda ke bibiyar abin da ke faruwa a Najeriya, yana sane da cewa ba mabiya addini guda ake kai wa hare-hare ba.

''A baya-bayan nan an samu hare-hare kan masu ibada a masallatai a Katsina da Zamfara, inda aka kakkashe su suka kuma aka sace wasu, amma hukumar Human Right Commission ba ta bayar da irin waɗannan misalai a cikin bayananta ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa a maimakon haka hukumar ta riƙa wallafa bayanan wasu hare-hare da aka kai wa mabiya addinin kirista a jihohin Benue da filato.

Don haka ne masanin tsaron ya ce gwamnatin Najeriyar ta makara sanadiyyar bayanan da ta riga ta fitar.

Me ya janyo zargin?

Dakta Kabiru ya Adamu ya ce abin da ke janyo zargin shi ne muradin gwamnatin Amurka.

''Ai ƙasar Amurka ita ce kan gaba a yaɗa waɗannan rahotonni, kuma muradin gwamnatin ƙasar ne, idan ka kula wannan gwamnati ta yanzu (ta Tump) waɗanda suka zaɓe ta, masu alaƙa da addini ne kuma addinin ma na ɓangare guda, kuma shi shugaban gwamnatin na ƙoƙarin biya musu buƙatunsu, don cimma burinsa na siyasa'', in ji shi.

Ya ce cibiyar USCRIS burinta shi ne tabbatar da walwalar addini a duniya baki ɗaya, kuma ... shi ne yaɗa addinin Kirista, saboda mafiya yawan magoya bayan Trump mabiya addinin Kirista ne.

Wane kallo ƙasashen ke yi wa Najeriya?

Dakta Kabiru Adamu ya ce irin waɗannan ƙasashe na yi wa Najeriya kallon ƙasar da babu ƴanci da walwalar addini.

''Haka kuma suna kallon Najeriya a matsayin ƙasar da ke yin danniya da muzguna wa wasu, don haka ne ma suke kiran saka wa ƙasar takunkumi'', in ji shi.

Wace illa hakan ke yi wa gwamnatin Najeriya?

Masanin tsaron ya ce ko shakka babu wannan zai iya yi wa Najeriya illa idan gwamnati ba ta ɗauki matakin dakatar da irin wannan ba.

''Idan hakan ya ci gaba , to wata rana gwamnatin Amurka za ta iya saka wa Najeriya takunmumi, saboda a fahimtarta ana hana walwalar addini a kasar'', in ji shi.

Sannan kuma za a iya dakatar da ba ta irin taimako da agaji da ƙasashen duniya ke ba ta, saboda takunkuman da aka sanya mata, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Masanin taron ya kuma ce matakin zai iya shafar zuba jari a ƙasar.

Haka ma Dakta Kabiru Adamu ya ce matakin zai iya shafar haɗin kan Najeriya, da yaƙi da ƴanbindiga da ake yi a ƙasar.

''Haɗin kai kan Najeriya na zaune a kan abubuwa guda biyu, wato addini da ƙabilanci, kuma duk abin da ya taɓa waɗannan abubuwa zai iya shafar zaman lafiyar ƙasar, har yaƙin basasa wannan zai iya janyowa'', in ji.

Ya ce yana da kyau gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan batu da matuƙar muhimmanci, ta yi wani shiri na musamman na yi wa tufta hanci game da matsalar.

'Ƙoƙarin da gwamnati na magance matsalar'

Ministan yaɗa labaran Najeriya, zaune cikin ofishinsa

Asalin hoton, Mohammed Idris

Gwamnatin Najeriya ta ce tana ƙoƙari wajen ƙoƙarin fattakar ƙungiyoyin ƴanta'adda a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyin ƴanƙasar, kuma ana ganin sakamakon hakan.

''Tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Fabrairun 2025 kadai, fiye da ƴanbindiga 13,543 ne sojojinmu suka kashe tare da kuɓutar da kusan 10,000 da ake garkuwa da su a faɗin ƙasar'', a cewar gwamnatin ƙasar.

Gwamnatin ta yi kira ga kafofin yaɗa labarai na duniya da saran masu sharhi su riƙa aiki bisa doka, tare da mutunta gaskiya a aikinsu.

''Muna kira ga masu ruwa da tsaki su riƙa aiki da ilimi wajen gudanar da ayyukansu , sannan su guji yaɗa labaran ƙarya da za iya kawo rarrabuwar kai a ƙasarmu, a maimakon haka su ƙarfafa wa gwamnati gwiwa a ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da laifuka a ƙasar''.