Me ya sa aka gaza warware rikice-rikicen jihar Filato?

Asalin hoton, Getty Images
Mahara sun kashe mutum 52 da tarwatsa wasu 2,000 a hare-haren da suka kai kan wasu al'ummu a jihar Filato ta arewacin Najeriya, kamar yadda hukumar kai agajin gaggawa ta Najeriya ta tabbatar.
Babu masaniya game da dalilan kai hare-haren a kauyuka shida na karamar hukumar Bokkos, wadanda su ne mafi muni tun bayan rikicin da ya barke a yankin a watan Disamban 2023, lokacin da aka kashe sama da mutum 100.
Harin na baya-bayan nan ya fito fili ne a cikin ƙarshen mako, lokacin da aka kai mutanen da suka jikkata asibiti, kuma tuni shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin zakulowa da kuma hukunta wadanda suka kai harin.
Filato ɗaya ce daga cikin jihohin Najeriya masu cakuɗuwar mutane daga ƙabilu da addinai daban-daban a arewa ta tsakiyar Najeriya, yankin da ya yi ƙaurin suna a rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya.
Ko me ya sa rikicin jihar ya ƙi ci ya ƙi cinyewa? BBC ta tattauna da Kabiru Adamu, masani kan tsaro a Najeriya da yankin Sahel, wanda ya lissafa dalilan da suka sanya rikicin ke tashi a kai a kai...
Rashin ɗaukar ƙwararan matakai

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa gwamnatin jihar Filato ta sha ayyana kafa kwamitoci da kuma gudanar da bincike kan rikice-rikicen da aka fama da su a jihar, har yanzu hakan bai kawo ƙarshen matsalar ba.
Kabiru Adamu ya ce hakan bai rasa nasaba da gazawar hukumomi wajen magance abubuwan da ke haddasa rikicin.
"A baya, abin da muka gani shi ne ana ɗaukar matakai ne sanadiyyar siyasa amma ba a ɗaukar matakan dindindin wajen magance matsalar," in ji Kabiru Adamu.
Ya ƙara da cewa "ba a bin matakan maganace matsalar na dindindin, kamar matsalar tattalin arziƙi da ƴan ƙasa ke ciki, da lalacewar muhalli duk suna nan ba a magance su ba."
Rashin dokar mallakar ƙasa
Kabiru Adamu ya bayyana matsalar rashin tsarin mallakar fili a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka sanya aka gaza magance matsalar rikicin na jihar Filato.
Ya ce: "Har yanzu gwamnatin jiha da na tarayya ba su fitar da ingantaccen tsarin da ɗan ƙasa zai mallaki filin da yake da iko da shi ba."
Wannan matsalar ta fito fili ne idan aka lura da yadda wasu a jihar ta Filato ke kallon kansu a matsayin ƴan ƙasa, waɗanda ke da ƴancin mallakar filaye, yayin da ake wa wasu kuma kallon baƙi waɗanda ba su da ƴancin mallakar fili.
Wannan ya haifar da ruɗani da rikice-rikice a lokuta daban-daban a jihar.
Kabiru Adamu ya ce ya kamata a samar da tsarin da za a bai wa wanda ya mallaki fili duk takardun da suka kamata na shaidar cewa ya mallakin filin bisa doka.
Ƙabilanci da addini

Asalin hoton, Getty Images
Ana kallon ƙabilanci da addini a matsayin ƙiraren da ke rura tashin hankalin na jihar Filato, inda a mafi akasarin lokuta duk wani rikici da kan tashi a yankin kan samo asali ko kuma ya rikiɗe zuwa na ƙabilanci ko na bambancin addini.
Masanin kan tsaro ya ce duk da akwai wasu jihohin da suka yi fama da rikice-rikicen ƙabilanci da addini, amma gazawar gwamnatin jihar na samar da matakan da suka dace ta sanya lamarin ya ci tura a Filato.
Ya ce "gwamnatin jihar ta gaza wajen samar da yanayin da zai ɗunke rashin haɗin kai ko bambance-bambance na addini da ƙabilanci da ke addabar jihar."
Ya ƙara da cewa "duk da cewa ta (gwamnati) ƙirƙiro misali, hukumar tabbatar da zaman lafiya, wato 'Peace Commission' da kuma Early warning system mai ankararswa idan matsalar tsaro za ta taso, to amma bisa ga fahimtarmu ba a ba su kuɗaɗe da damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba," in ji Adamu.
Siyasa
Wani abin da Kabiru Adamu ya bayyana a matsayin lamarin da ke kawo cikas ga zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Filato shi ne siyasa.
Ya ce inda siyasa ta shigo cikin lamarin shi ne ƴan siyasa ba su fahimci muhimmanciu ɗaukan matakan da suka dace domin kawar da matsalar baki ɗaya ba.
"Misali, za ka ga idan wanda ke riƙe da madafun iko na son ya ɗauki mataki, amma idan ya yi la'akari da yadda magoya bayansa za su fahimci matakin, to saboda siyasa sai ka ga ko ya ƙi ɗaukan matakin ko kuma ya yi wani abin na daban da zai faranta wa magoya bayansa rai, ba tare da ya ɗauki ainahin matakin da zai magance matsalar ba," in ji Kabiru Adamu.
Ya ƙara da cewa ko a game da batun dokar mallakar filaye, "abu ne wanda gwamnati za ta iya yi idan tana so, amma saboda dalilai na siyasa har yau ba a samu gwamnatin ta da iya ɗaukan matakin ba."
ce ta sanya gwamnati ta gaza samar da dokar da za ta tantance
Matsalar tsaro a jihohi masu maƙwaftaka
Baya ga Filato, kusan dukkanin jihohin da ke kewaye da Filato na fama da wasu mataloli na tsaro, ko dai wasu matsalolin daban, ko kuma masu kamanceceniya da na Filato.
Taraba na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsananciyar matsalar rikicin manoma da makiyaya, hakan nan ma jihar Nasarawa da kuma Bauchi.
Kabiru Adamu ya ce irin waɗannan matsalolin tsaro da ke faruwa a jihohin da ke maƙwaftaka da Filato "kan taso su shiga jihar."
Sauran matalolin da masanin tsaron ya ambato sun kuma haɗa da:
- Taɓarɓarewar harkar shari'a
- Rashin ƙarfin hukumomin gwamnati
Masana dai na ganin duk da cewa a koda yaushe aka samu ɓarkewar rikici a jihar Filato ana alaƙanta ta da bambancin addini tsakanin Musulmai da Kirista ko kuma ƙabilanci - tsakanin ƙabilun jihar Filato da kuma a ɓangare ɗaya Fulani makiyaya da Hausawa, amma sauyin yanayi da kuma tsukewar dazukan kiwo na daga cikin manyan dalilan da ke iza wutar rikicin.
Mece ce mafita
Kabiru Adamu ya ce mafitar ita ce a magance matsalolin da aka bayyana a sama.
- Ƙarfafa tsarin hukunta masu laifi
- Samar da kuɗaɗe ga hukumomin daidaita zamantakewar al'umma
- ƙarfafa tsare-tsare na tsaro, kamar shirin 'Safe Heaven' - tare da fitar da lokaci da abubuwan da shirye-shiryen ke son cimmawa
- Samar da tsarin mallakar filaye ba tare da la'akari da addini ko ƙabilanci ba
- Haɗa hannu wurin musayawar bayanan tsaro tsakanin Filato da jihohin da ke maƙwaftaka da ita masu fama da rashin tsaro
- Hukuma ta janyo fararen hula a jiki ta yadda za su iya ba ta bayanai kan masu son tayar da hargitsi











