Joshua Dariye na shan suka kan yunƙurin tsayawa takara

Asalin hoton, EFCC
Masu yaki da rashawa a Najeriya na sukar wani yunkuri da aka ce tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye ke yi na sauya-sheka zuwa Jam`iyyar Labour da nufin neman takarar kujerar sanata ta mazabar Filato ta tsakiya.
Wasu dai na ganin cewa bai kamata mutumin da kotu ta kama da laifin badakala na makudan kudade ya sake neman shugabancin al`umma ba.
A ranar Litinin ne aka saki tsohon gwamnan da wasu daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekara hudu a daure, sakamakon kama shi da laifin wawure kudin gwamnatin jihar fiye da naira miliyan dubu daya.
Kasa da mako guda da sakin tsohon gwamnan, maganar sake tsayawa takararsa domin neman kujerar Sanata a mazabar Filato ta tsakiya ta fara fitowa kuma a hankali maganar sai kara karfi take yi.
Har a rahotanni ana cewa an kammala shirin karbar sa a jam`iyyar Labour tare da share masa hanyar shiga takara.
Sai dai masu yaki da rashawa a Najeriyar na cewa bai kamata a ba shi wannan damar ba, ganin cewa dawowarsa ke nan daga gidan yari, sakamakon daurin da aka yi masa, bayan kotu ta kama shi da laifin cinye kudin jihar ta Filato a zamanin da yake gwamna.
Auwal Musa Rafsanjani shi ne wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya kuma ya bayyana cewa wannan ya nuna cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da ake yi a Najeriya ya zama wasan yara.
"Idan Buhari ya ce ya yafe, ai jama'ar da aka sace kuɗinsu waɗanda suna nan suna fama cikin wahala da yunwa da talauci ai su ba su yafe ba," in ji Rafsanjani.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya bayyana cewa idan akwai gaskiya da adalci bai kamata a ce Dariye ya sake fitowa da batun yin takara ba, bayan laifukan da aka same shi da su a baya.
Gwamnatin Najeriyar dai ta yi la`akari da larurar rashin lafiya da Mista Dariye yake fama da ita ne ta sake shi. Wannan ne ma ya sa Auwal Rafsanjani ke zargin cewa akwai rashin gaskiya a cikin lamarin, ganin cewa ba a je ko ina ba har ya fara maganar takara.
"Mutumin da ba shi da cikakkiyar lafiya ya za a yi kuma ya dawo ya fara tsayawa takarar siyasa, ke nan dalilin nan da aka ce an bayar domin a sako su karya ce da yaudarar jama'a," in ji Rafsanjani.
Tun a ranar Larabar da ta wuce aka fara jin maganar shigar tsohon gwamnan Jam`iyyar Labour, kuma BBC ta yi kokarin tuntubar shugabar jam`iyyar a Jihar Filato, Madam Grace Zamfara ta waya game da wannan batu, amma ba a same ta ba.
Sai dai babbar sakatariyar jam`iyyar ta bayyana cewa tana sane da wannan batu kamar yadda Dakta Yunusa Tanko wanda shi ne kakakin jam`iyyar Labour na Najeriya ya shaida wa BBC.
Ya bayyana cewa daga jihar Filato an tuntuɓi jam'iyyar Labour kan batun takarar ta Dariye, sai dai a cewarsa, lokacin da mutum ya kamata ya tsaya zaɓe tuni aka rufe, amma duk da haka ya ce akwai yiwuwar a duba wannan lamari a ga yadda za a yi musamman idan doka ta bayar da damar yin hakan.
Sai dai duk da wannan ce-ce-ku-cen da ake yi, tsohon gwamnan na Filaton bai fito fili ya ce komai a kan wannan batu ba.










